Yadda ake yi wa yara auren wuri a Amurka

Angel na da shekara 13 lokacin da mahaifiyarta ta tilasta mata yin aure. 'Na rika ji na kamar baiwa', ta ce dangane da yarintarta.

Duk da wasu kasashen kamar su Zimbabwe da Malawi da El Salvador sun soke auren wuri a baya-bayan nan, har yanzu a kasar Amurka ba a soke auren wurin ba, inda jihohi 25 ba su da sharadin shekaru na auren wuri.