Shugaba Edgar Lungu ya kori wani minista a kan rashawa

Shugaba Lungu ya nuna rashin jindadinsa da rahotan da ke cewa an karkatar da kudaden gwamnati Hakkin mallakar hoto others
Image caption Shugaba Lungu ya nuna rashin jindadinsa da rahotan da ke cewa an karkatar da kudaden gwamnati

Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu, ya kori ministan jin dadin jama'ar kasarsa.

Mai magana da yawun gwamnati ta ce an samu zarge-zarge a kan kashe kudadde ta hanyar da ba ta dace ba a ma'aikatar da Emerine Kabanshi ke shugabanta.

Da fari Burtaniya ce ta soma dakatar da duk wani tallafi da take bai wa kasar bayan Mujallar Africa Confidential, ta bayyana cewa kudadden tallafawa iyalai marasa galihu sun bata a asusun kasar da kuma kudaden da ake ware wa fanin kiwon lafiya da ilimi.

Mujallar ta ce an karkatar da kudedden ne wajen sayen motoci masu tsada, kuma an sace maguguna masu yawan gaske daga rumbun ajiyar kasar.

Shugaba Lungu dai ya umarci a gudanar da bincike akan al'amarin.

Labarai masu alaka