Shin akwai wani mutum da ke rayuwa a cikin jikinka?

ARIKO INAOKA Hakkin mallakar hoto ARIKO INAOKA

Za ka dauka cewa jikinka da zuciyarka naka ne kai kadai. To amma halittu da dama ne suka tattaru suka samar da kai, wadanda suka hada da wani mutumin.

David Robson zai yi maka bayani:

Asalin yadda ka samu a duniya ba wani abu ne mai wuyar sani ko fahimta ba idan ka duba dabi'ar auratayya tsakanin namiji da mace.

Ka faro rayuwarka tun daga cikin mahaifiyarka, har ka fito duniya kana wutsul-wutsul da kuka, rabinka babarka daya rabin kuma babanka, kashi dari bisa dari kuma kai ne karan kanka ba wani ba.

To amma wannan labari yanzu ya sha bamban, ya zama mai sarkakiya, domin bayan kwayoyin halitta daga iyayenka, akwai tarin kwayoyin halittun bairus (virus) da bakteriya (bacteria) da kuma wasu mutanen a tattare da kai.

Idan kai 'yan biyu ne zai iya kasancewa kana dauke da wasu fannoni na abokin tagwaitarka a jikinka da kuma kwakwalwarka.

Wannan abu ne da ba ka sani ba har yanzu amma kuma kila yana tasiri wajen yadda kake gudanar da rayuwarka.

''Mutane ba halittu ba ne daidaiku halitta ce da ta kunshi wasu tarin halittun,'' in ji Peter Kramer na Jami'ar Padua da ke Italiya.

''A kwai halittu masu tarin yawa daban-daban wasu mutane ne wasu kuma ba mutane ba ne wadanda suke ta fafutukar iko a cikinmu.''

Wannan masani tare da Paola Bressan ya wallafa wata kasida a mujallar nan ta abubuwan da suka shafi kimiyyar tunanin dan-adama mai suna ''Perspective in Psychological Science'' a Ingilishi, in da yake kira ga masana tunanin dan-adam da likitocin kwakwalwa da su fahimci yadda wannan hadaka ke iya tasiri a dabi'armu.

Hakkin mallakar hoto ARIKO INAOKA
Image caption A shekaru shida da suka gabata mai daukar hoto Ariko Inaoka ya yi kokarin gano dangantakar da ke tsakanin 'yan tagwayen Iceland Erna and Hrefna

Watakila wannan ya zama kamar wani abin da zai tayar da hankali, to amma daman abu ne da aka dade da sani cewa jikinmu hadaka ce ta halittu daban-daban.

Akwai kwayoyin halitta a jikinka da suke iya samar da wasu kwayoyi da za su iya sauya yanayinka.

Wasu masana kimiyya ma sun ce suna ganin kwayoyin halittar ka iya sauya yanayin dandanonka, ka ji cewa kana bukatar abincin ka fi so.

Ita kuwa kwayar halitta ta cuta da ake kira Toxoplasma gondii a Ingilishi ka iya kai ka ga mutuwa.

A yanayi na halitta, ire-iren wadannan kwayoyin halitta suna nan a cikin kwakwalwar bera ta yadda suke sa yake jin tsoron kyanwa.

Haka kuma irin wadannan kwayoyi ne dai a kwakwalwar mutum da suke haifar masa da yanayi na sa ya ji yana kaunar ya hallaka kansa.

A yanzu kusan kashi daya bisa uku na naman da ake samarwa a Birtaniya yana dauke da wannan kwayar halitta mai cutarwa duk kuwa da an san cewa idan mutum ya kamu da su za su iya haifar masa da larurar tabin hankali. Kramer ya ce dole ne a dakatar da wannan.

A dalilin wannan, abu ne da ya bayyana karara cewa dabi'ummu ba namu ba ne gaba daya.

Wannan kadai ya isa ka binciki kanka, musamman ma idan ka gano cewa ba ire-iren wadannan kwayoyin halitta ba ne kadai suka mamaye kwakwalwarka ba har ma da sauran mutane.

Babban misali na zahiri a nan shi ne, na 'yan biyun da suke manne wuri daya wadanda suke da kwakwalwa daya in ji Kramer.

Amma kuma ya ce hatta tagwayen da ba a hade suke ba suna iya amfani da wasu halittu na jiki tare ba tare da sun san hakan na faruwa ba.

A matakin farko-farko na halitta, kwayoyin halitta kan iya rarrabuwa tsakanin 'yan biyu ko 'yan uku.

A da an dauka wannan abu ne da ba kasafai yake faruwa, amma yanzu abin mamaki mun gano cewa abu ne gama-gari.

Misali kusan kashi takwas cikin dari na 'yan biyun da ba su yi kama da juna ba da kuma kashi 21 cikin dari na 'yan uku ba rukunin jini biyu suke da shi maimakon daya.

Kwayoyin halittarsu ya samar da rukuni daya, dayan kuma kwayoyin halittar abokin tagwaitakarsu ne ke samarwa.

A takaice ke nan za a iya cewa su jiki biyu ne a dunkule wuri daya, wanda kuma hakan ba lalle ya tsaya a rukunin jini ba kadai zai iya kasancewa a wasu sassan jikinsu da suka hada da kwakwalwa.

Hakkin mallakar hoto ARIKO INAOKA
Image caption Yadda tagwaye ke girma a ciki tare suna iya musayar kwayoyin halitta yadda za su fi kusanci da juna fiye da yadda muka fahimta a da

Kwakwalwar da ke tattare da wasu sassa na daban za ta iya kasancewa da wasu matsaloli. Misali mun san cewa yadda tsarin halittar kwakwalwa yake abu ne da yake da muhimmanci kan yadda aikinta yake.

Saboda haka idan aka samu wasu bakin jijiyoyi ko kwayoyin halitta wadanda kuma wasu kwayoyin halitta ke tafikar da ayyukansu da wani sakon na daban, wannan zai iya rikita ayyukan kwakwalwar.

Wannan ne zai iya kasancewa misali dalilin da ya sa da wuya tagwaye su kasance masu amfani da hannun dama.

Wanda wannan gado ne na halitta da ke na dangantaka ko nasaba da ta shafi bangaren hagu da kuma na dama na kwakwalwa.

Watakila kasancewar kwakwalwa da wasu kwayoyin halittar na daban shi yake haifar da wannan sabani.

Ko da ba ka taba tunanin cewa kana da abokin tagwaitaka ba, akwai wasu hanyoyi da dama da wasu kwayoyin halitta na wani mutumin za su iya mamayarka.

Misali za ta iya kasancewa a lokacin da kake dan tayi ku tagwaye ne amma kuma ku hade ku zama daya yayin da halittarku ke girma, kuma ya kasance jikin mutum daya amma da halayyar kwayar halittar karin wani mutumin.

''Ga shi a zahiri kamar mutum daya ne kai amma kuma kana dauke da karin kwayoyin halittar wani mutumin a jikinka. Ka kasance kamar mutum biyu ne kai kenan in ji Kramer.

A wani lamari na daban, wata mata ta yi mamakin yadda aka sheda mata cewa ba ita ce ainahin mahaifiyar 'ya'yanta biyu ba.

Ana ganin abin da ya haddasa hakan zai iya kasancewa kwayoyin halittar wata 'yar uwarta sun zauna a jikinta ne, har suka shiga jikin wadannan 'ya'ya nata bayan da ta dauki cikinsu.

Duk ma dai yadda lamarin ya faru, abu ne da zai iya yuwuwa ace wani sashe na jikin wani mutum ya iya sa kwakwalwa ta kasance ta wata hanya da ba a yi tsammani ba, in ji Lee Nelson, daga Jami'ar Washington.

A yanzu dai tana gudanar da bincike ko abu ne da zai iya kasancewa samu dashen kwayoyin halittar uwa a kwakwalwar jariri.

''Bambanci na yawa ko irin kwayoyin halitta ko kuma na lokaci a lokacin da aka samu kwayoyin a jiki duka ka iya haifar da wasu matsaloli a jariri,'' in ji ta.

Nelson ta gano cewa ko da ka girma ne ba ka da kariya daga wadannan kwayoyin halitta masu kutse.

A 'yan shekarun da suka gabata Nelson da William Chan na Jami'ar Alberta da ke Edmonton sun dauki 'yan wasu sassa na kwakwalwar mata suka duba kwayoyin halittarsu, inda suka gano cewa kashi 63 cikin dari suna dauke da kwayoyin halittar maza.

A fahimtarsu suna ganin wadannan kwayoyin halittar sun shiga kwakwalwar matan ne daga jaririnsu maza ta cibiya.

Suna ganin wannan ya sa uwar ta rage hadarin kamuwa da cutar mantuwa can gaba a rayuwarta, ko da yake ba a san dalilin hakan ba.

Wasu masana kimiyyar ma na ganin wannan zai iya kasancewa abin da ke sauya yanayin halayyar uwar a lokacin da take dauke da juna biyu.

Hakkin mallakar hoto ARIKO INAOKA

Iliminmu na zaman mutum a matsayin wata halitta da ta kunshi halittu da dama bai kai ya kawo ba har yanzu saboda haka da yawa daga cikin abubuwan da muke fada abubuwa ne da suke matakin nazari a yanzu.

Kramer da Bressan ba suna nufin bayar da wata tartibiyar amsa ba ne da kasidarsu, illa dai kawai su fadakar da sauran masana tunanin dan adam da likitocin kwakwalwa game da sauran yawancin abubuwan da suka sa muka zama abin da muke a yau.

''Ba za mu iya fahimtar dabi'ar dan-adam ba ta hanyar nazarin wannan mutumin ko wancan mutumin ba kadai, ''in ji Kramer.

Dole ne mu fahimce su duka kafin mu fahimci yadda dabi'armu take.

Misali masana kimiyya sukan hada ko kwatanta tagwaye kafin su san asalin dabi'a.

Amma ksancewar hatta tagwayen da ba su yi kama da juna ba sukan yi musayar wasu kwayoyin halitta a kwakwalwarsu, wannan zai iya kawo cikas ga sakamakon binciken.

Ka da mu dauki wadannan bakin kwayoyin halitta masu kutse a jikinmu a matsayin abokan gaba, domin ko ba komai su suka sa muka zama abin da muke a yau.

''Ina ganin yanzu mun fahimci cewa wadannan bakin kwayoyin halitta sun dade a tare da mu, da dadi ba dadi muna tare,'' in ji Nelson.

''Kuma ina ganin alfanunsu ya fi rashin alfanunsu.''

Labarai masu alaka