Ka san illolin kaifin basira kuwa?

Wata mata cikin damuwa Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Damuwa na daga abubuwan da masu basira ke fama da su

Kana jin basira za ta iya kasancewa matsala mai ban takaici maimakon alheri mai tarin amfani? Watakila ka amince da haka ko kuma ka kekasa kasa ka ce ba ka yarda da wannan magana ba, ko?

Yi nazarin wannan binciken da David Robson ya yi wa BBC

Idan jahilci alheri ne, ko basira za ta iya zama masifa? Yawancin mutane za su ce haka abin yake.

Muna daukar mutanen da suke da baiwa a matsayin wadanda suke tattare da wata damuwa da kadaici.

Ka duba mutane irin su Virginia Woolf da Alan Turing ko Lisa Simpson dukkaninsu za ka ga sun yi fama da kadaici, ko da a lokacin da suke kan ganiyarsu.

Kamar yadda Ernest Hemingway ya rubuta: ''Farin ciki a wurin masu basira abu ne da ba kasafai ba wanda na sani.''

Za a iya ganin wannan magana kamar wani karamin abu ne da ya shafi wasu mutane 'yan kadan, amma hasken da take bayarwa abu ne da zai iya shafar mutane da yawa.

Yawancin manufofinmu na ilimi sun bayar da fifiko ne wajen bunkasa abin da ya shafi boko ko wanda ake koyarwa a makaranta.

Duk da cewa an san yana da iyaka amma har yanzu ana amfani da ma'aunin kaifin basira (IQ) a matsayin hanyar auna basirar mutum, kuma muna kashe makudan kudade wajen horad da kwakwalwa da bunkasa ta domin cimma wannan mataki na yawan maki na ma'aunin kaifin basira.

To amma kuma ina amfanin badi ba rai, idan duk bayan wannan dawainiya abin da za a samu (kaifin basira) ba shi da wani amfani?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arziki rigar kaya. Idan ka kasance mafi basira a cikin jama'a, to dawainiya ta same ka

Kimanin shekaru dari daya da suka gabata ne aka dauki matakin farko na amsa wannan tambaya, a lokacin ganiyar kidan Jazz na Amurka.

A wannan lokacin sabon tsarin jarraba kaifin basira na tashe, bayan da aka ga tasiri da muhimmancinsa a cibiyoyin daukar soji na yakin duniya na biyu, da kuma yadda Lewis Terman ya yi amfani da tsarin wajen ganowa da kuma nazari a kan wasu yara 'yan baiwa.

A lokacin ya bincike makarantun California na yaran da suka fi kokari, inda ya zabo 1,500 wadanda ma'aunin basirarsu ya kai lamba 140 ko sama da haka.

Haka kuma daga cikinsu akwai wadanda nasu ya wuce lamba 170.

Da aka hada gaba dayansu ne sai aka kira su da Ingilishi ''Termites'' (Gara), kuma har zuwa yau ana nazarin rayuwarsu.

Kamar yadda na san za ka yi tsammani, yawancin wadannan yara ko dalibai (Termites) sun samu dukiya da suna.

Fitacce a cikinsu shi ne Jess Oppenheimer, wanda ya rubuta wasan kwaikwayon nan na shekarun 1950 mai suna ''I Love Lucy''.

Lokacin da aka fara nuna wannan wasan kwaikwayo na shi a tashar talabijin ta CBS, albashin yawancin takwarorinsa (termites) ya linka na yawancin mai aikin ofis biyu.

To amma ba duka daga cikin wadannan dalibai 'yan baiwa ba ne suka cimma abin da Terman ya yi tsammani ba.

Akwai wasunsu da yawa da suka zabi wasu ayyukan na daban na rufin asiri kamar, aikin dan sanda da aikin jirgin ruwa da aikin akawu.

A bisa wannan dalilin ne Terman ya ayyana cewa ''basira da cimma nasara a rayuwa ba lalle ne a ce suna da dangantaka ba''.

Ma'ana ba dole ba ne a ce mutumin da yake da basira ya samu nasarar zama wani abu a rayuwa.

Kuma ba wajibi ba ne basirarsu ta jawo musu farin ciki.

A rayuwar wasunsu (Termites) sun yi fama da matsalar mutuwar aure da shan barasa da kashe kansu.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Wasu masu wayo da basira kan yi fama da takaici

A lokacin da suka kai shekarunsu na tsufa wadannan dalibai masu basira (Termites), an rika maimaita darasin da ke tattare da labari ko rayuwarsu.

Darasin kuwa shi ne, basira ba daya take da kyakkyawar rayuwa ba; ta iya ma kasancewa ba ka cimma burinka a rayuwa ba.

To amma ba wannan ba yana nufin a ce duk wanda yake da kaifin basira (IQ) ya gamu da matsala ko damuwa ba kamar yadda yawancin mutane za su dauka ba, abu ne dai da zai iya kasancewa mai rikitarwa.

Me ya sa ba za a ga amfanin kaifin basira ba a karshe?

Kaya mai nauyi

Wani abu da zai iya kasancewa shi ne ilimin basirarka zai zama kamar dabaibayi a wurinka.

A shekarun 1990, an bukaci wasu daga cikin wadannan dalibai masu kaifin basira (Termites) da su waiwayi rayuwarsu ta shekara 80 da suka yi.

Maimakon su ga irin nasarorin da suka cimma a rayuwa, da dama daga cikinsu sun nuna nadama da damuwa cewa ba su cimma abin da ya kamata su cimma ba, idan suka yi la'akari da baiwar da suke da ita a lokacin suna da kuruciya.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ba ko da yaushe wadanda suka samu cigaba tun suna matasa suke yin nasara a rayuwa ba

Tunanin irin nauyin da ke kan mutum musamman idan aka hada da irin abin da wasu ke sa rai a kanka, abu ne da ke addabar yara da yawa masu kaifin basira ko wata baiwa.

Babbar abar dubawa a irin wannan ita ce Sufiah Yusof wadda ke da baiwar lissafi, wadda aka dauke ta a Jami'ar Oxford tun tana da shekara 12, amma kuma ta yi watsi da karatun kafin ta yi jarrabawarta ta fita, kuma ta kama aiki a otal.

Daga karshe ta zama mai nishadantar da baki da baiwarta ta hanyar tilawar hanyoyin lissafi iri daban-daban yayin da take rawa ta batsa.

Wata matsala da ake yawan ji a wurin haduwar dalibai da tarukan intanet ita ce, mutane masu basira suna ganin irin matsaloli da gazawar duniya fiye da sauran jama'a.

Yayin da yawancinmu ba ma gani tare da damuwa da matsalolin gazawar duniya, masu kaifin basira kuwa suna cike ne da damuwa kan halin kuncin da wasu ke ciki ko kuma sakarci da wawancin da wasu mutanen ke yi.

Yawan damuwa zai iya kasancewa wata alama ta kaifin basira, amma ba kamar yadda masu falsafa ta cima-zaune suka dauka ba.

Da ya gudanar da bincike tare da tambayar dalibai a makaranta a kan abubuwa da dama na rayuwa, Alexander Penny na Jami'ar MacEwan da ke Canada ya gano cewa wadanda suke da kaifin basira suna cikin damuwa duk tsawon rana.

Kuma abin mamakin shi ne damuwar ta al'amrun duniya ne na yau da kullum.

Kuma wani abin shi ne daliban da suka fi kaifin basira sun fi nanata magana kan wani abu na damuwa da ya faru, maimakon tambaya.

'' Ba wai cewa damuwarsu ta fi ta kowa ba ne, a'a, abin shi ne sun fi damuwa ne sosai a kan karin wasu abubuwan,'' in ji Penney.

''Idan wani abu maras kyau ya faru sun fi tunani a kansa.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Masu basira sun fi tunani a kan wani abu da ya faru maras kyau

Penny ya gano cewa zurfafa bincike na da alaka da basirar magana, wato irin abin da ake jarrabawa a wasannin jarrabawa na sanin kaifin basira (IQ) idan aka kwatanta da wasan harhada kalmomi (puzzles) ( wanda ya kan rage damuwa).

Masanin yana ganin iya magana ka iya sanya ka ka rike furta damuwarka (zancen zuci) kana ta tunanin a kai.

Ba lalle a ce hakan wata matsala ba ce, in ji shi, ''watakila sun fi sauran mutane gano hanyar magance matsala ne kawai,'' wanda hakan zai taimaka musu koyon darasi daga kura-kuransu.

Abubuwan da hankali ba ya gani:

Gaskiyar lamari ita ce kaifin basira ba daya yake da yin hukunci ko yanke shawarar da ta fi dacewa ba, a wani lokaci ma shawararka sai ta iya kasancewa kamar ta sakarai.

Keith Stanovich na Jami'ar Toronto ya shafe shekaru goma da suka wuce yana tsara wata jarrabawa ta hankali, inda ta nan ya gano cewa hukuncin gaskiya wanda ba san kai a cikinsa ba danganci yawan kaifin basirar mutum ba.

Misali a nan shi ne abin nan da za ka ji mutum ya ce 'a ra'ayina', wanda hakan ke nuna cewa za mu yanke hukunci ne a bisa fahimta ko ra'ayinmu wanda hakan ke kara tabbatar da dabi'armu ko kuma ra'ayin namu a hukuncin da za mu yi.

Abin da ya fi dacewa a nan kawai shi ne, ka ajiye ra'ayinka gefe daya yayin da kake muhawara (wato idan ka ji wanda ya fi naka ka amince da shi ).

To amma matsalar ita ce kamar yadda Farfesa Stanovich ya gano, mutanen da suke da wayo ko kuma kaifin basira ba kasafai suke yadda su yi hakan ba idan aka kwatanta da wadanda basu da basira kamarsu ko kuma masu kaifin basira kamar na yawancin mutane gama-gari ne.

Wannan ba shikenan ba, domin mutanen da suka yi nasara a jarrabawar auna kaifin basira sun fi yin hukunci ko rike ra'ayi na son-kai.

Wato ba kasafai suke iya ganin gazawarsu ba duk kuwa da cewa sun isa sukan ra'ayin wasu ko kuma ganin kuskuren wasu.

Sannan kuma sun fi fadawa tarkon gurguwar fahimtar nan ta cewa idan abu ya cika faruwa fiye da yadda aka saba gani, a gaba ba zai faru ba sosai.

Ko kuma idan abu bai cika faruwa ba sosai akwai yuwuwar zai faru sosai a nan gaba.

Harwayau a bisa wannan fahimta, idan abu ya faru sau goma akwai yuwuwar ba zai faru ba a karo na 11.

Wannan mummunar fahimta ita kan sa masu hannun jari su sayar da hannun jarinsu kafin su kai kololuwar darajarsu, bisa fahimtar cewa nan da dan lokaci darajarsu za ta fadi tun da sun yi ta tashi.

To duk wannan dabi'a ce ta mutane masu kaifin basira, wadda kuma ba kasafai take kai su ga nasara ba.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Mutanen da suka fi basira ma a duniya sukan yarda da abin da kimiyya ba ta yarda da shi ba

Stanovich yana ganin akwai irin wannan matsala a tsakanin dukkanin rukunin al'umma.

''A yau akwai mutane da dama da suke yin abubuwa na rashin hankali duk da cewa suna da basira fiye da ta yawancin mutane,'' in ji masanin.

Ya kara da cewa, ''mutanen da suke yadawa iyaye ra'ayin watsi da allurar riga-kafi da wadanda suke yada karerayi a shafukan intanet yawanci suna da ilimi da basira sosai fiye da sauran mutane''

Wannan na nunawa karara cewa za a iya ruda da yaudarar mutanen da suke da wayo da basira, a kai su a baro.

To idan basira ba ta kai mutum ga yanke shawar ko yin hukuncin da ya dace ba, meye zai yi hakan?

Igor Grossmann na Jami'ar Waterloo da ke Canada na ganin ya kamata mu koma wa dabarar tun tale-tale wato ''hikima''

Da farko za a ga wannan dabara tasa ta fi kama da kimiyya.

To amma shi da kansa ya amince cewa, ''hikima ba abu ne da za a iya gani a zahiri ba.''

''Amma idan ka duba ma'anar kalmar hikima ta gama-gari, za ka ga cewa mutane da yawa za su yarda cewa magana ce ta mutumin da zai yi hukunci mai kyau da ba san-rai a cikinsa.''

A wani bincike ko gwaji Grossmann ya gabatar wa mutanen da ya yi binciken a kansu wasu matsaloli daban-daban na rayuwa kama daga abin da suke gani za su iya yi a kan yakin Crimea.

Yayin da mutanen suke bayani kan yadda za su bullo wa matsalolin, wasu masana tunanin dan-adam na auna dalilai ko hikimarsu da rauninta idan aka danganta ga san-rai;

Wato abubuwan dubawa a maganganun nasu, su ne, a ga ko za su iya yarda da iyakar iliminsu (rashin girman kai) da kuma ko suna kauce wa muhimman bayanai da ba su zo daidai da ra'ayinsu ba.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Mutanen da suke da kaifin basira sosai da ya zarta lamba 140 (a ma'auni) kusan sun fi cin bashi

Wadanda suka samu maki mai yawa suna da alama ta wadatar zuci a rayuwa da kyakkyawar mu'amulla da rashin damuwa kan wata matsala wanda dukkanin wadannan abubuwa ne da kusan a ce ba a ganinsu a wurin mutanen da suke da dabara ko wayo ko kuma basira sosai.

Haka kuma yanke shawarar da ta dace, ko yin abin da ya kamata na nuna alamun samun tsawon rayuwa, wato wadanda suka samu maki mai yawa za su iya samun tsawon rayuwa.

A takaice Grossmann ya gano cewa kaifin basira ba shi da alaka da dukkanin wadannan abubuwa da aka yi amfani da su a matsayin ma'auni.

''Mutanen da suke da kaifin basira za su iya saurin gabatar da ra'ayi ko matsayinsu kan abin da ya sa suke ganin ra'ayinsu shi ne na daidai, kuma za su yi hakan ne ta hanyar nuna fifiko ko san ransu.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Wadanda suka ci nasara sosai a rayuwa sukan yi nadamar wata dama da suka rasa a baya

Abin koyi:

Wannan zai sa nan gaba masu daukar ma'aikata su rika la'akari da wadannan abubuwa maimakon matsayin kaifin basirar mutum (IQ).

Tuni kamfanin Google ya ce zai rika tantance mutanen da zai dauka aiki ta binciken abubuwa kamar rashin girman kai maimakon tsabar basira

Ita dai hikima ba za a ce a binne take cikin dutse ba duk irin matakin basirarka, wato komai rashin basirarka, kamar yadda Grossmann ya bayyana yana ganin za a iya horar da kai yadda za ka zama mai hikima.

Ya nuna cewa muna samun saukin ajiye ra'ayinmu idan muka yi la'akari da halin da wasu suke ciki maimakon mu kanmu.

Ta wannan hanya ya gano cewa idan ka gabatar da matsalarka a matsayin ''wani'' ko ''wata'' maimakon ''ni'' wannan na taimakawa wajen nesanta kanka da ra'ayin wanda hakan zai sa ka rage son ranka abin da zai kai ka ga muhawara da ta fi dacewa.

Ana sa ran karin bincike a wannan fanni zai sa a gano wasu dabaru.

Kalubalen shi ne yadda za ka sa mutum ya yarda da rauninsa.

Idan ba ka iya kawar da ji da kai da basirarka ba wato a kullum kana tunkaho da basirarka kenan, to zai yi wuya ka yarda cewa basirar taka tana hana ka ganin gaskiya ko daukar matsayin da ya fi dacewa.

Kamar yadda Socrates ya ce, mutumin da ya fi kowa shi ne wanda ya yarda cewa bai san komai ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The surprising downsides of being clever