Ko kun san amfanin kunya?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane masu jin kunya sun ba da gagarumar gudunmawa a duniya

Duk ranar da ka ji ka na dari-dari saboda kunya, ka tuna Agatha Christie.

A watan Afrilun 1958, wasan kwaikwayon da ta rubuta, 'The Mousetrap' ya zamo wasan da aka fi dadewa a na yi a gidajen wasannin dandamali na Burtaniya, bayan da aka gudanar da shi a kwanaki 2,239 a jere.

Mashiryin wasan ya tsara wata liyafa a Otal din Savoy domin murnar wannan nasarar.

Ta sanya doguwar rigarta koriya da fararen safar hannu na fata wadanda su ka kai har gwiwar hannu sannan ta tunkari dakin da ake liyafar.

Sai dai a bakin kofa mai gadi bai shaidata ba, don haka ya hana ta shiga.

Maimakon ta ce masa "Ba ka san ko wacece ni ba?", marubuciyar mai shekaru 67 sai ta juya ta samu wuri a harabar otal din ta yi zamanta.

Duk da littattafanta sun fi na kowanne marubuci a zamaninta kasuwa, ta ce ta na fama da "matsananciyar kunya".

"Har yanzu na kan ji kamar cewa ni marubuciya ce," a cewar Agatha Christie.

Ta yaya matar da ta ke da irin wannan daukaka za ta zama mara kwarin gwiwa?

Wannan ita ce tambayar da wani sabon littafi 'Shrinking Violets' ke kokarin amsawa ta hanyar nazari kan kunya a fagen siyasa, adabi da kuma nazarin dabi'ar bil'Adama.

Kunya ba'a bakin komai ta ke ba ga wadanda ba su da ita, amma kamar yadda Moran ya bayyana, kunya kan iya kai wa ga mutuwa dungurungum;

Shaharren likita ba'amurke Henry Heimlich ya taba cewa "wani lokacin, mutumin da ya kware lokacin da yake cin abinci, kunya za ta sa ya yi kokarin boye halin da ya shiga, har ya samu ya fice daga wurin cin abincin ba tare da kowa ya lura da shi ba.

Sai dai kuma, ya na iya somewa a waje, har ya mutu ko ya samu wata cutar kwakwalwa kafin a samu mai kai masa dauki".

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Duk da cewa ta sayar da miliyoyin litattafai data wallafa Agatha Christie tana fama da matsananciyar kunya

Moran ya ce tun tasowarsa ya na da matukar jin kunya - kuma ya fahimci irin halin da Christie ta shiga.

"Idan ni ma hakan ta same ni, iyakar abinda zan yi ke nan."

Mai yiwuwa ne ma kunyar ce ta yi tasari kan zabin abubuwan da zai rinka nazari a kansu.

Littattafansa na baya kan yi duban tsanaki ne kan al'amuran yau da kullum.

Misali 'Queueing for Beginners' ya bada tarihin abubuwa irin su famfo da bargon shimfida da bin layi domin sayayya a kanti.

'Armchair Nation' kuma ya yi nazari kan kallon talabijin a Burtaniya. "Ina ga kunya na sa ka yin nazarin dabi'u saboda kai kullum a matsayin dan kallo ka ke."

Moran ya ce: "Ita kunya wata dabi'a ce mai karo da juna, wacce ta kan zo ta koma." Don haka ne ya mai da hankali wurin nazarinta.

Image caption Bill Gates mutum ne da baya son shiga mutane inda yake shafe lokaci mai tsawo yana zaune shi kadai a kamfaninsa

A cikin littafin, Moran ya bada misali da wani basarake a karni na 19, Duke na Portland wanda ya gina hanya mai tsawon mil 15 a karkashin gidansa don ya samu kewayawa daga daki zuwa daki ba tare da ya hada ido da masu aikinsa ba.

Sai dai kuma ba duk masu jin kunya ne ba sa son hulda da mutane ba.

Kamar yadda Susan Cain, marubuciyar littafin 'Quiet' ta bayyana, akwai bambanci tsakanin jin kunya da kuma gudun hulda da mutane.

Wasu misalan da Moran ya kawo sun hada da masanin kimiyya Charles Darwin (wanda ya ce "ba shi da wayerwar hulda da jama'a' kuma 'ba shi da fasahar jawabi"), da 'yar fim, Keira Knightley (wacce ba ta iya hira a wurin liyafa), da marubuci Oliver Sacks, da shugaban kasar Faransa Charles de Gaulle, da mawaki Morrissey.

Wasu daga cikin fitattun mutanen na amfana ne da abinda Jamusawa ke kira "Maskenfreiheit" wato 'yancin da ka ke samu a ranka idan ka sanya abinda zai rufe fuskarka.

Ma'ana, idan su na jawabi ga dimbin jama'a, za su ji kamar ba su ba, su yi ta zuba, amma da sun kare jawabin sai kunya ta lullube su idan su ka kebe da 'yan mutane kadan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rahotanni sun ce Dirk Bogarde na firgita a duk lokacin daya hau kan dandamalin wasa

Tabbas dai kunya ba ta hana samun daukaka a rayuwa.

To amma anya ta na da wani amfani?

Wasu masanan sassauyawar halittu na cewa kunya dadaddiyar dabi'a ce da ta taimaki kakannin kakanninmu wurin samun tsira a rayuwa.

Binciken da aka yi baya-bayan nan akan halayyar dabbobi, sun gano cewa jin kunya da dari-dari kan taimaki dabbobi da dama.

Yayinda gwarazan dabbobi sun fi samun abokan jima'i da abinci, masu kunya, da ke labewa a gefe, sun fi tsira daga mahara.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu mutane irin su Keira Knightley kan nuna alamun kwarin gwiwa a fagen wasa amma suna matukar jin kunya

Sai dai Moran na ganin wannan ba shi ne cikakken bayanin kunya ba.

A ganinsa, abinda ke jawo kunya shi ne baiwar da mutane su ke da ita na yin tunani game da kansu da kuma irin kallon da al'umma ke yi musu.

Haka kuma amfani da harshe ya kara taimakawa wurin samun kunya a tsakankanin mutane.

"Maganganun da mu ke yi na kiyasta abubuwan da ke zukatanmu ne don harsunan ba za su iya isar da sakonmu dari bisa dari ba.

Ina ga abinda ke faruwa shi ne, mutane masu kunya sun fi fahimtar wannan nakasar."

Hakan na haifar da dabi'ar nan da akan ce "ta baya, ta rago," wato sai bayan ka bar inda aka yi magana ka fara tunanin ai da na ce kaza da kaza.

Amma mai yiwu ita ma da ranarta.

"Mafi yawan marubuta da masu ayyukan fasahar da na ba da labarinsu a littafin nan sun yi ayyukansu ne sanadiyyar tunanukan da kan zo musu bayan an kammala magana.

Ban ce duk marubuci ko mai aikin fasaha ya dogara da irin wannan matsalar don yi masa kaimi ba, amma dai ana samun da yawa wadanda dalilin rubutunsu ke nan," in ji Moran.

Moran ya kuma yi nazari akan bambancin kunya tsakanin al'umomin kasashe dabam-daban, inda wasu kasashen su ka fi wasu daurewa kunya.

Misali, a kasar Finland, akwai karin maganganu da dama da ke nuna muhimmancin kunya irin su "kalma daya na iya jawo matsala mai yawa", ko "karen da ke haushi bay a kama zomo".

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Wake Wake hanyoyi ne da mawaka kamar Morrissey ke bayyana irin halin da suke ciki a rayuwarsu ta yau da kullum

Sabanin haka kuma, a kasar Amurka, ana daukar kunya a matsayin wata cutar tabin hankali, abinda ke damun wasu masu nazarin halayyar dan Adam da ke ganin wannan dabi'a ce kurum ta mutane ba wai cuta ba.

Kundin bayanin cututtukan kwakwalwa na Amurka ya bayyana samfuran cutar kunya da ya ce sun hada da "makunyaciyar mafitsara" (wato kasa yin fitsari a magewayin al'umma), da kuma "kurumtar jefi-jefi" (wato kasa magana a gaban wasu mutanen).

Hanyoyin warkar da cutar kunya a Amurka sun hada da bada horon magana da dabarun hulda da jama'a da kuma amfani da magunguna masu rage dar-dar.

"Zuciyata ta rabu biyu game da wannan mataki," in ji Moran.

"Yayinda na ke ganin akwai mutanen da kunyarsu ta kai intaha da har za a iya kiranta cuta, ina kuma tunanin cewa mai da kunya baki dayanta cuta ba daidai ba ne domin kuwa dabi'a ce ta bil'adama."

Bayan da ya kammala rubuta littafinsa, yanzu Moran ya fahimci cewa ashe akwai mutane da yawa da ke jin kunya, fiye da yadda ya yi tsammani.

"Daya daga cikin manyan kura-kuran da masu jin kunya ke yi shi ne su dauka kamar su kadai ne ke fama da ita."

Ba mamaki littafin na Moran ya zama silar da masu jin kunya za su bayyana kansu tare da yin alfahari da dabi'arsu.

Idan kana son ka karanta na turanci sai ka latsa nan: Why we should celebrate shyness