Guguwa ta yi ta'adi a Amurka da Asiya

Iyalai sun shiga tasku bayan zabtarewar kasar da guguwar ta haifar a Benguet Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Iyalai sun shiga tasku bayan zabtarewar kasar da guguwar ta haifar a Benguet

Gwamnan Jihar North Carolina a Amurka ya gargadi abinda ya kira karuwar barazanar da rai ke fuskanta, sakamakon ambaliyar da guguwar Florence ta haifar.

Tuni dai guguwar ta yi sanadin rayukan mutum 16.

Roy Cooper ya bukaci mutane su kauracewa tituna, tare da bayyana cewa ba a taba fuskantar irin wannan barazanar ta ambaliya ba.

''Ya ce wannan guguwa na sake zama barazana a North Karolayna, an fuskanci ambaliya har a yankunan da basu taba ambaliya ba, wannan yanayi na iya haifar da zabtarewar kasa.''

Guguwar da ke tafe da ruwa da iska mai karfin gaske ta shafi jihohin Carolina ta Arewa da Carolina ta kudu.

Daruruwan mutane aka ceto, yayin da dubbai suka fake a matsugunan gaggawa, yawancin yankunan kuma na fama da rashin wutan lantarki.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane na gudun neman tsiri dag guguwa mai karfi irinta da ake fuskanta a Asiya

A yankunan Asiya ma, mahaukaciyar guguwar da aka lakabawa suna Mangkhut ta ratsa yankunan kudancin China na Guangdong da Hainan tafe da karfin iska mai gudun kilomita 160 a sa'a 1, da ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Mahukuntan China sun kwashe mutane kusan miliyan biyu da rabi a yankin da ke makare da mutane da dawo da dubun-dubatan jiragen kamun kifi tashoshi kafin isowar guguwar a yammacin Lahadi.

An kuma rufe akasarin shagunan da ma'aikatun gwamnati.

Kafafen yada labaran kasar sun ce mutum biyu sun mutu.

Hakazalika guguwar ta ratsa Hong Kong, inda ta girgiza dogayen benaye da tarwatsa tagogi.

A arewacin Philippines ma gomman mutane suka rasa rayukansu, ciki har da masu hakar ma'adinai 30.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yadda guguwar ta tarwatsa tagogi a Hong Kong