Ya kamata mu ji tsoron mota mai tuka kanta?

Hakkin mallakar hoto AP

Idan akwai abubuwan da fina-finan kirkirarrun labaran kimiyya suka koyar da mu, hadarin da ke tattare da amfani da na'urori masu sarrafa kansu na daya daga cikisu. Saboda wannan ma guji mota marar direba?

Ga nazarin Christian Blauvelt

An san cewa an kirkiro kwamfutoci ne domin mu samu saukin rayuwa, amma kuma duk wanda ya dan dauki lokaci misali sa'o'i da masu kawo dauki ga mutanen da wata kwamfuta ko na'urarsu ta gamu da matsala, ya san cewa ba haka abin yake ba a ko da yaushe.

Amma kuma duk da haka muna wani zamani ne na rayuwa a cikin fasaha kuma wannan zamani ne da ba zai sauya ba a nan kusa.

A wannan watan ne hukumar kiyaye hadura ta Amurka (US National Highway Traffic Safety Administration), ta sheda wa kamfanin Google cewa na'urar fasaharsa da ke sarrafa mota maras direba ta kai matsayin da za a iya daukarta kamar direba, matsayin da ake ba wa mutane kawai.

Ko da ya ke wannan ba shi ne shinge na karshe ba da motar mai tuka kanta za ta fuskanta kafin ta shiga kasuwar motoci a fara ganinta a titi kamar sauran motoci, amma dai wata babbar nasara ce ta kaiwa ga matsayin.

Hakkin mallakar hoto REUTERS

Babu tantama ba tababa motar Google tana da kyau kuma abar sha'awa ce, za a iya ma ce wa san-kowa-kin-wanda ya rasa ce, da siffar da aka yi wa gabanta na alamun fuskar mutumin da yake cike da mamaki, kan wani abu da ya gani wanda ya burge shi matuka. Tabbas da gani babu tambaya ka san cewa da niyya aka yi hakan.

Ba yadda za ka kawo tunanin wani abu maras kyau ko na mugunta idan ka zuba wa wannan farar 'yar kumbular mota ido.

Amma kuma duk da haka a kwanan nan ana ta zazzafar muhawara a kan amfani da kuma illar na'urori ko kwamfuta da ake kyale su, su rika yin abubuwa na basira daga fasaha ko tunanin da aka sanya musu kamar mutum.

A farkon watan nan lokacin da darektan tattara bayanan sirri na Amurka, James Clapper, yake jawabi ga 'yan kwamitin musamman na kula da bayanan sirri na majalisar dokokin kasar ya ce, ''illar fadada amfani da wannan fasaha (wadda ake kira 'AI' Artificilal Intelligence, da Ingilishi), ta hada da karin samun hare-hare kan cibiyoyin internet da wuyar tabbatar da dalilin da ya sa aka yi abu da yuwuwar hukumomin tsaro su rika satar bayanan jama'a daga na'urorin da ke amfani da intanet kamar talabijin da waya da ma firji da sauransu, da yuwuwar aukuwar hadari da makamantansu da kuma haifar da rashin aikin yi.''

Ka duba fasahar Skynet. A Burtaniya, reshen kamfanin Google na kasar ya samar da wani shiri na amfani da na'urori masu amfani da fasaha da kansu (AI), wanda aka tsara domin yin wasan wata dara (dabarar yaki) mai sarkakiya ta tun shekaru 2500 ta mutanen China wadda ake kira 'Go'.

Kuma abin mamaki na'urorin suka kasa wasu kwararrun duniya na wannan wasan dara har sau biyar ba tare da sun yi nasara a kan na'urorin ba ko da sau daya.

Za mu jarraba yin wasa ne? Abin da muke son yi da fasahar, misali mota maras direba a kan titi daya ne da wasa?

To bari mu yi amfani da wannan damar mu gabatar da irin matakan kiyaye tsautsayi ko kuskuren wannan fasaha ta 'AI'.

Ka tuna da na'urar HAL 9000 wadda aka fara amfani da ita wajen sarrafa kumbon zuwa sararin samaniya maras matuki mai suna Discovery One. To idan ka tuna ka duba yadda fasahar ta zama.

Hakkin mallakar hoto Scott Park

Kada ka rena yadda abubuwan da ke sarrafa na'urar HAL suka cika daki daya kawai, wannan na'ura ce da za ta iya sarrafa jirgin sama jannati gaba dayansa da ma'aikatan da ke cikinsa.

Wa zai bukaci wani abu wai shi iTunes, idan har HAL zai iya kawo maka dukkanin wakoki na asali na Amurka? Kuma ga shi fasaharsa ta iya nazarin motsin leban mutum ya san abin da mutum ya furta ko ya fada babu kamarta. Sannan ga shi ba kada wata fargaba game da kare bayanan sirrinka na intanet.

Na'ura ko fasahar HAL ta damu da batun kare sirrinka ta kuma kammala aikin da aka sa ta ta yi, ta yadda idan ka kalubalance ta za ta yanke igiyar da ka daure kanka da ita a jikin kumbon sama jannatin (don kada ka bata daga wurin jirgin) ta bar ka kana yawo kamar takarda a sararin samaniya.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Should we be afraid of the driverless car?