Neman sanin abubuwa ya kan sanya mutum guje wa son rai

Tarin ilimi da yawan fasaha ba sa hana mu rike ra'ayoyi na son rai - amma budaddiyar zuciya mai neman sanin gaskiya na iya yi mana garkuwa daga bin yarima a sha kida.

Idan ka tambayi duk wani mai ra'ayin kawo sauyi a Burtaniya dangane da ra'ayinsa game da makamashin nukiliya, kafin ya furta jawabi ka san mai zai ce.

Idan kuma ka tambayi dan ra'ayin rikau na kasar Amurka ra'ayinsa game da barazanar sauyin yanayi, shi ma ka san jawabin da zai bayar tun kafin ya budi bakinsa.

Kamata ya yi a ce ilimin kimiyya shi ke sarrafa ra'ayoyinmu game da irin wadannan batutuwa ba akidarmu ta siyasa ba. Sai dai kuma ba haka lamarin ke kasancewa ba.

Tuni dai ilimin halayyar dan Adam ya nuna cewa iliminmu da fasaharmu ba sa hana akidar siyasa ta yi tasiri kan ra'ayinmu, ko da kuwa bamu da wata gamsasshiyar hujja ta kankame wannan akida.

Maimakon haka ikon iya kallon abubuwa daga bangarori da dama tare da tsayar da ra'ayi bisa hujja ya dogara ne kan wani dabi'a da muke raina wa wato son sanin kwakwaf.

Mahangar siyasa

Akwai tarihin hujjoji da ke nuna cewa tasirin akidar siyasa bai tsaya kan ra'ayoyinmu game da batutuwan da su ka danganci kimiyya ba, har ma da yadda mu ke fassara sababbin bayanai.

Don haka kuskure ne ka yi tsammanin za ka iya sauya ra'ayin mutane ta hanyar ba su sababbin hujjoji, kasancewar nazarurruka da dama sun nuna cewa mutane na dabi'ar watsi da duk wata sabuwar hujja da ba ta dace da ra'ayoyinsu ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rashin sani ba shi ke kawo son rai ba

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wannan ya sa mutanen da su ka fi kafewa wurin rike ra'ayin da ya sabawa ilimin kimiyya - misali wadanda ba su amince da barazanar sauyin yanayi ba - sun fi wadanda su ke da sassaukar adawa da lamarin tarin sanin ilimin kimiyya.

Amma ai son rai ba ya tasiri wurin saita ra'ayin masu kokari ko? Ba haka bane. Wani binciken ya nuna cewa mutanen da suka fi tarin ilimi, da kwarewa a fannin lissafi, da kuma yawan nazari mai zurfi game da akidunsu sun fi tsananin kin amincewa da sababbin bayanan da suka saba wa son ransu.

Wato mutanen da ke da zurfin tunani, su na da karfin kwakwalwar da za su kare ra'ayoyinsu tare da yin watsi da duk wani batu da ya saba wa ra'ayinsu komai ingancin hujjarsa.

Wannan dai labari ne mara dadi ga mutanen da su ka damu da ilimin kimiyya da kuma aiki da kwakwalwa. Sai dai kuma akwai dan

abin faranta rai daga wani sabon bincike da wasu masanan falsafa, da ilimin halayyar dan Adam da kuma masu shirya fim karkashin jagorancin Dan Kahan na jami'ar Yale.

Kahan da tawagarsa sun yi bincike ne kan yadda akidar siyasa ke tasiri game da yadda muke sarrafa sababbin bayanai, da kuma nazarin masu kallon finafinan kimiyya domin taimakawa masu shirya fim.

Sun samar da ma'aunai guda biyu. Na farko ya auna ilimin kimiyyar da mutane ke da shi ta hanyar yin tambayoyi game da sanin batutuwan kimiyya, hanyoyin binciken kimiyya, da kuma yadda ake tantance bayanai.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ra'ayoyi daban-daban na mutane kan sauyin yanayi

Ma'auni na biyu kuma ya auna yadda mutanen ke da sha'awar sanin batutuwan da suka danganci kimiyya.

Baya ga tambayoyin kai tsaye ma'aunin kuma kan bai wa mutane zabi game da irin labaran da ya kamata a sa a nazarin auna ra'ayin jama'a game da labarai.

Mutumin da ya zabi labaran da su ka danganci kimiyya maimakon siyasa ko wasanni, sai a kara masa maki a ma'aunin neman sanin ilimin kimiyya.

Bayan da su ka sami wadannan ma'aunan, masu binciken sun gwada ra'ayoyin al'umma game da batutuwan da suka shafi kimiyya. Da su ka yi amfani da ma'auni na farko, sakamakon da su ka samu ya nuna cewa ra'ayin siyasa ya na da matukar tasiri.

Amma a ma'auni na biyu, duk da akwai bambancin siyasa, amma wadanda su ka nuna sha'awar sanin ilimin kimiyya ra'ayinsu kan zo daya ko da kuwa akwai bambancin siyasa a tsakaninsu.

Don haka son sanin kwakwaf, na iya tsare mu daga amfani da ilimin kimiyya wurin tabbatar da ra'ayoyinmu na siyasa.

Haka kuma domin habaka fahimtar abubuwan da su ka shafi al'umma, ya na da matukar muhimmanci ga masu koyarwa su yi kokarin ganin sun sa wa dalibansu sha'awar sanin abubuwan da suka shafi kimiyya ba wai kawai su haddace sakamakon bincike ba. Idan kana son karanta na turanci sai ka latsa nan How curiosity can protect mind from bias