Najeriya: Mutum 35 sun mutu a gobara

Daruruwan mutane sun jikkata a gobarar da iskar gas ta haddasa Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Daruruwan mutane suka jikkata a gobarar da iskar gas ta haddasa

Mutum 35 aka tabbatar da mutuwarsu a wata gobara da iskar gas ta haddasa a garin Lafiya na jihar Nassarawa, yayin da wasu daruruwa suka samu rauninka.

Rahotanni sun ce wata tankar dakon gas ce ta kama da wuta a wani gidan man Natson da ke kan babban titin da ya hada Abuja da Arewaci da kuma kudancin kasar.

Kuma wutar ba ta tsaya a anan kadai ba, domin ta kona motocin da ke ajiye a bakin hanya da kuma masu wucewa, da kuma kona shaguna da dama

Gobarar ta tayar da hankalin mazauna yankin da abin ya shafa.

Mutanen da gobarar ta rutsa dasu sun samu munanan kuna.

Labarai masu alaka