Yadda kudi ke sauya maka dabi’a

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ba mamaki ka taba zama a majalisar hira, inda mai kudin cikinku shi ne na karshen daukar nauyi idan an tashi sayen wani abin motsa baki.

Mai yiwuwa ne ka tambayi kanka dama can rowar ce ta basu damar tara kudin ko kuwa mallakar kudi ke sa mutane su tsiri rowa?

Wannan tambaya ce mai sarkakiya wacce za a iya tunkararta ta fuskoki dabam-daban.

Ka na iya daukar wani rukunin mutane da ke da dangantaka da harkokin kudin, kamar masu ilimin nazarin tattalin arziki, ka gwada kyautarsu da ta sauran jama'a.

Wani bincike da aka yi a 1993 ya gano cewa daliban nazarin tattalin arziki da su ka ce ba su taba bada sadaka ba sun nunka dalibai masu nazarin taswirar gine-gine da ilimin halayyar dan Adam wadanda ba sa ba da sadaka.

Binciken ya kuma gano cewa daliban nazarin tattalin arzikin sun fi sauran dalibai rashin kyautawa a wasannin da ke bukatar hadin kai irin su Prisoner's Dilemma.

Da aka gwada dalibai a farkon fara digirinsu da kuma bayan kammalawarsu, wadanda ke karantar wasu fannonin kan kara yawan sadakarsu yayin da su ke kammala makaranta amma masu karantar fannin tattalin arziki su na nan yadda su ke lokacin da su ka shiga makaranta.

Amma fa wannan sakamakon jimillar dalibai ne don kuwa ba a rasa daidaikun daliban tattalin arziki masu hannun kyauta.

A hakikanin gaskiya ma, akwai hujjar da ke nuna cewa masu kudi, ko kuma dai akalla mazauna unguwanni masu tsada sun fi talakawa kirki.

Masu bincike sun kewaya unguwannin birnin London 20, inda su ka zubar da wasiku 15 a kowacce unguwa.

Kowacce wasika na cikin ambulan da aka rubuta adireshi kuma aka manna kan sarki.

Daga nan sai su ka koma su ka jira su ga adadin wadanda za a tsinta a kai gidan waya.

A unguwannin masu kudi irin su Wimbledon kaso 87 aka aika da su, amma a unguwannin talakawa irin su Shadwell kaso 37 kawai aka samu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akwai yiwuwar mutanen dake zaune a unguwanni masu galihu su rika bada sadaka, koda yake mai yiwuwa saboda suna da saukin kai kuma cikin farin ciki

Bugu da kari, masu kudi sun fi ba da kyautar da jama'a ba za su sani ba, kuma babu damar wani ya rama musu nan gaba.

Misali, Kristin Brethel-Haurwitz da Abigail Marsh da ke jami'ar Georgetown sun yi kokarin gano dalilan da ke sa akan samu gagarumin bambanci tsakanin sassan kasar Amurka a adadin masu bada kyautar koda ga mutanen da basu san su ba.

Sun yi la'akari da dalilai da dama ciki har da riko da addini, amma babban abinda su ka gano ya na da tasiri kan karuwar masu bada kyautar koda ga mutanen da basu san su ba shi ne karuwar kudin shiga ga al'umma.

Wato dai jihohin da mutane su ka fi samun kudin shiga su ne su ka fi bada kyautar koda.

Wannan ba lallai ya na nufin cewa masu kudi sun fi talakawa bayar da kyautar kodar ba ne, amma dai ya na nufin akwai dangantaka tsakanin kyauta da samu koda yake karuwar lafiya wacce ita ma ta na da alaka da samu, na iya sa mutane su kara zama masu kyauta.

Wato ke nan idan ka dauke daliban tattalin arziki na shekarun 1990, masu kudi sun fi mara sa karfi zuciyar bayarwa.

Wannan haka ya ke idan ba ka karanta nazarin Paul Piff na jami'ar California Berkely ba.

A wani bincike da ya yi, ya raba wa mutane takardu dauke da wasu maganganu domin gwada son kai.

Misalin maganganun shi ne 'In da ina cikin jirgin Titanic na cancanci a cece ni cikin kwalelen farko.'

Masu kudi ne su ka fi amincewa da wannan maganar fiye da talakawa.

Masu kudin kuma su ne su ka fi amincewa da ba sa kuskure, sun kware akan komai, kuma su na duban madubi kafin a dauki hotonsu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A wani binciken dabam kuma, Piff ya tara mutane da ke samun kudin shiga hawa-hawa ciki har da masu samun akalla $200,000 a shekara, inda ya ba kowannensu $10 kuma ya basu damar su yi sadaka da duk abin da su ke so daga ciki.

Piff ya gano cewa talakawan cikinsu sun fi bayarwa da auki.

Amma fa ku tuna, wadannan mutanen daman masu kudi ne tun kafin Piff ya gwada su.

Mai yiwuwa ba kudin ne ya sauya musu dabi'a ba, dabi'ar ce ta taimaka musu su ka yi kudin. Ba mamaki tsimi da tanadi, tare da jin cewa sun cancanci komai a duniya, su ne su ka taimaka musu su ka yi kudin.

To me zai hana a azurta wani mutum a dakin gwaji don ganin ko hakan zai sauya masa dabi'a?

Akan haka ne Piff ya sa mutane su ka yi wasan Monopoly amma da wani bambanci guda.

A farkon wasa sai aka yi 'yar-canke.

Wanda ta fada kansa ya fara wasan da nunkin kudin da ake ba sauran 'yan wasa sannan kuma ana ba shi nunkin abinda ake ba ragowar duk san da ya zagayo filin wasan.

Kamar yadda kowa ya za ta, 'yan wasan da suka samu wannan karin su ne kan lashe gasar.

Sai dai Piff ya buya a wani dakin dabam ya na kallon wasan ta cikin madubi domin ganin wadanne abubuwa ne kuma za su sauya bayan da dan wasan ya yi kudin gan-gan.

Da yawansu kan cika baki a lokacin wasan.

Wasunsu kuma su kan debi fiye da kasonsu a kayan kwalan-da-makulashen da ke kan teburin wasan.

Bayan kammala wasan, Piff ya kan tambaye su menene sirrin nasararsu, inda su kan yi bayanin kokarinsu da hikimarsu.

Amma ba a samu ko guda daya da ya ce nunkin kudin da aka ba shi ne ya jawo masa nasarar ba.

Don haka, mai yiwuwa ne samun kudi, ko da na wucin-gadi ne kan sa mutane son-kai.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Motoci masu tsada ba kasafai suke tsayawa masu tafiya da kafa don su tsallake titi ba, mai yiwuwa hakan na nuna cewa direbobi attajirai basu da dabi'a mai kyau

Piff ya kuma gudanar da wani nazarin a wata mahadar hanya a garin San Francisco domin ganin motocin da suka fi tsaya wa a danjar bada hannu tsakanin masu tsada da masu arha.

Idan ka ce matukan motoci masu arha ne suka fi matukan motoci masu tsada tsayawa a danjar bada hannu, to ka cinka.

Amma dai tuka mota mai tsada ba lallai ya na nufin mallakar kudi ba.

Mai yiwuwa ne matukan motocin direbobi ne ba su su ka mallake su ba. Ko kuma talakawa ne da suka sayi motar bashi.

Stefan Trautmann na jami'ar Heidelberg ya yi kokarin kaucewa wadannan rudanin inda ya yi amfani da sakamakon nazarin mutane 9,000 da ake gudanarwa a hukumance a kasar Netherlands sau hudu a shekara.

Ya gano cewa masu kudi sun fi dogaro da kansu tare da rashin shiga harkokin jama'a.

Sai dai kuma lokacin da ya gwada su a wasannin da suka shafi rike amanar kudi, bai samu wani bambancin cin amana tsakanin masu kudi da talakawa ba.

Da alama dai sakamakon nazarce-nazarcen da ke gwada halayyar taimakon al'umma tsakanin masu kudi da talakawa sun ci karo da juna.

To ina labarin alkaluman kididdigar adadin kudaden da ake bayarwa sadaka?

Shin Warren Buffet - biloniyan da ya yi alkawarin bayar da fiye da kaso 99 na dukiyarsa - ya fita daban ne ko kuma masu kudi sun fi bada kaso mai tsoka na dukiyarsu a matsayin sadaka?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akasarin mutane ba su da mu ba su ba da kashi 2.3 na kudin da su ke samu a matsayin sadaka

Masu bincike a kwalejin Boston sun tattara wadannan alkalumma tun daga masu samun $10,000 a shekara zuwa masu $300,000, inda su ka gano cewa kowanne rukuni na al'ummar kasar Amurka na bayar da kaso 2.3 na kudin shigarsu a matsayin sadaka.

Amma masu kudin kololuwa, wadanda ke samun fiye da $300,000 a shekara, su na ba da akalla 4.4 na kudinsu ne a matsayin sadaka.

Don haka masu tsananin kudi za su iya cewa sun fi kowa ba da sadaka.

Wannan bincike na Boston na nuna cewa sadakar masu kudi bata gaza ba kuma bata dara ba idan aka kwatanta da ta sauran jama'a.

Sai dai masu kudin da ke matakin kololuwa.

Ka na iya cewa ai su ba za su ji ciwon fitarsu ba, amma dai ai ganin dama su ka yi su ka bayar.

Don haka nan gaba, idan ka lura mai kudin majalisarku baya azamar biya muku kudin abin motsa baki, ka sani cewa mai yiwuwa ne ba kudi ne ya sa shi rowa ba; dama dabi'arsa ce.

Bincike dai ya nuna cewa masu kudi na sadaka sosai, amma darasin da ke ciki shi ne a kaucewa son-kai, musamman ma idan ana wasan Monopoly.

Idan kana son karanta labarin a harshen Ingilishi latsa nan: The complicated ways that money messes with your morals