Ko kun san fa'idar sanƙo?

An sabunta labarin bayan da aka fara wallafa shi ranar 27 ga watan Satumbar 2016.

Wasu na kallon mutum mai sanƙo a matsayin mai basira kuma mutumin kirki
Bayanan hoto,

Wasu na kallon mutum mai sanƙo a matsayin mai basira kuma mutumin kirki

An dai san turawa Vikings a shekarun baya suna amfani da man shafawa da ake yi da kashin agwagwa.

Haka kuma shekaru aru-aru da suka gabata, 'yan kasar Girka sun yi amannar cewa abun da ya fi inganci wajen magance sanƙo shine kashin tattabaru da ake hada shi da wasu ganyayyaki .

Wani magani kuma da al'ummar ƙasar Masar ke amfani da shi fiye da shekaru dubu biyar shi ne suna niƙa ƙayar da ke jikin bushiya sai a kwaba da zuma a riƙa shafawa a wurin da sanƙo ya ke.

Matuƙar dai maza za su ci gaba da amfani da madubi, tabbas za su riƙa nuna damuwa akan yadda gashin kansu yake.

Wannan itace irin damuwar da Julius Caesar ya shiga ciki lokacin da ya yi ƙokarin ganin gashin kansa ya koma kamar yadda yake a baya.

Irin hular saƙar da ya riƙa sanyawa a kansa ba don al'adar mutanen Roma ba ne, illar domin ya rufe kansa ne wanda a lokacin ya ke ta ƙyalli.

Sai dai a yayin da ya hadu da Cleopatra, tuni kansa ya riga ya gama yin sanƙo.

Kuma a yunƙuri na ƙarshe da ta yi na maido da gashin kansa, ta bashi shawarar amfani da kashin bera da haƙoran doki da ake hadawa da man kade.

Sai dai kuma kash! Wannan magani bai yi aiki ba.

Daga ƙarshe dai ya rasa gashin kansa kamar sauran wasu fitattun mutane da suka gabata wadanda suka hada da Socrates da Napoleon da Aristotle.

Saura sun hada da Gandhi da Darwin da Churchill tare da Shakespeare sai kuma Hippocrates - wanda duk da amfani da kashin tattabaru, yana da sanƙo da har ake masa laƙabi da suna ta musamman.

Daga bisani dai gashi mai tsawo ya fara fitowa a bayan kan Caesar inda ya riƙa dabarar tace kansa daga baya zuwa gaba.

Bayanan hoto,

Charles Darwin misali ne na yadda ake kallon masu sanƙo a matsayin manyan mutane masu basira da kuma ƙima

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Daga bisani bayan wasu shekaru masu yawa, an daina amfani da magungunan gargajiya aka koma amfani da man shafawa na zamani tare da ƙwayoyi ko kuma tiyata domin dashen gashi.

A yanzu mutum zai iya zuwa asibitin da ake bada maganin kakkabewar gashi, har ma ba sabon abu bane yadda ake ganin tattalace-tallace wadanda ke kira ga masu sanƙo da su je su ga likitan su.

"Akwai wasu ƙasidu ma dake bayani akan sanƙo har ta kaiga yanzu akwai wasu kalmomi na kimiyya da ake amfani wajen bayyana matsalar sanƙo wato "androgenic alopecia".

A halin yanzu an ƙiyasta cewa ana kashe kimanin dala biliyan uku da miliyan dari biyar wajen neman maganin sanƙo a duk shekara.

Wannan adadi dai ya zarta yawan kasafin kudin da kasar Mecedonia na shekara guda, ko kuma kamar yadda Bill Gates ya nuna a bara cewa, ya zarta yawan kudaden da mu ke kashewa wajen yaƙi da zazzabin cizon saura wato dala miliyan dari biyu kacal a duk shekara.

Wani binciken jin ra'ayoyin jama'a da ƙungiyar likitoci masu yin tiyata don maido da gashin kai wato International Society of Hair Restoration Surgery ta gudanar a shekarar 2009, ya nuna cewa kusan kashi 60 na maza sun fi son gashi a kansu gaba daya maimakon kudi ku kuma abokai.

Ko mun yi kuskure ne?

Akwai wasu ƙwararan hujjoji da suka nuna cewa sanƙo ba ya faruwa haka kawai.

Ana kallon masu sanƙo a matsayin mutanen da suka fi basira, kuma manyan mutane da suke da ƙima, kuma irin yadda kan su ke ƙyalli zai iya taimakon wajen jan ra'ayin mata ko kuma su ceto rayuwa.

Kafin mu yi bayani akan ko me yasa sanƙo yake da tasiri, ya kamata mu fahimci wasu abubuwa tukuna.

Sabannin hasashen da aka saba yi da kuma kasancewar wasu shahararrun mutane masu sanƙo kamar su Bruce Willis - Irin yadda gashin kai yake ƙarewa akan mutum ba shine zai sa mutum ya zama cikakken mutum ba.

Bayanan hoto,

Sir Patrick Stewart ya samu sanƙo tun yana dan shekaru 19

Ta yaya hakan ya faru?

A shekarar 1897, an shiga cikin wani yanayi na fargaba bayan da wani likita dan kasar Faransa ya sanar da cewa ya gano abun dake janyo sanƙo.

Kuma idan aka duba batun sanƙo, hakika akwai dogon tarihi na kuskure wajen fahimta.

Aristotle na ganin yawan jima'i ne ke janyo sanƙo.

A zamanin Roman, an danganta annobar kakkabewar gashi akai a tsakanin jami'an soji akan hular kwano na ƙarfe da sojoji ke sanyawa.

Daga bisani kuma aka danganta matsalar ga bushewar ƙwaƙwalwa.

Bayanan hoto,

Sir Winston Churchill ya yi fice akan jaruntakarsa a lokacin yaƙin duniya na 2

Sakamakon wasu bincike da suka gabata sun nuna cewa mata ba sa ganin maza masu sanƙo a matsayin mutanen da ke basu sha'awa, mai yiwuwa kuma saboda galibin wasu masu sanƙo sun tsufa, kuma wani abun mamaki shi ne mata basu cika sha'awar tsofaffi ba.

"Mun san cewa mata sun fi sha'awar matsayin mutum, a don haka koda kuwa sha'awar ba ta siffar mutum ba ne, sha'awar tana iya zama ta wani bangare," in ji Muscarella.

Kafin ka tambayi Muscarella cewa ko ya nuna son zuciya game da wannan hasashe sai ya ce. "Sam sam ba ni da sanƙo ni ina da gashi mai yawa a kaina".

Bayanan hoto,

Salman Rushdie ya yi fice a litattafansa fiye da wadanda suka san shi, ya auri Padma Lakshmi a shekarar 2004

Akwai wasu hujoji da ake cece kuce akai wadanda ke nuni da cewa sanƙo na iya ceto rai.

A lokuta da dama lamarin ba haka ya kan kasance ba.

Bayanan hoto,

Bara mujallar Forbes ta sanya Lloyd Blankfein shugaban kamfanin Goldman Sachs a mataki na 26 cikin jerin manyan mutane a duniya

" Peter Kabai na jami'ar István da ke Hungary,ya lura cewa shekaru aru-aru da suka gabata a nahiyar turai, rashin samun wasu sinadirai nau'in UV, ya sa maza da ke samun raguwar gashi akan su da kuma alamun sanƙo kafin su cika shekaru 30 akwai yiwuwar za su iya kamuwa da cutar kansa na kusan kashi 45 nan gaba a rayuwar su.

Sai dai hujjar hakan tana ƙaruwa, domin maza da suka fi aiki a waje sun fi shiga hadarin kamuwa fiye da wadanda ke aiki a cikin gida.

Hakan kuma gaskiya ne musamman ga wadanda fatar jikin su ya dushe da ke zaune a yakunan da ake fama da tsananin zafin rana, ko kuma su kan yi mafi yawa na hutun su a ƙasashen waje.

Idan kana son karanta cikakken labarin a harshen Ingishi latsa nan: The benefits of going bald