Omar al-Bashir ya rusa gwamnatinsa

Asalin hoton, Reuters
Shugaba Albashir ya lashe takobin farfado da tattalin arzikin Sudan
Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya rusa gwamnatinsa, inda yake cewa kokari ne na shawo kan matsalar tattalin arzikin kasar.
Za kuma a rage adadin yawan ministocin daga 31 zuwa 21.
Shugaba al-Bashir ya ce daukan wannan mataki ya zama tilas domin magance radadi da wahalhalu da kasar ke fuskanta.
Wakilin BBC ya ce: 'Tattalin arzikin Sudan na cikin matsala, kuma kasar na fuskantar haka ne tun bayan balewar Sudan ta kudu daga kasar a 2011, wadda ta yi gaba da kaso mai yawa na albarkatun man kasar.'
Tun a watan Janairu Sudan ke fuskantar zanga-zanga, lokaci da farashin burodi ya rubanya, bayan gwamnatin Sudan ta soke tallafin da take bayarwa a kansa.
Darajar kudin kasar kuma ya karye, wanda hakan ya sa a ke wahala sosai wajen iya sayen kayayyakin amfani daga kasashen ketare.