Abubuwan koyo daga bata-gari da miyagu

Hakkin mallakar hoto paramount pictures

Yadda kasurgumin mai hadahadar miyagun kwayoyin nan na kasar Mexico ya tsere daga kurkuku a watan Yuli da farko abin ya zama wani abu da manyan kamfanonin kasuwanci za su koyi wani darasi a ciki.

Amma kuma wasu da ke cikin harkar kasuwancin a duniya sun ga akasin hakan ne.

Bayan abubuwan keta doka wadanda masu aikata miyagun laifuka ke yi, wasu manyan masana kan harkokin kasuwanci sun ce, akwai abubuwan koyo daga manyan kungiyoyin masu

aikata manyan laifukan da masu satar shiga shafuka da runbunan kwamfuta na wasu da masu fashi a teku da sauran masu aikata abubuwan da suka sabawa doka, kan yadda kamfanoni da 'yan kasuwa za su yi gwagwarmaya da fuskantar sauyi na gaggawa.

Wadannan manyan masana a harkar kasuwanci suka ce ba wai maganar halatta ko karfafawa saba doka gwiwa ba ne.

Magana ce ta zahiri, kamar yadda manyan kamfanonin kasuwanci sukan kwaikwayi kanana, shugabannin kamfanoni ka iya koyo daga masu aikata manayan laifuka yadda za a yi sauyi

domin tunkarar wani sabon yanayi na daban da kirkira da kuma yadda za ka sauya cikin hanzari idan yanayi ya juya ta yadda za ka ci gaba zama a gaba ko akalla ka zama ana damawa da kai.

Shugaban cibiyar nazarin laifukan zamani kuma mai bayar da shawara kan laifukan intanet a duniya Marc Goodman, ya ce kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka ba sa barci.

''Kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka suna da kuzari da hanzari wadanda manyan kamfanonin 'yan kasuwa ba su da su.

Yayin da kamfanonin kasuwanci ke mayar da hanakali kan dokokin ya kamata su bi, masu laifi neman yadda za su kewaye wa wadannan dokoki suke.

Kuma su miyagu ba su da wata iyaka kuma wannan shi ke sa su samu damar fadada tunaninsu sosai da sosai.''

Misali shugaban kungiyar hada hadar miyagun kwayoyi ta Mexico Joaquin Guzman, ya sulale ne daga dakin kurkukunsa ta cikin wata 'yar mitsitsiyar kofa a shayarsa ta wanka, wadda ta

bulla zuwa wani ramin karkashin kasa na tsawon mil daya, wanda aka sanya wa hasken lantarki da kofofin samun iska.

Samun nasara a wannan shiri na bukatar basira da shiri na tsawon lokaci da kuma juriya, wanda dukkanin wadannan abubuwa ne da suka zama dole irin wadanda kuma ake bukata kafin a yi nasara a babban kasuwanci.

Yayin da Devin Liddell wanda ke shugabantar sashen tsare-tsare na kamfanin zayyana, Teaguel da ke Seattle a Amurka, ya yi watsi da batun kwaikwayon tashin hankali da sauran

ayyukan saba doka da kungiyoyin bata-gari ke yi, yana kuma mamakin yadda irin wadannan kungiyoyin miyagu ke dorewa.

Wasu manyan kungiyoyin masu aikata laifuka suna dorewa duk da irin kokari da matakan da hukumomin tsaro ke dauka a bangarori biyu na iyakar Amurka(wato Amurka da Mexico) da

kuma miliyoyin dalolin da hukumomin duniya suke kashewa domin kawar da kungiyoyin masu laifin. Liddell yana ganin lalle akwai abin koyi a nan kan juriya.

Dabara daya da ya ware ita ce yadda miyagun suke saurin daukan matakan sauyi idan an toshe hanyar da suke ko an kama hanyar dakile su.

Misali domin kauce wa iyakar da ke tsakanin Amurka da Mexico kungiyar masu hada hadar miyagun kwayoyin ta Sinaloa ta dauki bullo da wata dabara ta daban.

Ta gina katafariyar hanyar karkashin kasa, ta dauki hayar iyalai a matsayin wakilan kan iyaka har ma kuma suka yi amfani da basusa suka kewaye wa katangar da aka gina da fasaha ta zamani sosai.

Sabanin kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka, kamfanonin kasuwanci na halak da yawa suna durkushewa saboda suna jinkiri wajen daukar matakan da suka dace, ta yadda za su tafi da zamani da zarar an samu wani sauyi.

Wani babban misali a nan shi ne, na yadda kamfanin bayar da hayar faya-fayen fim da na wasannin kwamfuta na Blockbuster, wanda bai tafi da yanayin sauyin zamani a kasuwa ba, saboda haka wasu sabbin kananan kamfanoni suka danne shi.

Liddell yana ganin bambancin da ke tsakanin bangarorin biyu shi ne, su kungiyoyin masu laifi galibi suna da dabi'a ne ta yin abubuwa ba da wani kyakkyawan shiri ba a ayyukansu na yau

da kullum yayin da su kuma manyan kamfanoni suna amfani da kirkirar wata hanya da ba irinta a matsaryin matakinsu na cimma wani buri.

Hanyoyin dorewa

Wadanna hanyoyin biyar ka iya tabbatar da dorewarka a matsayin na gaba gaba idan ma ba na farko ba.

Yin abu da jiki: Juriya da karfin hali na taimakawa wurin cigaba

Kutse: Gano inda rauni yake ka yi amfani da damar.

Kwaikwayo: Ka yi amfani da fasahar wani ka gina taka a kai ko da kuwa akwai dokar hakkin mallaka a kanta.

Sauyi: Idan kida ya sauya kai ma sai ka yi sauri ka sauya rawa, wato da zarar wani sabon kalubale ya zo to kayi sauri ka sake tsari ta yadda za ka dore.

Tunzurawa: Ka kalubalanci duk wani tsari da ake bi na al'ada

Asalin inda ka samo wadannan shawarwari: Littafin The Misfit Economy na Alexa Clay da Kyra Maya Phillips

Liddell ya ce, ''wannan kalubale ne na shugabanci. Yadda kamfanoni suke kirkira da tafiyar da kansu alama ce ta yadda shugabanci yake.''

Kananan kasuwanci da ba su da kudi sosai suna amfani da dabarun da suka saba wa al'ada wajen shawo kan wata matsala kuma su gina kasuwancinsu tun daga farko.

Yawanci ana wannan kirkira da dabara ne idan abu ya ci tura kamar rashin kasafin kudi mai karfi.

Masu aikata laifi da sabbin 'yan kasuwa, ''suna kalubalantar hukuma kuma su yi abin da ya sabawa doka wanda ta haka suke hango wasu hanyoyi na daban na cimma manufa, '' In ji Goodman. Ya ce, '' Ko dai su zama Elon Musk(hamshakin dan kasuwa da ke Canada) ko kuma El Chapo (hamshakin mai hadahadar miyagun kwayoyi na Mexico).''

Kuma ma wasu kananan 'yan kasuwar ba sa ma tsoro na su taka wasu dokokin shari'a a kokarin da suke na rikita kasuwa.Kamar yadda wadanda aka yi hadakar kirkiro da kamfanin sayar

da kade-kade ta hanyar turawa mutum kidan da yake so ta intanet na Napster, a misali suna sane suna keta dokokin hakkin mallakar fasaha kan wasu kade kaden ta tsarin kasuwancin

nasu tun da farko, wanda kuma wannan fasaha tasu ta samar da hanyar kirkiro wata hanya ta doka wadda da hukumomi ba su lura da ita ba.

Goodman da sauransu suna ganin tsananta tunani kan gano hanyar magance wata matsala kafin damuwa a kan dokoki ka iya hana manyan kamfanoni fadawa tarkon kamfanoni masu gogayya da su wadanda ba sa bin ka'idojin al'ada.

A littafinsu mai suna Misfit Economy, Alexa Clay da Kyra Maya Phillips sun duba yadda mutum zai iya amfani da wannan dabara ya bunkasa basirarsa ta kirkira da kuma kasuwancinsa.

Marubutun sun yi nazari ba a kan kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka ba kadai kamar 'yan fashin teku na Somalia, har da wasu da suke karya dokoki domin samun mafita ga matsalar

harkokinsu na kasuwanci, kamar mutanen da ke zaune a unguwanni na talakawa a Mumbai ko masu kutse a shafukan intanet inda suka gano wadancan dabaru biyar da muka gabatar a baya da wadannan suke amfani da su.

Clay ya bayar da misali da dan kasuwar nan na Saudiyya Walid Abdul-Wahab.

Shi dai Abdul-Wahab ya rika kai nonon rakumi ne Amurka tun kafin hukumomin Amurkan su amince da hakan, wanda ta hanyar juriya da jajircewa ya samar da wanta babbar hanya ko

kamfani, inda ya fara sayar da madarar ko nonon ta shafukan sada zumunta na intanet.

A yanzu kuma kmafninsa, Desert Farms yana sayar wa da manyan kantuna da jama'a ke sayayya a wurinsu irin su Whole Foods Market.

Wadanda suke zaune a gefe ba su da hanyar samun aikin manyan kamfanoni, hakan ke tilasta su tunanin yadda za su rayu, in ji Clay.

Dole ne su zama masu juriya da karfin hali domin su yi karko a duniyar da ke wajen rayuwar aikin ofis.''

''Idan ka ji mutum na tsoron dare to ba a daure shi ya kunce ba'' kamar yadda Clay ya yi bayani

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Life lessons from villains, crooks and gangsters