An kirkiro na'urar keke mai nuna wa bako hanya

Hakkin mallakar hoto Beeline

BeeLine 'yar karamar na'ura ce da za ka makala a hannun kekenka, wadda ta ke aiki da masarrafar taswirar Google, sai kawai ta dukufa aikin nuna maka hanyar unguwa ko garin da za ka je.

Ga bayanin David K Gibson

BeeLine na'ura ce ta nuna hanya a keke wadda aka kera ta da zummar amfanar da wadanda basu ci gajiyar fasahar nuna hanyar wurare ta intanet ta ababan hawa wato GPS ba, masu hawa keke kenan.

Ba kawai yawo da keken ba ne ko kuma jin dadin kurda-kurda cikin lungu da sako na birane inda mota ba za ta iya shiga ba ne dadin hawa keke, wannan na'ura za ta kara maka armashin tattakinka a kan keken, inda za ta rika nuna maka wuraren wasu abubuwa ko harkoki da za ka iya bukata ko son ka sani.

Ita wannan na'ura ba wai tana nuna maka hanyar da lalle ita za ka bi ba ne, tana dai ba ka shawara ne kan inda za ka bi, sai ya rage naka ka zabi inda ya fi dacewa.

A lokacin da ba ka amfani da ita, za ka iya makale ita wannan na'ura ne a jikin dan mukullinta. Na'urar wadda 'yar siririya ce, da za ka makala ta a hannun kekenka, kuma tana aiki da fasahar Bluetooth da wayarka ta komai-da-ruwanka (smartphone).

Na'urar tana gaya maka nisan wurin da za ka je, da inda wurin yake ta hanyar alamar wata kibiya da ke nuna maka hanya.

Duk da cewa tana nuna maka hanya, amma kuma kana da damar ka yanke hukuncin inda za ka bi ka je, bisa la'akari da yanayin cunkoson ababan hawa da ma kila wani biki da ake yi a kan hanyar da sauran abubuwa.

Na'urar tana da maleji da ke nuna maka gudun da kake yi, ga kuma karin wasu maleji-malejin na nuna wasu abubuwan da za su kara tabbatar da cewa ka isa wurin da za ka ba tare da wani kuskure ba.

Haka kuma tana da wata fitila a bayanta domin amfani da daddare, sannan abubuwan nata gaba daya ba sa jan caji sosai, domin za ta iya kaiwa tsawon watanni idan ana cajinta daga lokaci zuwa lokaci ta hanyar USB.

Muna ganin na'urar BeeLine wadda kamfanin Map da ke Landan, ya kirkiro, wadda za a rika sayar da ita a kan fan 60 ko dala 90, za ta zama jagora ta sosai ga mai keken da bai san hanyar zuwa wani wuri ba a wani sabon birni da ya je, idan dai har ya san kalmar hanyar da ba ta bullewa a yaren garin.

Idan akwai gadojin da za a tsallaka, da tafkunan da za a kauce wa ko wasu wurare da ya zama dole a kiyaye da su, na'urar za ta ba ka damar tsara mata hanyar da kake son ka bi a tafiyar taka.

Masanan da suka kirkiro na'urar BeeLine sun yi hangen nesa domin sun tsara ta yadda za a iya sabunta manhajar aikinta yadda za ta karbi duk wani sabon abu da aka kirkiro wanda ya danganci aikinta.

Hakkin mallakar hoto beeline

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. BeeLine bike nav points urban riders in the right direction