Pogba ba zai buga wasan Man City ba

Alkalin wasa ya ba wa Pogba jan kati a wasansu da Arsenal ranar Asabar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alkalin wasa ya ba wa Pogba jan kati a wasansu da Arsenal ranar Asabar

Dan wasan Manchester United Paul Pogba ba zai taka leda a wasan da kungiyarsa za ta kara da Manchester City, sakamakon jan katin da aka ba shi a wasan da suka fafata da Arsenal.

Alkalin wasa Andre Marriner ne ya fitar da mai tsaron tsakiyar United din, bayan da ya taka mai tsaron bayan Arsenal Hector Bellerin a minti na 74 da fara wasan.

Har ila yau dan kwallon mai shekara 24 ba zai buga wasan da kungiyarsa za ta karbi bakuncin Bournemouth ranar 13 na watan Disamba ba, da kuma wasan da za su buga a gidan West Brom na ranar 17 ga watan Disamba ba.

Pogba ya dawo wasa ne bayan da ya shafe wata biyu yana jinya.

Labarai masu alaka