Ana yaƙin cutar Zika da tsoffin tayoyi

Hakkin mallakar hoto Roger Eritja

A ƙasar Canada an ƙirƙiro wani tarko da ake yi da tsohuwar taya, mai matuƙar tasiri wajen yaƙi da sauron da ke yaɗa ƙwayar cutar Zika, wadda ke sa haihuwar gilu (yara masu karamin kai).

Ga bayanin Ken Wysocky

A wani mataki wanda zai yi matukar tasiri mai amfani ga kasashen da ke yankin da ke da zafi na duniya, masu bincike a kasar Canada, sun kirkiro wata hanyar yaki da sauro, mai tasiri da sauki wadda kuma ba ta yada guba, da tsoffin tayoyi.

Dakta Gerardo Ulibarri na jami'ar Laurentia a Sudbury da ke Ontario, ya ce, ''mun juya makamin da sauro yake amfani da shi a kanmu, a kan shi sauron, makamin shi ne tsohuwar taya.

Malamin ya kirkiro tarkon ne wanda ya sanya wa suna ovillanta, (ma'ana tayar yin kwai da harshen Spaniyanci ), domin hallaka kwayayen da sauron da ke yada kwayar cutar Zika da zazzabi da sauran cutuka yake yi.

Hakkin mallakar hoto Daniel Pinelo
Image caption Tarkon sauro na Ovillanto

Tarkon na ovillanta, yana taimaka wa sosai wajen yaki da wadannan cutuka, wadanda suke kama miliyoyin mutane a Afrika a duk shekara, musamman ma mutanen kasashe masu zafi, lamarin da yake jawo mutuwar dubban mutane, kamar yadda bayanan hukumar lafiya ta duniya suka nuna.

Shi dai wannan tarko yana kawar da bukatar amfani da magungunan kwari, wadanda za su iya yin illa ga muhalli da cutar da wasu kwarin ciki har da wadanda ke cinye sauron kansa.

Bugu da kari dogaro ga maganin kwari abu ne da zai iya sa a gaba a samu nau'in sauron da ke iya bijirewa magani, in ji Ulibarri.

Sannan wannan hanya ta maganin sauro, ta bullo da wata hanya ko da yake karama ce, ta sarrafa wata shara da ke da wuyar kawarwa a duniya- tsohuwar taya.

Tarkon ba shi da tsada ga saukin yi, kuma kayan yinsa kusan ba za su kare ba, domin an yi kiyasin ana samun tsoffin tayoyi biliyan daya da miliyan 500 a duk shekara a fadin duniya.

Ulibarri ya kirkiro wani tarkon da zai taimaka wajen yaki da kwayoyin cutar 'west Nile a Ontario a shekara ta 2012, amma sai aka ga zai yi tsada sosai da kuma wuya a iya kai shi kasashe masu tasowa.

Ya ce, ''saboda haka ne na fara neman abubuwa masu sauki da za a yi da su, daga nan ne na gano tayoyi, saboda kusan kashi 30 cikin dari na sauron da ke yada cutuka yana yin kwai ne a cikin tayoyin da aka ajiye ruwa ya taru a cikinsu.''

Ya kara bayani da cewa, ''ba haka muka tsara ba dace ne kawai muka yi, tunanin hakan ya zo mana.''

Masu bincike sun gano cewa irin wannan tarko 84 da aka sanya a wasu unguwanni bakwai a garin Sayaxche na Guatemala, ya lalata kwayayen da sauro ya yi sama da 18,000 a wata daya. Wannan kusan ninki bakwai na abin da tarko na sosai zai yi kenan.

Shidai wannan tarko, ovillanta, wanda ake yi da robar taya da aka yanka tsawon kusan inci 20 (kamar shan wata) da wata kofa a kasa, wadda za a iya tsiyaye ruwa ta wurinta, tsari ne na irin wurin da sauron yake yada kwayayensa.

Za a iya yin tarko uku da taya daya. Ga yadda ake aiki da shi: Ana zuba ruwa ne na kusan lita biyu ko rabin galan a cikin yankakkiyar tayar, sannan kuma a sa wata takarda a gefe da gefen tayar ta shiga cikin ruwan, inda matar sauron za ta yi kwai a kai.

Image caption Sauron da ke yada kwayar cutar Zika

Ulibarri ya ce, ''Sauro ba ya yin kwai a kan wuri ko abin da yake busasshe, sai a kan abin da yake da danshi. Saboda haka idan a yanayi na zafi ne, sai kana yi kana kara ruwa a cikin tayar daga lokaci zuwa lokaci, saboda zafin rana yana sa ruwan ya ragu da sauri.''

Masanin ya ce, ''dole ne a rika tsiyaye ruwan sau biyu a sati,(ta wannan kofa da aka yi a kasan tayar), inda zai rika shiga wani gwangwani da za a sa masa rariya (wani farin kyalle a bakinsa). Ana rariyar da farin kyalle ne domin za a fi ganin kwayayen a kan farin kyalle.''

Bayan ruwan ya gama zuba cikin gwangwanin, sai a dauki rariyar wato wannan kyallen inda kwayayen suke a bata su, sai kuma a mayar da ruwan cikin tayar, sannan a sa wasu fararen takardun kamar da ta cikin ruwan inda sauron ke zuba kwan.

Yana da kyau ka sake mayar da wannan ruwan wanda ka yi amfani da shi, domin akwai sinadarin da sauron ya zuba a ciki wanda duk wani sauro da ya zo wurin zai ji wari ko kanshin sinadarin da zai san cewa wuri ne da ya dace ya yi kwai, in ji Ulibarri.

Masanin ya ce, ''Fahimtar abokin gaba ita ce hanyar da ta fi dacewa wurin yaki da shi.''

Galibi ya kan dauki kamar wata daya, kafin a fara ganin tasirin wannan tarko wajen rage yawan sauron da ke wuri, saboda wata daya ne tsawon rayuwar tamatar sauro a yanayi na zafi. Kuma idan aka sa tarkon da yawa a wuri zai fi yin tasiri sosai.

Malamin jami'ar ya ce, yana ganin tarkon zai taimaka sosai wajen rage cutuka da dama da sauro ke yadawa, kuma ya kara da cewa idan aka jarraba wani tarkon kuma yana ganin a nan ma za a iya yaki da sauron da ke yada cutar maleriya.

Akwai kuma wata dabarar ta yaki da sauron da ke yada kwayoyin cutuka bayan, wannan ta amfani da tsoffin tayoyi. Akwai wata hanyar ta amfani da salansar babur ( MotoRepellant), wadda aka bullo da ita a Asia wajen kashe sauro.

Ana makala 'yar wata na'ura ne a jikin salansar babur, wadda zafin salansar yake sa wani mai da ke cikin 'yar na'urar ya rika fitar da wani wari ko kanshi wanda sauro ba ya so. Abin yana aiki a tsakanin nisan kafa goma daga inda babur din yake.

Wannan dabara ta amfani da babur wadda ake yi a Thailand tana maganin sauron da ke yada wani nau'in zazzabi (dengue), wanda hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta yi kiyasin yana kama mutane miliyan 390 a duniya, sannan yana hallaka mutane 25,000.

Hukumar ta ce sama mutane biliyan biyu da miliyan 500, wato kashi daya bisa uku na mutanen duniya na fuskantar hadarin kamuwa da cutar.

Ulibarri ya ce, ''Idan za mu hada kai mu yi aiki tare, watakila za mu iya kawo sauyi.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Battling the Zika virus, one old tyre at a time