Me kuka sani game da salon kidan jazz?

Olakunle Tejuoso a Jazzhole da ke Legas Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Olakunle Tejuoso a shagonsa na sayar da fayafayai da litattafai a Legas

Olakunle Tejuoso na tsaye a tsakiyar shagonsa na sayar da fayafayen kida mai suna The Jazzhole, sanye da rigar buba da wando, inda yake magana da ma'aikata masu jera litattafai a kan kanta.

Tejuoso ya tuna wasu abubuwan da ya yi sha'awa a lokacin yarintarsa.

"Gaskiya da farko na yi fatan mallakar shagon sayar da fayafayai... Tun ina dan yaro na fara tattara wakoki.

Tejuoso ya ce "A gareni tamkar abun dabi'a ne in koma yin abin da na yi sha'awa a yarintata bayan kammala karatu."

Hakkin mallakar hoto Princess I. Abumere/BBC
Image caption The Jazzhole

An fara The Jazzhole wanda ke titin Awolowo Road a Legas babban binrin kasuwancin Najeriya ne tun a 1991 a wani karamin wuri a birnin.

Yanzu da kada-kaden Afrobeat ke tashe a gidajen radiyo a gidajen rawa, Jazzhole ta koma tamkar ma'adanar wasu nau'uka na kade-kade da raye-raye.

Yanzu Jazzhole da ke sayar da faya-fayen sauti da litattafai na daga cikin muhimman wuraren da mutane kan je domin kebewa a Legas domin shakatawa da dadadan tsoffin kade-kade a wannan zamani.

Hakkin mallakar hoto Princess I. Abumere/BBC
Image caption The Jazzhole na da fayafayen jazz music na zamani daban-daban

"Mun bude ne musamman domin sayar da kade-kaden jazz da na 'yan Afirka. Mun fi karkata ne a kan kade-kaden bakar fata."

Kidan Jazz ya yi tashe a 1990s, amma yanzu hakan ya kau, wasu nau'uka ne ke tashe.

"A wancan lokaci ne faifen CD ya fara fitowa, kuma mawadata ne abokan cinikinmu. Masu sayen fayafayen sun fahimci kidan saboda yawancinsu sun sha ganin wasan mawakan a dandali.

"Yawacinsu sun taba zuwa kasashen waje kuma suna da kudin halartar bukukuwa."

Hakkin mallakar hoto Princess I. Abumere

Tejuoso ya ce yanzu mutane sun fi sha'awar samfurin jazz na "funk'' da "smooth jazz."

"Matasan yanzu sun dan bambanta da zamanin da muke tasowa."

Hakkin mallakar hoto Princess I. Abumere/BBC
Image caption Duk da cewa ana cikin zamanin sauraron kade-kade ta intanet, har yanzu The Jazzhole na sayar da fayafayen garmaho da na CD

Bukukuwa na kai tsaye

Kazalika ana shirya wasanni na kai tsaye a Jazzhole. Tejuoso ya ce irin wadannan wasannin wata hanya ce ta tallata wakokin.

"Kar a manta a lokacin babu intanet. Hanyar da ake da ita ta tallatawa ko sayar da wakokin ita ce ta sanyawa a gidan radiyo domin ko kuma a kirkiro hanyar da mutane za su rika shigowa shagonka. Saboda haka sai ka yi amfani da abin da zai jawo mutane su zo ko su taru a shagonka. Kai kuma sai ka yi amfani da damar ka sayar musu da hajarka kuma ka tallata musu."

Hakkin mallakar hoto Princess I. Abumere/BBC
Image caption Rawar da mawakiya 'yar Najeriya Nneka ta yi a The Jazzhole a watan Agustan 2019

Mawaka da dama irinsu Asa da Brymo da kuma Nneka a baya-bayan nan, sun yi wasa a Jazzhole.

Yayin da Tejuoso ke tuna wasu abubuwan 1990s, ya kira matarsa wacce tare suka mallaki Jazzhole, ita ma ta fadi irin nata wakokin da take sha'awa.

"Har yanzu na fi son zamanin [Fatai Rolling] Dollar. Idan kuma mawaka ake magana, na fi son mawakan da," a cewarta.

Tejuoso ya tuna lokacin Fatai Rolling Dollar, daya daga manyan mawakan highlife suka yi wasa tare da mawakiya Keziah Jones.

"Mu'amala da tarayyar wasu daga zamanin [1950s] da irin mawaka 1990s.

Hakkin mallakar hoto Jon Lusk/Getty
Image caption Mawaki dan Najeriya Fatai Rolling Dollar yana waka a kan dandamali a Cargo ranar 14 ga watan Yuni 2009 a Landan.

"Mawakan da 'yan kallon na da ban sha'awa kasancewar muna yi ne da mawakan zamanin jiya da kuma yadda abin ke burge matasa."

"Wanda Asa ta yi abin tunawa ne. Mutane da yawa ne suka halarta. Shagonmu ya cika ya batse," inji matsarsa.

Kamfanin JazzholeRecords

Sakamakon karuwar bukatar wakokin 'yan Afirka, Tejuoso ya ga dacewar tashi daga matsayin mai sayar da faifen waka ya koma mai shiryawa. Hakan ce ta sa ya bude kamfaninsa a 1995.

"Yawancin wakonin da muke da su a 1990s muna samunsu su ne daga wasu kasashen Afirka ko Turai ko wasu sassan duniya.

"Wata rana sai na ce akalla ya kamata mu ma mu rika hada wakoki muna fitarwa zuwa wasu kasashe. Da haka aka fara kamfanin."

Hakkin mallakar hoto Princess I. Abumere/BBC
Image caption Daga cikin album din da kamfanin Jazzhole Records ta yi

Duk da cewa yanzu kidan jazz ya sauya ga kuma yadda suke tarayya da sauran nau'ukan kade-kade, Tejuoso na ganin cewa har yanzu Jazz na da damar sake yin tashe a kasuwanni.

"Idan har kana so jazz ya cigaba a nan gaba, to sai ka mayar shi da yarenka. Za mu sake sauya tsarinsa ta yadda zai dace da mu ta wata fuska."

Mawaka da 'yan fim da manyan mutane irinsu Sarki Mohammed na shida na Morocco da mawakiya 'yar kasar Mali Salif Keita da jarumar fim din Black Panther Lupita Nyong'o da Danai Gurira duk sun ziyarci Jazzhole.

Jazzhole mai cike da fayafayen CD da na garmaho da tarin littafai, ga kuma kidan jazz na tashi, yanzu ya zama wurin shakatawa ga masoya kidan jazz.

"A ganina an fi daukar kidan jazz da muhimmanci a wuraren da mutane ke zuwa su saurara cikin nutsuwa, ba a inda mutane ke shan taba ko shaye-shaye ba. Wata hanya ce ta musamman na jin dadin kida."

Labarai masu alaka