Ana iya gane aikin kwakwalwar matattu?

Dubban marasa lafiya basu san halin da suke ciki ba Hakkin mallakar hoto AF archive / Alamy
Image caption Dubban marasa lafiya basu san halin da suke ciki ba

Daga Roger Highfield

Dubban marasa lafiya na nan a dabaibayin langabun rashin sanin inda kansu yake, a yanayin rai kwakwai, mutu kwakwai (tsakanin rayuwa da mutuwa).

Manyan masana kimiyya uku na kokarin ceto su, kamar yadda Roger ya kawo rahotanni al'amuran.

"Kaddara ka farka a cikin wani akwati, a cewar Adrian Owen.

"Ka ji garau tun daga kan yatsun hannu zuwa yatsun kafa. Lamarin ya yi bambarakwai a akwati tunda kana jin komai da ake yi a kewaye da kai, amma ba za a iya jin muryarka ba.

A gaskiya ma akwati garkame yake kam daure da fuskarka da lebanta ta yadda ba za ka iya magana ba ko wani surutu.

Da farko, wannan al'amari ya yi kama da wasa. Sai batu na gaskiya. Kana gani da jin yadda 'yan uwanka ke alhinin makomar da ka samu kanka. Ka daskare da sanyi.

Sai kuma ka dumame da zafi. Ko da yaushe kana fama da kishirwa ziyarar abokai da 'yan uwa sai ta ragu. Abokin zamanka shi ma ya dakata. Kuma babu abin da za ka iya yi kan haka."

Ni da Owen muna tattaunawa a kafar sadarwa ta Skyoe. Har yanzu ina nan a Landan, qasar Birtaniya, shi ma yana nan a Landan kimnanin mil dubu uku da rabi daga Jami'ar Western Ontario ta qasar Canada.

Jan gashin Owen da gemunsa da aka daddatse sun bayyana akan akwatin talabijin dina, inda aka yi mini zayyanarsa tare da kwatanta mini yadda wadanda ba sa iya magana ke shan azaba: marasa lafiyar da yake kula da su.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yi bincike don gano yadda za a kimanta rukunin farfadowa farkawa.

Mutanen da "rashin lafiya ta langabar da su" a farke suke ba tare da saninsu ba. Idanunsu a bude har a wasu lokutan suka jujjuya.

Suna iya yin murmushi, su kama hannun wani, su yi kuka ko gyaran muryta. Sai dai motsin tafa hannu bai dame su ba, ba sa iya gani ko fahimtar magana.

Motsinsu ba da niyya ko manufa, sai dai kwatsam ya bijiro. Alamu na nuna abin da ke damfare a kwakwalwarsu ya gushe, babu sosuwar zuciya ko kudura niyya, wasu dabi'u da suka ta'allaka a jikin daidaikunmu.

Tunaninsu ya garkame gam. Har yanzu dai, idan idanunsu suka bude, sai a barka da mamakin cewa akwai dan burbushin farkawa tattare da su.

Shekaru goma baya, amsar tambaya kan lamari kawai ba a bukatarta ko kuma a ce kawai a'a! Kada a sake bijiro da ita ko kadan, ta hanyar amfani da na'urar daukar hoton bibiyar kwakwalwa, Owen ya gano cewa wasu kawai a dabaibaye suke a daure cikin jikinsu, duk da haka suna iya yin tunani har su dan ji wani abu gwargwadon hali.

Yawan majiyatan da ke fama da matsalar kasa farfadowa suna karuwa a shekrun nan, wani abin mamakin ma shi ne likitoci sun samu dabarun ceto marasa lafiyar da suka samu munanan raunuka.

A yau, majiyatan da jikinsu ke dabaibaye da jagwabewa da tsukewar kwakwalwa sun mamaye asibitoci a fadin duniya -a Turai kawai yawan wadanda suke a some suna kaiwa kimanin 230,000 a kowace shekarta, inda daga cikinsu 30,00 ke kasancewa a yanayin langwabewa.

Irin wadanan su ne wadanda suka fi shiga matsanancin hali, inda ake tarairayarsu da na'urorin kula da lafiya na zamani masu tsada. Owen na da matukar fahimtar lamarin.

A shekarar 1997, wata kawarsa ta kud-da-kud ta ta shi yadda ta saba ta hau keke don zuwa wajen aiki. Anne (wadda aka sauya sunanta) ta samu nakasu a magudanar jininta da ke kaiwa ga kokon kai, wadda aka sani da raunannar jijiyar jinin kwakwalwa.

Minti biyar da fara tafiyarta, sai langababbiyar jijiyar makwararar jininta ta fashe, inda nan take ta yi karo da wata bishiya. Daga nan ba ta sake farfadowa ba.

Hotunan mutane da ke some a fina-finai irin su Hable con Ella (wasan kwaikwayon mutanen Spain da ke nufin yi mata magana) lamari ne da ya kauce wa hakikanin gaskiya.

Wannan musifa ta sa Owen ya shiga zurfin tunani, ta yarda hadarin Anne ya kawo masa sauyi tsawon rayuwarsa.

Daga nan ya fara jefa alamar tambaya kan marasa lafiyar da ke cikin matsananciyar suma da wadanda sumarsu ba ta ta'azzara ba, da kuma wadanda suka samu kansu a tsakanin al'amuran biyu (matsanaciya da sassaukar suma)?

A wannan shekarar, sai ya koma Cibiyar binciken Likitanci da ke nazarin fannoni kimiyyar kwakwalwa a Cambridge, inda masu bincike suka yi amfani da dabarun daukar hotuna daban-daban.

Daya daga cikin dabarun mai lakabin PET na nuna yadda kwakwalwa ke gudanar da ayyuka, wadanda suka hada da amfani da iskar oxygen da sarrafa sukari.

Gudar dabarar kuwa mai lakabin fMRI na nuna sassan kwakwalwa da ke aiki ta hanyar gano dishi-dishin jini da ke kwarara da yawa. Owen ya cika da tunanin yin amfani da wannan fasahar kere-kere ga majiyata, irin kawarsa da ke halin rai kwakwai, mutu kwakwai.

Kudurin farfadowa

Tsawon rabin karni da ya wuce, idan zuciyarka ta daina bugawa sai a tabbatar da mutuwarka ko da daukacin jikinka na farke sai kawai likitoci su turaka wajen adana gawa (macuware).

Wannan lamarin shi ke nuni da cewa a tarihi an sha samun wadanda "suka mutu, suka farfado."

Tamkar yadda ta faru a shekarar 2011, inda a Majalisar Lardin Malatya da ke tsakiyar kasar Turkiyya ta ba da sanarwar kera macuware mai nakararwa da kofofin sanyaya gawa da ake iya bude su daga ciki.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jenett ya kirkiro ma'aunin sumar Glasgow (Glasgow Coma Scale) don kimanta yanayin suma

Matsalar dai ita ce har yanzu ma'anar da kimiyya ta bai wa "mutuwa" ba a cimma matsaya kanta ba, tamkar yadda "farkawa" take.

Kasancewa a raye yanzu bas hi da alaka da bugun zuciya, kamar yadda Owen ya bayyana. Idan ina da zuciyar dashe, shin na mutu ke nan?

Idan na'urar na tarairayar rayuwarka, ana nufin ka mutu ke nan? Gazawar ngudanar da harkokin rayuwa a kashin kai na nufin mutuwa ke nan?

A'a, sabanin haka lamarin yake, domin da tuni daukacinmu mun "mutu" cikin watanni tara kafin a haife mu.

Lamarin na dada rincabewa idan muka yi la'akari da wadanda ke dabaibaye a tsakanin rayuwa da mutuwa - tun daga kan wadanda suka san inda suke da ma wadanda ba su san inda kansu yake ba, wadanda ke dabaibaye a "tsukukun sumar farkawa,' har zuwa kan wadanda jikinsu ke langabe ko doguwar suma.

Wadannan majiyatan alamu na nuna a farke suke ta hanyar kakaba musu bututun shaker iska cikin shekarun 1950 a kasar Denmark, wata kirkirar fasaha da ke nuni da karshen rayuwa bisa la'akari da da mutuwar kwakwalwa, ta hanyar samar da kyakkyawar kulawa, inda ake gane marasa lafiyar da suka ki tashi sai a kimanta su a matsayin "langababbu" ko "taushin jiki (irin na kifi mai fila-filai - jelly fish)".

Kamar yadda aka saba duk sa'adda ake yi wa marasa lafiya magani, yanke matsaya na da wahala: wato fahimtar yiwuwar rayuwarsa, tattare da alfanun maganin da ake yi da sauran al'amuran da suka danganta kan hakikanin cutar da aka gano.

A shekarun 1960, masanin sarrafa sakonnin kwakwalwa Fred Plum a New York da mai tiyatar jijiyar laka Bryan Jennett a Glasgow su suka fara gudanar da bincike don gano yadda za a kimanta rukunin farfadowa farkawa. Plum ya kirkiro lakabin "matsalar dabaibayewa," inda mara lafiya ya san inda kansa yake a farko, amma ba zai iya motsi ko Magana ba.

Tare da Plum, Jenett ya kirkiro ma'aunin sumar Glasgow (Glasgow Coma Scale) don kimanta yanayin suma, sai Jennett ya sake samar da wani ma'aunin sakamakon Glasgow don kimanta yanayin farfadowa, wato daga mutuwa zuwa 'yar karamar nakasa.

Gaba dayansu sai suka rika amfani da lakabin matsanancin langabewar jiki" ga marasa lafiyar da suka rubuta "kimar lokacin farfadowarsu da zarar idanunsu sun bude suna motsi; tasirin warkewarsu an ta'allaka shi ga motsin gabobi ko karsashin gabar da aka taba, kuma ba sa taba yin magana."

A shekarar 2002, Jennett na cikin gungun masana aikin kwakwalwa da suka yi furucin "farkawa kadan" don kwatanta wadanda a wani lokaci suke a farke tare da dan sanin inda kansu yake, da ke nuna alamun farkawa ta yarda a wani lokaci za su iya bin umarnin abin da aka ce su yi, wasu kuwa ba za su iya ba.

Har zuwa yau, ana ci gaba da taqaddama kan wane ne ya san inda kansa yake da kuma wanda bai sani ba.

Labarai masu alaka