Jirgin Rasha ya yi batan dabo a teku

Jirgin ya bata ne a hanyarsa ta komawa sasanin Rasha da ke arewa maso yammacin Syria. Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Jirgin ya bata ne a hanyarsa ta komawa sasanin Rasha da ke arewa maso yammacin Syria.

Wani Jirgin binciken dakarun Rasha ya yi batan dabo a tekun Mediterranean dauke da sojojin ta 14.

Kafar yada labaran Rashar ta ce kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar a Moscow ta shaida, jirgin ya bata ne a hare-hare da Isra'ila ta kai ta sama akan Syria.

Kuma jirgin Rashar ya gano wata roka da aka harba daga jirgin ruwan yakin Faransa.

Wani jami'in Amurka da ba a bayyana sunansa ba, ya shaidawa kamfanin dilancin labaran Reuters cewa Washington na ganin cewa gwamnatin Syria ce ta kakkabo jirgin da makamin artilary amma a bisa kuskure, a kokarinta na harba makami mai linzami a kan Isra'ila.

Wannan al'amari na zuwa ne adaidai lokacin da Rasha da Turkiya suka amince su kafa yankin tudun mun tsira tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a lardin Idlib na Syria.

Moscow ta ce yarjejeniyar na nufin gwamnatin Syria a yanzu za ta dakatar da kaddamar da hari a yanki na karshe da 'yan tawaye ke da karfi wanda kuma ke dauke da mutum miliyan 3.

Rasha ta ce za a bukaci kungiyoyin da ta kira masu tsautsauran ra'ayi irinsu Al-qaeda janyewa daga yankin.

Labarai masu alaka