Red Cross ta nemi a saki ma'aikatanta

ICRC ta ce tana iyakar kokarinta domin ganin an sako su cikin koshin lafiya. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption ICRC ta ce tana iyakar kokarinta domin ganin an sako su cikin koshin lafiya.

Kungiyar bayar da agaji ya kasa-da-kasa, Red Cross ta bukaci mayakan Boko Haram su saki ma'aikatanta biyu da ke hannunsu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar a Najeriyar Aleksandra Matijevic Mosimann ta fitar ta ce babban daraktan gudanarwa na ICRC Dominik Stillhar ne ya yi kiran lokacin da ya kai ziyara arewa maso gabashin Najeriya ranar Laraba.

Ya kai ziyarar ne domin yin ta'aziyya ga iyalan Saifura Hussein Ahmad Khorsa, ungozomar da ke aiki da kungiyar, wacce 'yan Boko Haram suka kashe kwanakin baya.

An kama Saifura ce a garin Rann na jihar Borno a ranar daya ga watan Maris na 2018, tare da Hawwa Mohammed Liman da kuma Alice Loksha Ngaddah, wadanda har yanzu ba a sako su ba.

Stillhart ya kai ziyarar ne tare da rakiyar mataimakin daraktan ayyukan na Afrika na Red Cross.

Manyan jami'an kungiyar sun gana da iyalan Hawwa don karfafa musu gwiwa a madadin sauran ma'aikatan kungiyar. 

"Na zo Maiduguri ne daga shalkwatarmu da ke Geneva domin na jiyarci iyalan Saifura in kuma jajanta masu," in ji Stillhart.

"Ina kuma jaddada wa danginta da kuma dangin Hawwa cewa za mu ci gaba da bayar da gudunmawarmu a wannan yanayi mai matukar wuya. Dangin Hawwa har yanzu suna cikin jimamin rabuwa da ita, abin ya sosa mani rai ainun ganin halin da iyalanta suke ciki. Babu iyayen da ya dace a sanya su cikin wannan hali."

  A cewar sa, ICRC tana iyakar kokarinta domin ganin an sako su cikin koshin lafiya.

Stillhar ya ce "Muna kira ga wadanda ke rike da Hawwa da kuma Alice da su sako su ba tare da bata lokaci ba. Ma'aikatan kiwon lafiya ne su, kuma wajibi ne a kare su!" 

Labarai masu alaka