Wanne shiri muka yi wa illar yakin Nukiliya zai jawo mana?

Nukiliya

Asalin hoton, Getty Images

Daga Chris Baraniuk

22 ga Agustan 2017

A karni na 20 muna da labarin yadda aka rika fadakarwa kan samun mafaka daga burbushin sinadaran nukiliya da karajin jiniya da daukacin fadakarwa kan barazanar da ke tattare da nukiliya.

Shin muna bukatar farfado da "kariyar al'umma daga farmakin yaki" a yau?

Idan yakin makamai masu linzami ya barke, Gwamnatin Biratniya ta tanadi mafakar karkashin kasa a tsakiyar Landan. Ana yi mata lakabi da Pindar.

Wannan suna ya yi daidai da na mai wake a tsohuwar daular Girka, amma dangatakar na da tayar da hankali.

An ruwaito cewa shekara ta 335 kafin bayyanar Almasihu (BC) Sarki Iskandar ya rusa birnin Thebe, inda ya bar gidan Pindar kadai, don nuna godiyarsa kan wasu wakokinsa, wadanda suka yabi magajin Sarkin Girka.

Ba ma magana kan bam din da aka da aka jefo ko ko illar da za ta biyo bayan wadannan kwanakin, amma wannan lamari na bukatar a sauya (tunani kansa) - Alex Wellerstein

Illar da za ta haifar, tabbas ita ce ko za a baje birrnin Landan a musayar wutar makaman nukiliya, Pindar za ta tsira. Ko dai an tsara ginin ne saboda wannan manufa ba a sani ba.

Hotuna kadan ne na farfajiyar ginin da aka taba wallafawa, duk da cewa m'aikatar tsaro ta tabbatar da ginin Pindar bisa la'akari da bukatar neman bayanai karkashin dokar ''yancin fadin albarkacin baki.

Ita ma hedikwatar tsaron soja ta kai makura wajen "ci gaban gwamnati" na bayar da mafakar Pindar, al'amarin da ta cve shirin gwamnati ne don tazbbatar da cewa hukuma za ta iya bayar da kariya bayan aukuwa munanan hadurra.

Sai dai karfin shugabannin soja da manyan 'yan siyasa na da dabarun shawo kan musifu lamari ne na daban.

Asalin hoton, (Credit: AFP/Getty Images)

Bayanan hoto,

Mafakar burbushin sinadaran nukiliya a New york

Wannan dai ita ce tambayar da ke kai-kawo, a cewar AlexWellerstein na cibiyar fasahar kere-kere ta Stevenss da ke New Jersey.

Dangane da ci gaban gwamnati kuwa, cewa ya yi, "ba ni da ra'ayi kan wannan.. wannan matsalarsu ce."

Ba da dadewa ba Wellerstein ya sanar da cewa shi da abokan aikinsa kuna cikin wadanda ke aikin farfado da shirin matakan kariya ga fararen hula.

Wannan na nufin, shirin da bayanan fadakarwa an tsara su ne don taimaka wa al'umma su kare kansu da zarar an kawo farmakin yakin soja ko aukuwa musifu.

Shirin kare rayuwar fararen hula shi ne abin da aka fi tattaunawa lokacin yakin cacar baki lokacin da kugen farmakin yakin nukiliya ke kara kaina a tsakanin al'umma da harkokin siyasa.

Baya ga daukacin wannnan, ragowa kawunan makaman nukiliya 15,000 da ke fadin duniyar nan a yau, wadanda mafi yawansu mallakar Rasha da Amurka ne Shugabannnin kasashen duk biyun, ba da dadewa ba suka amince da cewa dangantakar kasashensu hadarin ya yi matukar yin kasa.

Ko da yake Wellerstein ya tabbbatar da cewa yakin nukiliya ko tayar da rugugin makamai masu linzami ga kasa mai mugun nufi ko 'yan ta'adda da wuya hakan ta kasance, sai dai yana da tabbaci kan bukatar da ake da ita ta yin shiri.

Asalin hoton, (Credit: Alex Wellerstein)

Bayanan hoto,

Nukemap sabuwar taswirar Google da aka inganta, wadda ke nusar da mai amfani da ita illar da ke tattare da fashewar makaman nukiliya

Daya daga ayyukan da Wellerstein ya gabatar shi ne taswirar Nukemap, wadda ita ce sabuwar taswirar Google da aka inganta, wadda ke nusar da mai amfani da ita illar da ke tattare da fashewar makamin nukiliya da suka harbor zuwa sashen da nike a duniya, wanda ya hada manyan birane.

Wannan manufa ce ta karfafa gwiwar mutane su saba da barazanar makaman nukiliya, ta yadda za su samu Karin tabbaci kan aukuwarta.

"Ka kaddara cewa ka dode kunnuwanka daga jin rugugin sauti (don hasashe/hangen nesa)," a cewarsa. "Kana kallon kololuwar saman Manhatttan, sai ka ga makaman nukiliya sun tashi sun tarwatse.

"Ka kaddara ka ga rumfar hadari ta yi sama a gabanka ake wasa da sako-sako wajen matakan kare fararen hula - "suna farin ciki da kyakkyata dariya," in ji shi.

Ko hakan na da matukar tasiri?"

Sabon aikin da ya fara zai yi la'akari da daukacin kayan da aka yi da manufa guda, a cewarsa.

Alal misali, ya yi nuni da cewa dabarar kawata littattafan labarai ita ce ilimantarwa kana bin da ya dace don kara samun damar tsira daga harin makamin nukiliya mai linzami.

Wannan shawara ce mai sauki da ke cewa a fake a cikin gida kada a fito a yi tuki a sassan da illar ta shafa.

Wannan kuwa sabo titunan a lokacin rikici sukan cunkushe da ababen hawa - kamar yadda ta faru sakamakon ambaliyar mahaukaciyar guguwar 'hurricane.'

Idan bam din nukiliya ya fashe zai tayar da dimbin kura da burbushin tartsatsin sinadarai (masu guba) kafin ya baibaye kasa.

"A tsakiyar ginin abubuwan kariya na nan harbutsai," kamar yadda Wellerstein ya bayya cewa, 'Ka fake a wurin na wasu sa'o'i, ta yadda illar da tartsatsin sinadarin zai yi maka ka iya raguwa matuka."

Asalin hoton, (Credit: Chung Sung-Jun/Getty Images)

Bayanan hoto,

Wata alamar 'mafaka' a kofar shiga tashar jirgin kasaa Seoul da ke birnin Koriya ta Kudu

Yadda Koriya ta Arewa ke kara kaimin karfinta wajen kaddamar da makaman nukiliya masu linzami da za su iya kai wa Amurka, wutar rikici ke kara ruruwa a tsakanin shugabannin kasashen biyu, inda wasu al'ummomi da ke cikin da'irar makaman masu linzaminta sun fara shirye-shirye da gaske.

A Japan, kauyuka sun fara shirin tunkarar harin nukiliya. Hawaii ta fara bitar ka'idoji ga al'umma kan matakin da za su dauka idan makamin nukiliya ya tarwatse, kamar yadda kananan hukumomin Amurka da ke Yammacin gabar teku ke yi.

Daya daga wurare da Koriya ta Arewa ke yi wa barazana, shi ne bangaren Amurka na Guam, inda ba da dadewa ba aka bayar da umarni kan yadda za a tarairayi tarsatsin sinadarai (masu guba) (duba 'shawarar Armageddon," a kasa).

Baya ga haka sashen tsaron cikin gida na Amurka kwanan nan ya fito da shafin sadarwar intanet mai lakabin Ready.gov, wanda ya kunshi sashen da ke bayani kan tarwatsewar makamin nukiliya.

A sauran kasashe, an kashe karsashin kariya ga fararen hulu ta yaddda a ''yan shekarun nan ba ya cikin tsare-tsaren da aka sa a gaba.

A shekarun 1980, Birtaniya ta bullo da dimbbin dabarun kariyar fararen hula a matsayin matakan zama cikin shiri, wadanda ssuka hada masu kula da yankuna a daukacin fadin kasar al'amarin da zai taimaka wajen ci gaban ayyukan gwamnati.

Sauran kuwa su ne jiniyar ankararwar harin sama da fadakarwa, wadanda aka bayar da umarnin yi wa al'umma.

Alal misali an girke jiniya a dubban wurare. Za a iya yin amfani da su wajen ankararwar farmakin makami mai linzami ko su yi karajin nuni da tartsatsin rugugin sinadarai, wadanda tuni an dakusar da yin su.

Shin za a ci gaba da amfani da dabarun zamanin yakin cacar baki idan aka fara musayar wutar makaman nukiliya? Lamarin ya zo da sauki domin ba a taba yi musu gwaji na hakika ba.

"Matsalar da ke tattare da wani al'amari shi ne bambancinsa da sauran al'amuran da ke bukatar matakin gaugawa," a cewar Patricia Lewis, daraktan sashen tsaron duniya a cibiyar farfajiyar Chatham. "Lamarin na da rikitarwa."

SHAWARAR ARMAGEDDON

Sakamakon barazanar Koriya ta Arewa, Guam ya wallafa ka'idoji kan yadda za a tarairayi kan harin nukiliya.

- Kada a kalli walwali ko tartsatsin wuta - don tana iya makantarwa.

- A nemi mafaka.. daga tartsatsin rugugin sinadarai mai cin nisan mila-milai. A tuna tsarin kariya guda uku: Nisa da mafaka da lokaci.

- kada a yi sanyar tsaftace jiki gwargwadon hali, don kakkabe burbushin sinadarai da ka iya baibaye jikinka.

-Tube tufafi na iya zam sanadin karkabe sinadarai da kashi 90 cikin 100.

-A daure kayan da suka gwamu da sinadarai a jakar leda ko a daure su. A jefar da tufafin nesa da mutane da dabbobi.

-A wanke jiki da sabulu da ruwa. Kada a dirje fata. Kada a yi amfani da na'urar kona gashi, saboda tana iya gwamuwa da sinadarai a gashinka.

- Ka bushe hancinka a hankali, ka goge idanunka da mayani mai danshi. A goge kunnnuwa a hankali.

A da, matakan kariya ga fararen hula a Birtaniya ba sa samun kyakkyawan tallafin kudi, inda aka takaita barazanarsu, a cewar Matthew Grant na Jami'ar Essex, wanda ya yi nazari mai fadin gaske a littafinsa mai taken 'Bayan harin bam: Kariyar fararen hula da yakin Nukiliya a Birtaniya, tsakanin 1945 zuwa 68.'

Kamar yadda Jennifer Cole ta Cibiyar Royal United Service (RUSI) ta bayyyana, yakin nukiliya ba ya cikin jerin hadurran da aka yi rajistarsu a Birtaniya, ko da yake akwai yiwuwar 'yan ta'adda su kawo harin bam din nukiliya, al'amarin da ake ganinsa a"matsayin faruwarsa ta yi karanci.'

"Hatsarin nukiliya ba wata matsala ce mai munin gaske ba a yanzu," in ji ta.

Asalin hoton, (Credit: AFP/Nikolay Doychinov)

Bayanan hoto,

Zane-zanen da aka baje a Bulgaria don tunawa da hadarin Chernobyl, al'amarin da ya yi nuni da mummunar illar da sinadaran makamin nukiliya ka iya haifarwa

Abokin aikinta a RUSI, Tom Plant, shi ma ya yi nuni da cewa jiragen ruwan yakin Birtaniya da ke dauke da makaman nukiliya suna cikin shirin ko-ta-kwana a kwanaki da dama' "tattare da ankararwar wuta."

Lokacin da yakin cacar baki ya yi Kamari, akwai yiwuwar a kaddamar da harin makamai masu linzami cikin mintuna 15.

"Ba ma cikin yanayin kariyar da ta haifar da yakin cacar baki, inda aka yi fama da zaman dar-dar," in ji shi.

Daukacin shirye-shiryen da aka yi cikin karni na 20 duk sun rushe.

Saboda rashin babbar barazana, mafi yawan shirye-shirye da gwamnatoci suka yi a karni na 20 ko sun watse ko kuma an karkatar da su ddon kariyar wasu musifun.

Tsare-tsaren da ake da su su ne na tunkarar dimbin ambaliya da harin ''yan ta'adda ko al'amarin da aka iya tarwatsa dimbin mutane al'amuran da aka karkatar da amtakan kariyar yakin cacar baki gare su, a cewar Cole.

Wadanne matakai aka girke a yau? Jigon al'amura a birtaniya matakan gaugawar tarairrayar rugugin sinadarai da fadakar da al'umma da ka'idoji. Alal misali a Portsmouth da Southampton.

Daukacin biranen Birtaniya wurare ne da aka girke jiragen ruwa dauke da makaman nukiliya. Don haka, majalisar birrnin na da cikakkkun bayanan matakan gaggawa karkashin tsarin Reppir don za a bi idan an samu hadarin tartsatsi da ruggugin sinadarai da za a iya bazawa a wuraren.

Shirin na nuni da cewa lokuta da dama turakun juya akalar makaman ba za ssu fashe a kashin kanssu ba.

Asalin hoton, (Credit: Chung Sung-Jun/Getty Images)

Bayanan hoto,

Dodon kariyar fuska da sauran matakan kariyar gaugawa da ke hanyoyin karkashin kasa a Seoul Koriya ta Kudu

Sansanin sojan ruwa na Portsmoutth na da tsohuwar jiniyar ankararwar kawo harin sama, wadda aka saba gwada daga lokaci zuwwa lokaci don kar-ta-kwana a yayin hadari.

Can a Birtaniya kuwa, sauran tsare-tsaren jiniyar ankararwar nan nan a girke, don ankararwa kan hadarin da ke tattare da gubar sinadarai da ke fitowa daga masana'antu.

Abin tambaya a nan shi ne, yaya mutum zai shawo kan illar bam din nukiliya da ke hakilon aukuwa?

Tabbas akwai wurare da dama a duniya da har yanzu ake da mafakar kariya daga nukiliya, wadanda suka hada da birrnin New York.

Sai dai wasu daga cikin wuraren fakewar tuni aka mayar da su wuraren ayyuka da ba su dace da mai neman mafaka ba, idan an kawo harin makaman nukiliya a kusa.

Kungiyar agajin duniya ta Redcross tana bibiyar matakan da za ta iya dauka akai-akai don tallafa wa kasashe daban-daban a sakamakon musifu da suka hada da fashewar makaman nukiliya.

"Idan muka dubi wuraren da abin ya yi illa mintoci da yin illarsa," a cewar Johanny Nehme, shugaban sashen lalata makamai, "kusan a iya cewa babu abin da za a iya yi."

"Taimakon agajin da nike hasashe zai yiwu ne bayan makonni daga bisani."

Asalin hoton, (Credit: AFP/Getty Images)

Bayanan hoto,

Abincin gwangwani da aka tara a tsohuwar mafakar karkashin kasa ta Gwmanatin Ireland kusa da Ballymena da ke Arewacin Ireland

Kuma ya yi nuni da cewa a lokacin yaki, akwai tabbacin rufe kan iyakoki da hana jirage tashi, al'amarin da zai dakusar da ayyukan kungiyoyin jin kan al'umma da za su taimaka wa wadanda suka tsira.

Gaskiyar lamari bayan fashewar makamin nukiliya a birni na zamani, inda aka dakusar da ayyukan kungiyoyin jingar al'umma, daukin gaugawa da taimakon gwamnati zai yi matukar wuya ga wasu.

Sai dai Alex Wellerstein da masu hankoron kariya ga fararen hula na da kwarin gwiwa: akwai yiwuwar samun damar tsira idan an zauna cikin shiri da fadakarwa.

Wannan abu ne da kowa zai damu kansa da tunani a kai ba. Sai dai abin da ba a zata ba na iya faruwa, ta yiwu a yi tunanin haka ko da kadan ne don samun damar tsira.