Kasar da ake biyan kudin koyon mota da jima'i

Hakkin mallakar hoto Bare feet

Wata al'ada ta ban-gishiri-in-ba-ka-manda, na jawo cece-kuce a kasar Holland, inda wadanda ba su iya mota ba suke biyan wanda zai koya musu tukin da jima'i maimakon kudi.

David K Gibson ya bincika mana lamarin.

A kasar ta Holland an amince da cinikin ban-gishiri-in-ba-ka-manda da jima'i, ko kuma idan ma ba wata doka da ta amince da tsarin karara, akalla an lamunta da shi, tun daga zamanin karni na biyar zuwa na 15 har zuwa yau.

Muna mamaki kan yadda ake cece-kuce kan wannan tsari, mai suna ''rides for rides'' (da Ingilishi), wanda ake biyan kudin koyar da tukin mota da jima'i maimakon kudi.

Duk da cewa ana ganin doka ta amince da tsarin amma kuma 'yan majalisar kasar ta Netherlands ba su fito fili sun ayyana shi a matsayin wanda bai dace ba.

Maganar doka a kan tsarin ta taso ne yayin da wata sabuwar akidar ra'ayin rikau ke bazuwa a kasar wadda ke da sassaucin dokoki, abin da ya kai ga kawar da wuraren da karuwai ke sheke ayarsu da kuma tsaurara dokoki a kan amfani da kwayoyin da ke sa nishadi da wasu kananan ababan hawa na zamani wadanda galibi masu yawan bude idanu ke iya kurdawa cikin cunkoso da su.

Duk da cewa bisa tsarin al'adar an yarda a yi amfani da jima'i domin biyan wani abu da ka saya ko aka yi maka, amma tsarin bai yarda ka sayar da jima'in ba.

Ma'ana za ka ko za ki iya biyan kudin koya miki tuki da jima'i, amma kuma ba za ki iya ba mutum damar bayan jima'i da ke ba ta hanyar cewa zai koya muki tuki ba.

Karin bayani shi ne, wanda ke son yin jima'in ba zai samu matar da ba ta iya mota ba, ya ce mata yana son ya yi jima'i da ita amma kuma ba kudi zai ba ta ba sai dai ya koya mata mota.

Koyon tukin mota a kasashen Turai abu ne mai tsarabe-tsarabe da kuma tsada idan aka kawtanta da sauran kasashen duniya.

Da yawa daga cikin manyan makarantun Amurka suna ba da darasin koyon mota ne ga dalibansu daga masu koyar da wasu wasan kwallon jifa (baseball) a matsayin ka'idar cikakkiyar manahajar karatunsu, a kasashen Turai koyon tukin mota abu ne da ya shafi mutum shi kansa ba ruwan hukuma.

Zai kuma iya kasancewa abu mai tsada, domin wadanda ke son koyon galibi ba su kai munzalin yin wani aiki na samun albashi mai yawa ba, kuma ga shi akan caji mutum kudin koyar da tukin kusan yuro daya (naira 430) a duk minti daya, wanda hakan bai kai farashin jima'i ba, ko da ya ke ana ganin lokacin koyon tuki ya fi tsawo.

To idan dan kasar ta Holland ko kuma 'yar kasar wadda take son koyon tukin motar 'yar shekara 18 ce, akwai wasu hanyoyin da doka ta amince da su da za ta biya kudin koyon.

Akwai bayani da doka karara a nan, kuma dabarar a fannin yarjejeniyar take. Ga yadda dokar take. An yarda ka bayar da jima'i a matsayin abin biya, amma kuma ba a yarda da gabatar da jima'in a matsayin abin sayarwa ba.

A takaice za ka ko za ki iya biyan kudin koya miki tukin mota da jima'i (maimakon kudi), amma kuma (matar) ba za ta yarda ka zo ka ce kana son ka yi jima'i da ita ba amma da ba kudi za ka ba ta ba sai dai ka koya mata mota, in har tana son yin hakan to sai ta yi rijista a matsayin mai sana'ar karuwanci (sex worker), to amma kuma ga shi ba wannan lasisin take nema ba, na tuki take so.

Akwai abubuwa da dama da ke tattare da tsarin domin ganin ba a ci da gumin wani bangare ba a tsakanin mai son koyon da mai koyarwar, ba don bambancin jinsinsu ba kadai da kuma shekarunsu ba.

'Yan sandan Rotterdam sun gudanar da bincike kan irin wadannan shafukan intanet masu gudanar da harkokin kasuwanci, wadanda suke irin wadannan hada-hada, ko da ya ke ba su fitar da sakamakon rahoton ba ga jama'a.

Idan kana son karanta wannnan a harshen Ingilishi latsa nan. Trading sex for driving lessons