Kun san boyayyar tashar rediyon da ba a san mai ita ba?

Duk da cewa masoya sun aminta a kashin kansu, sai dai ba su san hakikanin manufar ma'anar abin da suke saurare ba. Hakkin mallakar hoto digi_guru
Image caption Duk da cewa masoya sun aminta a kashin kansu, sai dai ba su san hakikanin manufar ma'anar abin da suke saurare ba.

A tsakiyar cabalbalin dajin Rasha, wanda ba shi da nisa daga birnin St Petersburg, akwai katangar karfe mai turaku uku.

A bayanta akwai turakun karafa masu tsatsa na tashar rediyo, ginin da aka yi watsi da shi, inda aka killace wajen watsa shirye-shiryen da ginin bangon dutse.

Wannan munnunan wuri yana da matukar ban mamaki, inda ya kai makura tun zamanin yakin cacar baki.

Ana zaton nan ne hedikwatar tashar rediyon "MDZhB", wadda babu wanda ya taba ikirarin alhakin gudanar da ita.

Kimanin shekara 35 yana watsa shirye-shiryensa sa'a 24 ko wacce rana a mako; shiri ne mara dadin ji da ake ta maimaitawa.

Ko wacce dakika sai an bijiro da wani sautin ankarawar jirgin ruwa a cikin hazo. Haka karajin da ke sarrafa kansa ke ta ci gaba.

Sau dyua ko biyu a mako, wani mutum ko wata mace kan karanta wani abu cikin Rashanci, kamar "kaarar kai-kawon jirgin ruwa" ko "kwararre kan noma." Wannan shi ne kawai.

Kowa a ko'ina cikin duniya zai iya saurare, da zarar ya juya tasha kan saitin 4625 kHz.

Lamarin na da rudarwar ban mamaki, tamkar an kirkirata ne da wata manufar makirci don jirkita tunani.

A yau tashar har mabiya gareta a shafukan sadarwar intanet, wadanda suka kai dubbai, da ke yi mata lakabi da "karajin ankararwa- the Buzzer."

Wasu tashoshin boye tamkarta na biye mata, wadanda suka hada da "the Pip- cukurkudaddun sakonni" da "Squeaky Wheel- juyawar karaji." Duk da cewa masoya sun aminta a kashin kansu, sai dai ba su san hakikanin manufar ma'anar abin da suke saurare ba.

Hakkin mallakar hoto US defence department

Kowa zai iya sauraren karajin The Buzzer da zarar an juya saitin tashar 4625 KHz.

A gaskiya babu mai kwatawa. "Babu bayani da ke nuni da bazuwar sako," a cewar David Stupples, wani kwararre kan sakonnin sirri da ke Jami'ar City ta Landan.

Ko me ke faruwa?

Tashar rediyon ana kyautata zaton ta sojan Rasha ce, duk da cewa ba su taba yin ikrarin hakan ba.

Ta fara watsa shirye-shirye ne dab da karshen yakin cacar baki, sa'adda kwamunisanci ya yi kasa warwas.

A yau ana watsa shirye-shirye daga sassa biyu, wato St. Petersburg da wani wurin da ke kusa da birnin Moscow. Wani abin mamakin shi ne bayan rushewar Tarayyar Sobiyat, maimakon tashar ta daina gudanar da shirye-shiryenta sai ma kara kaimi da ta yi. Ko me ke faruwa?

Babu gazawa a mahangar fahimtar manufar shu'umar tashar, wato tun daga kan aikewa da sakonni ga sojoji zuwa kan mutanen boye.

Daya daga cikin irin wannan dabarar (da aka gano) ita ce "kunamar boye" mai ankararwa: ta yadda ko an kawo wa Rasha harin nukiliya, kawai sai Na'ura mai sarrafa kanta za ta daina aiki, sai a harba kunamar daukar fansa..

Babu tambaya kan wannan, domin manufa ce kawai ta kawar da makaman nukiliya. Akwai zargi game da wannan shirin ankararwar kanta.

Ta yiwu lamarin ba zai kasance da rudani ba kamar yadda yake nuni.

Asalin shirin dai an fara shi ne tun zamanin Tarayyar Soviet, inda aka rika amfani da dabarun sarrafa kwamfuta da ke bibiyar sakonnin sadarwar da ake watsawa don tantance tartsatsin sinadaran nukiliya masu aiki ko wadanda suka watsu.

Tashin hanakalin shi ne, kwararru da dama sun dauka cewa har yanzu ana amfani da shi. Tamkar dai yadda Shugaban Rasha Vladmir Putin ya yi nuni da kansa a farkon wannan shekarar, "babu wanda zai tsira" a yakin nukiliya tsakanin Rasha da Amurka. Ko wannan tashar kariyar farko ce?

Faruwar lamarin na nuni da wasu alamu a tsarin ankararwar kanta. Tamkar sauran tashoshin rediyo na duniya, wannan tashar na aiki ne bisa tsarin da ake yi wa lakabi da "gajeren zango."

Wannan na nufin cewa in an kwatantata da rediyon gida ko wayar tafi-da-gidanka da sakonnin talabijin, sakonni kadan ne ke ratsa kafa guda ko wacce dakika. Kuma lamarin na nufin za su iya kara kai wa gaba.

Duk da cewa sauraren tashoshin gida irin su BBC Landan ya zama dole a yankin makwafta, gajeren zango irin na tashar duniya ta BBC na watsa shirye-shiryenta tun daga Senegal zuwa Singapore. Sai dai daukacin tashoshin biyu ana watsa shirye-shiryensu daga gida guda.

Hakkin mallakar hoto (Hoto: Sashen tsaron Amurka)

Idan tsarin "kunamar boye" bai gano alamun da ke nuni da kimar matakin soja ba, sai kawai ya harba kunamar daukar fansa.

Daukacin jin dadin ya danganta ga "sakonnin da ake watsowa." Sakonnin rediyo da ake cilla wa sama sosai suna tafiya ne kai tsaye, inda daga bisani su bace da sun yi karo da shinge ko sun kai qololuwa.

Amma sakonnin matsakaicin zango suna da karin mafita - ta yadda za su yi tsalle su samu karsashin kara nausawa sama, inda za su samu damar yin tafiyar tsutsa sai su mike a tsakanin doron kasa da sama, inda za su share dubban mila-milai.

Wannan ne dalilin da ya sa za mu sake bin kadin mahangar kunamar boye.

Tamkar yadda kake sa raki, gajeren sakonnin zango su ne mafi shahara.

A yau jiragen ruwa da na sama da sojoji suna amfani da su wajen aikewa da sakonnin a daukacin nahiyoyi, har ma da yankuna masu tsaunuka. Sai dai akwai kugiyar kanainayewa.

Wannan babban falale ba falle ba ne mai haskawa, amma abu ne da ke watsuwa, wanda ke torokon tafiyar tsutsa tamkar a karkashin teku.

Da rana sai ya taso sama sosai, amma da dare ya yi sai ya kwanta a qasa. Idan har bukatarka samun tabbacin jin tashar rediyon a wani bangare na duniya - ko juya akalarta wajen yakin nukiliya, ta yiwu abin da kake yi ne - to yana da muhimmanci ka sauya watsa shirye-shiryen zuwa lokacin rana, ta yadda zai yi daidai.

Tuni shirye-shiryen duniya na BBC World ke bin wannan tsarin. Ita kuwa waccar shu'umar tasha ba haka take ba.

Wata fahimtar ita ce tashar rediyo na nuni da "karajin" nisan mabubbugar tartsatsin lantarki. "Don samun kyakkyawan sakamako na'urar hange da tattara bayanai da Rashawa ke amfani da su wajen gano makamai masu linzami, akwai bukatar ka fahimci hakan ," a cewar Stupples.

Tsawon tafiyar da sakonnin ke yi kafi kai wa sama da dawowa kasa, wato nisan da ya zama dole a kai gare shi.

Akwai tashar da ke da tsari irin wannan na kut-da-kut.

Takaicin shi ne lamarin na da kamar wuya. Bibibiyar nisan mabubbugar sako zai bukaci a samu wani sauti kamar karar ankararwar mota ta yadda mabambantan sakonni za su kai gare su daidai. "Karajinsu ba zai yi daidai da na shu'umar tashar ba," a cewar Strupples.

Abin da ke daukar hankali shi ne, akwai tashar da ke da tsari irin wannan na kut-da-kut. Tashar rediyo ta "Lincolnshire Poacher," wadda ta rika watsa shirye-shiryenta daga tsakiyar shekarun 1970 zuwa 2008.

Tamkar shu'umar tasha, an jiwota a sassan duniya. Kamar yadda shu'umar tasha take, shirye-shiryen na watsuwa ne daga boyayyen wuri, ko da yake an yi hasashen cewa daga Cyprus yake.

Kamar dai wannan hatsabibiyar tasha shirye-shiryenta wadansu cukurkudaddun al'amura ne.

A farkon ko wacce sa'a, tashar Lincolnshire Poacher kan fara shirinta na wake-wake ga rukunin masu jin Ingilishi:

Bayan an maimaita wannan sau 12, sai wata cukurkudaddiyar muryar mace ta koma karantun lambobi - "1-2-0-3-6" - a dunkule cikin Karin da mutanen Birtaniya ke furta kalaman Ingilishi.

Don gane hakikanin abin da ke faruwa, sai a koma nazarin abin da ya auku a shekarun 1920. Daukacin kungiyoyin hadingwiwar Rasha (arcos) su ne cibiyoyin kasuwanci masu muhimmanci da ke kula da hada-hada a tsakanin Birtaniya da Tarayyar Soviet. Ko kuma dai a ce shi ne abin da suka ce suna yi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Bayan da kungiyoyin suka kai farmaki Landan, sai Rashawa suka fahimci managarciyar hanyar isar da sako da 'yan leken asiri da suka fake a kasashen waje.

A Mayun 1927, shekaru da dama bayan an kama jami'in leken asirin Birtaniya, wani ma'aikaci da ya yi sakon kutsa kai cikin ofishin 'yan kwamunisanci da ke Landan, 'yan sanda sun kai samame ginin kungiyoyin arcos.

Ta yiwu a yi mamakin lamarin, amma Birtaniya ba ta gano wani abin da ba su sani tun a da ba.

Sabanin haka ma samamen da suka kai ya farkar da Tarayyar Soviet, inda suka gano cewa jami'an asiri na M15 na bin kadin ayyukansu tsawon shekaru 15.

Karshe Rasha ta karke da kirkiro dabarar cukurkuda sakonni. Kusan tashi guda suka koma amfani da tsarin "lalata shafin sakon."

A wannan tsarin, a kan canki mabudin (fashin baki) mutumin da ke aikewa da sako a tura wa mutumin da kawai aka yi nufin kai wa gare shi.

Matukar ma'anar an samar da ita ta 'yar canke, to da wuya a warware cukurkudaddun al'amuran. Don haka babu damuwa game wanda ya saurari sakon.

Yanzu Koriya ta Arewa ke kwata irin wannan salon.

Sabuwar kafar sadarwar na da matukar amfani, domin ba ta daukar lokaci kafin lambobin tashoshin su karade fadin duniya.

Akwai sunan tashoshi masu kayatarwa Nancy Adam Susan", "Russian Counting Man" da "Cherry Ripe" -tashar Lincolnshire Poacher da 'yar uwartawaxanda ke baza waqen

Za a yi mamakin jin cewa har yanzu ana amfani da lambobin tashoshi, sai dai suna da wani muhimmin amfani.

Ko da yake za a samu saukin gane wanda ke gabatar da shirye-shirye, kuma kowa na iya sauraren sakonni, amma dai ba za a iya sanin ko wane ne ake son isar wa sakon ba.

Wayar tafi-da-gidanka da intanet za su fi isar da sako cikin sauri, amma da zarar an bude saqon tes ko i-mail daga jami'in asirin da aka sani za ka iya rudewa.

Za ta iya zama lambobin tashar a lokacin rikici, wato idan aka kai wa Rasha mamaya.

Dabara ce ta dole: shu'umar tashar da ta buya, tana bayar da umarni ga haramtattun 'yan leken asirin Rasha a daukacin fadin duniya. Akwai dai matsala guda. Wannan shu'umar tasha ba ta gabatar da shirye-shirye a jerin sakonni.

Hakkin mallakar hoto Vlad Breazu / Alamy Stock Photo

A zamin yakin cacar baki, 'yan leken asirin Soviet na samun umarni ne bisa tsarin gajeren zango.

Wannan dai ba sakonnin ankararwa ba ne. Sabanin haka mutane da dama na ganin cewa tashar tana da manufa biyu.

Sakonnin da ke juya kansu a kai-akai suna cewa, "wannan tashar tawa ce, wannan tashar tawa ce…." Don haka mutane amfani da ita.

Ta yiwu an rigaya an warware rudanin da ke tattare da tashar rediyon Rasha. Amma idan masu sha'awar saurarenta sun tabbatar da gaskiyar lamarin, sai a yi fatan sakonnin da ke sarrafa kansu ka da su dakata.

Labarai masu alaka