Me ke sa jarirai kyalkyala dariya?

babies Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Su dai jarirai ba za a ce suna jin wani abin ban dariya ba, to in haka ne me yake sa su kyalkyala dariya a wasu lokutan.

Amsar wannan tambaya na iya bayyana abubuwa da yawa da zuciyarmu ke yi inji Tom Stafford.

Me yake sa jarirai yin dariya? Wannan tambaya ce da za a ce mafi ban dariya da mai bincike zai duba, to amma fa akwai wani babban dalili na kimiyya da ya sa Caspar Addyman ya sa yake son gano wannan amsa.

Wannan masani ba shi kadai ba ne da ya taba wannan tambaya. Darwin ya yi nazarin dariya a kan dan jaririnsa, Freud kuma ya samar da wani nazari da ke nuna cewa abin da ke sa mu dariya yana samuwa ne daga yadda muke fifita kanmu a kan wasu.

A dangane da haka ne muke jin dadi idan mun ga wani yana cikin wata matsala, misali a irin faduwar nan ta 'yan bori da mutum kan yi a wasan kwaikwayo na ban dariya da kuma wani hadari da za ka ga abin tausayi ne amma kuma sai ka yi dariya, saboda ba a kanka abin ya faru ba.

Babban masanin ilimin tunanin dan-adam, Jean Piaget yana ganin za a iya amfani da dariyar jarirai a fahimci abin da yake ransu.

Idan ka yi dariya to lalle kam ka ga wani abin ban dariya ne, domin abin ban dariya mai kyau yana kasancewa ne tsakanin yanayin da mutum yake na halin da ba ya tsammanin abin da kuma yanayi na rudewa da kuma yanayi

na kasancewa da ba za a iya hasashen halin da mutum yake ciki ba da kuma yanayi na gundura.

Masanin ya ce, saboda wannan, nazarin lokacin da jarirai ke dariya zai iya zama wata babbar hanya ta sanin yadda suke daukar duniyar nan.

Duk da cewa tun a shekarun 1940 ya yi wannan bayani,har yanzu ba a jarraba wannan tsari da ya ayyana ba sosai.

Haka kuma duk da cewa wasu fitattun masana sun yi nazari a kan lamarin na dariyar jarirai, masu nazarin ilimin tunanin dan-adam na zamanin nan sun yi watsi da binciken.

Addyman na Birkbeck na Jami'ar Landan ya kudiri aniyar sauya wannan. Shi yana ganin za a iya amfani da dariya a san daidai yadda jarirai suke daukar duniya.

Masanin ya kammala bincike mafi girma a kan abin da yake sa jarirai dariya, inda ya gabatar da rahotansa na farko a wurin taron duniya kan nazarin al'amuran jarirai a birnin Berlin a shekarar da ta wuce.

Ya gudanar da binciken ne ta hanyar shafinsa na intanet inda ya tambayi sama da iyaye dubu daya daga kasashen duniya daban daban, ya tambaye su lokaci da wuri da kuma abin da ke sa jariransu dariya.

Sakamakon ya kasance kamar shi kansa abin binciken wato abu mai dadada zuciya.

Jariri yana murmushinsa na farko ne a kusan watanni shida na haihuwarsa, yana kuma dariyarsa ta farko ne lokacin da ya kai kusan wattani uku da rabi( ko da ike wasu sukan kai linki uku na wannan lokaci kafin su fara dariya, saboda haka ka da ku damu idan jaririnku bai fara dariya ba har yanzu)

Hakkin mallakar hoto Hakkin mallakar hotoTHINKSTOCK

Wasan buya yana sa yara dariya sosai amma abin da ya fi sa su dariya kai tsaye shi ne cakulkuli.

Bincike ya nuna jarirai ko kananan yara za su fi yin dariya idan suka fadi maimakon idan wani ya fadi.

Wani abu mai muhimmanci shi ne daga lokacin da jariri ya fara murmushinsa na farko, amsar da iyaye suka bayar kan binciken ta nuna cewa jarirai suna murmushi tare da sauran mutane(wato idan aka yi musu) da kuma murmushin kan abin da suke yi.

Yi musu cakulkuli kadai bai isa ya sa su murmushi ba kamar yadda buya da fitowa ko bayyana kadai ba zai sa su murmushi ba.

Wadannan abubuwa biyu na cakulkuli da wasan buya suna zama abin dariya ko murmushi a wurinsu ne idan babban mutum ya yi musu domin sa su murmushin.

Wannan ya nuna cewa yadda yara ko jarirai suke kafin su fara tafiya ko magana su da dariyarsu abubuwa ne na walwala.

Idan ka yi wa yaro cakulkuli yana dariya ne saboda kana yi masa cakulkulin amma ba wai kawai domin ana yi masa cakulkulin ba.

Wani abu kuma shi ne kamar yadda bayani ya kasance a can baya, yara ba kasafai za su yi dariya idan suka ga wani ya fadi ba, amma idan su suka tintsire, za su iya yin dariya, kamar yadda ba lalle su yi dariya ba idan wasu

suna farin ciki, amma idan suna cikin wata 'yar damuwa ko wani abu na rashin dadi ya shammace su za su iya yi.

To daga wannan sakamako na binciken da Freud ya yi, wanda ya gudanar ta hanyar tattaunawa ko tambayar iyaye maimakon wani bincike mai zurfi a kan su kansu jariran ko yara wadanda abin ya shafa, sai a ce binciken ba shi da makama.

Ko da ike dai iyaye na cewa jarirai maza sun fi mata yin dariya kadan, to amma dukkanin jinsin jariran suna daukar iyayensu maza da matan masu ban dariya.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Jarirai suna daukarmu masu ban dariya duk da cewa sun yi kankanta su fahimci mai ya sa

Addyman yana ci gaba da tattara bayanai kuma yana fatan yayin da sakamakon ke kara bayyana abubuwa zai iya amfani da bincikensa ya nuna yadda dariya za ta sa a fahimciyadda jarirai ko yara suka dauki duniya.

Addyman ya ce, duk da muhimmancin da bincike a kan dariyar jarirai yake da a fagen kimiyya, abin mamaki shi ne, ba a ba wannan bincike muhimmanci ba.

Wani daga cikin dalilan hakan shi ne, wahalar da ke tattare da sanya jarirai dariya a dakin bincike, ko da ike, ya kuduri aniyar shawo kan wannan matsala a kashi na gaba na aikin binciken.

Amma kuma ya ce yana ganin ba a mayar da hankali a kan lamarin ba ne saboda ta wani fanni ba a dauki lamarin a matsayin wani abu mai muhimmanci da kimiyya za ta duba ba.

Wannan bambanci ne da Addyman, ya yi niyyar kawo karshensa, domin a wurinsa bincike kan dariya abu ne ba na ban dariya ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why do babies laugh out loud?