Aiki mafi kyau na masu basira amma malalata

A wannan duniya da ake fama da wahalar aiki ko za a iya cewa hanyar da ta fi dacewa ita ce samun aiki maras wahala kuma wanda aka fi samun kudi?

Ko zabin aikin da mutum zai yi a nan gaba zai kasance aikin da ba takura sosai? To wai ma menene illar a ce mutum ya nemi aikin da ba shi da matsi sosai?

Mun duba shafin tambaya da amsa na Quora domin samun shawara akan ayyukan da suka fi dacewa ga mutane masu basira amma kuma malalata. Ga abin da mutane suka ce:

Ga abin da Andy Lee Chaisiri, mai zayyana wasan kwamfuta ya rubuta: ''Watakila kusan duk malamin harshen turanci daya a cikin uku da na hadu da shi a Beijing yana bayyana kansa a matsayin mai basira amma kuma malalaci.''

Ya rubuta cewa aikin koyarwa a China yawanci yana da samu sosai amma kuma yana da takurawa. Ba a tsanantawa ko takaitata sharudan daukar mutum aikin.

A wasu lokutan abin kawai da ake bukata da mutum shi ne ya zamanto an haife shi ne a kasar da ake yin turanci.

Chaisiri ya bayyana cewa, saboda shi aikin koyar da turanci ba a tsayar da lokacinsa ba wuri daya, an rarraba shi, mutane da dama suna yin sa a matsayin aikin wucin-gadi.

Suna yinsa ne kawai na wani dan lokaci ko kuma kafin su samu wani aikin. Wanda hakan ke nufin idan ka dauki aikin koyar da turanci a matsayin aikinka na dindindin za ka rika samun cigaba.

Kuma ya kara da cewa,''yawan albashinka zai kai daidai da matsakaitan ma'aikata da suka kammala kwaleji da suke aikin sa'oi 50 a sati kuma har ma su kara da aikin bayan lokaci har karshen rayuwarsu.

Shi ne Chaisiri ya rubuta: ''To ku malalata sai ku je ku yi ta koyar da Turanci!''

Idan ba ka son ka yi nisa da ofishin gidanka, Paul Denlinger ya ba ka wannan shawarar: '' Ka zama mai shirye-shiryen kwamfuta: Aiki ne da ake ci gaba da koyo, amma kuma ba ka bukatar ka yi wani aiki mai wahala, kuma sannu

a hankali za ka fahimci cewa da yawa daga cikin wahalhalun da ke tattare da ikin maimaci ne kawai.

Hatta yanayin aikin ma ya nuna ba wani aiki mai yawa za ka yi ba kamar yadda ya nuna. ''Kwararrun masu shirye-shiryen kwamfuta dan rubutu kadan kawai suke yi na sirrin wasu lambobi da harufa na bude wani abu ko shiga

wani shafi, amma kuma suna samun kudi sosai, duk da lalacin da ikin yake sa wa.'' Kamar yadda Denlinger ya rubuta.

Ya kara da cewa,'' kuma duka wanna fa kana iki ne tare da wasu mutanen masu basira, shi kuma mai kamfanin yana ta turo maka kudi domin ka kirkiro wata fasahar kuma.''

To amma kuma, Chris Leong wani mai shirye-shiryen kwamfutar a Sydney yana ganin, ''aikin gwamnati shi ya fi, domin yawancin ayyukan gwamnati ana sa'oi 35 a mako a kasar Australiya, sai dai idan ka kai babban matsayi.''

Shi kuwa Mathew Kuzma ga abin da ya rubuta: ''Shawarata ita ce aikin da ya fi dacewa da wanda yake mai basira amma kuma malalaci, shi ne ya zama kwararre a wani abu, inda mutane da za su yi aikin da ke da wahalar za su

rika tuntubarsa kuma ana biyansa akan hakan.''

Ya shawarci wadanda ba sa aikin komaida, ''su duba wasu ayyuka da suke ganin ba wasu ayyuka ba ne masu wahala, su kware a kai, su zamar musu sana'a. Akwai yuwuwar cewa aikin da ka dauka ba mai wahala ba ne, a wurin wahi aiki ne mai wuya da zai biya ka ka yi masa.''

Ko da yaushe akwai dama:
Hakkin mallakar hoto AFP

Kamar yadda ake gani, sake dauko wani tsari ko shiri da aka yi watsi da shi a baya, a yi amfani da shi wajen shawo kan wata matsala, ba abu ne da za a ce ba shi da kyau. Arvind Krishnan ya ruwaito hamshakin attajiri Bill Gates

yana cewa,'' a ko da yaushe zan zabi malalaci ya yi min aikin da yake mafi wahala, domin shi zai fi samo hanya mafi sauki ta yin aikin.''

To malalatan mutane amma fa masu basira: ''kamar kuna da dama a Microsoft,'' kamar yadda Krishnan ya rubuta.

Idan kan son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The best jobs for smart, but lazy people