Kasuwar zuma ta bude a China

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Lokacin da Peter Molan, wanda yanzu tsohon malami ne kuma masanin kimiyya a New Zealand ya fara bincike a kan zuma sama da shekara 30 da ta wuce, ba sosai mutane suke bukatar wadda ta ke a wani daji da yake da wasu bishiyoyi da ake kira Manuka ba.

''Da zubar da ita ma ake yi,''ya ce. ''Idan ka sha ainahin zumar manuka, za ka ji tana da dandano mai kama baki sosai kuma mutane ba sa son ta.''

A yayin bincikensa ne, Molan ya gano wannan zuma tana dauke da wasu abubuwa na musamman.

Wadan nan abubuwa sun kunshi sinadaran maganin wasu cutuka da wata nau'in zumar a duniya ba ta da su.

Wani bincike ya nuna wadannan sinadarai za su iya maganin ciwuka tare kuma da karfafa garkuwar jikin mutum.

Har yanzu dai ana bincike a kan maganar maganin na zumar, wadda bayan samun labarin irin amfanin da ake cewa tana da shi a wajen kasar ta New Zealand, sai bukatarta ta bude aka shiga harkar samar da ita, ta zama wani kasuwanci na duniya.

Fitattun mutane a duniya kamar zakaran kwallon tennis na duniya Novak Djokavic da 'yar wasan fim Scarlett Johansson na daga wadanda suke tabbatar da ingancinta.

Yanzu kasuwar wannan zuma ta bude sosai a tsakanin attajiran China, inda damuwa da fargba a kan lafiyar kayan abinci ta sa mutane suka karkata ga kayan abinci na waje da ba a sanya masa komai na zamani ba.

Shekarau bakwai kusan babu wani abu da China take sayo wa daga New Zealand amma yanzu ta kamo Hong Kong a matsayin ta biyu a duniya wadda ke siyayya daga kasar kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna.

A shekara ta 2014 ta sayo kusan tan 1,500 na abubuwa daga New Zealand din kuma mafi yawa wannan zuma ce ta manuka.

Idan aka hada sayayyar Hong Kong da China daga New Zealand ta zarta ta Birtaniya sosai, wadda ita ce kasa ta daya da ta fi siyayya daga kasar tsawon shekaru, amma kuma kasuwancinta daga New Zealand din ya ragu tun 2009.

Yanzu dai zumar manuka da New Zealand ta ke fitar wa waje ta karu daga ta dala miliyan 23.7 a 2014 zuwa ta 121.5 a 2015. Kuma ana ganin za ta iya karuwa.

Burin gwamnatin kasar dai yanzu shi ne ta bunkasa kasuwancin zumar ya kai na dala 779 a shekara zuwa 2028, ta yadda kasuwancinta zai zama daya kusan daya da na giyar da take yi.

Ka shiga duk wani babban kantin kasaita na sayar da kaya a Shanghai za ka ga yadda kudin zumar ta manuka yake, inda farashi ya kan kai har dala 279 a kanruba mai cin nauyin gram 500, wanda hakan zai nuna maka cewa sai wanda ya isa ne zai saya.

Yawan bukata da kuma karancin wannan zuma ta manuka shi ya sa take da tsada a duniya, amma dai daman kayan waje sun fi tsada a China musamman ma wadanda aka dauka na jin dadi.

Ba kamar sauran kayan alfarma irin su jakar Vuitton ko hutu a Maldives ba, ba a daukar sayen zumar manuka kamar bannar kudi ko nuna matsayi, in ji James Roy, babban jami'in bincike kan kasuwanci na China a Shanghai.

''Ana daukarta ne kamar ka ce yadda 'yan Koriya suka dauki Jinseng, wanda abu ne da kake amfani da shi kusan kullum domin amfanin lafiyarkam.'' In ji Roy.

Shirley Kwun, wata manaja mai shekaru 29 a Shanghai, ta ce babarta ta da ke Hong Kong ta fara sayen zumar manuka tun shekaru da dama da suka wuce inda take amfani da ita a matsayin sukari a kalacinta (abincin safe).

Yanzu ita ma Kwun ta fara sayen zumar manuka kamar sauran 'yan uwanta lokacin da suka je ziyara New Zealand.

Ta ce. ''Babata ce ta fara sayen wani mai mai magani (flaxseed) a tsakanin kawayenta, ina ganin kamar ita jagaba ce a irin wadannan abubuwa.''

Kamar yadda ake yayin duk wani abu na harkar lafiya da ya bulla a China, da maganar baki kawai kasuwar zumar manuka ta bazu.

Sakamakon yadda ake fama da matsalar jabun abubuwa a China, fitattun kamfanonin da suke samar da zumar sai da suka bullo da wasu dabaru na kasuwanci inda suke kai zumar kantunan da masu yawon bude idanu 'yan China suke yawan zuwa a New Zealand da kuma tallata ta a shafukan sada zumunta na intanet na China.

''Maganar fatar baki ita ce babbar hanyarmu ta yada kasuwarmu,'' in ji Brett Hewlett, babban jami'in kamfanin Comvita wanda ke samar da zumar ta manuka a New Zealand.

Ya ce. ''Jama'ar China suna da shakku da dar-dari a kan hanyoyin tallata kaya da aka saba bi, inda duka wani abu da wani fitatcen mutum zai yaba da shi da sunan tallata shi sai su yi shakku a kansa.

Ba abin da suka fi yarda da shi kamar a ce su ji daga bakin wani aboki ko dan uwa.''

Hakkin mallakar hoto comvita nz ltd
Image caption Masu samar da zumar manuka na fafutukar yadda za su wadatar da masu bukata

Yanzu dai kasuwa ta bude a shafukan yada labarai da sada zumunta na intanet, wajen tallata wannan zuma ta manuka.

Hatta sanannen shafin sada zumuntar nan na WeChat yanzu masu tallarta sun yi fice. Wata ma ta tabbatarwa da masu saye a wurinta cewa zumarta ta ainahi ce saboda tana da 'yar uwa a New Zealnad wadda za ta kawo ta kai tsaye zuwa China, tare da bayar da lambobin da mutum zai bi diddigin tabbatar da hakan.

Matsalar bunkasar kaya.

A baya matsalar samar da jabu ta kawo cikas ga kasuwar zumar manuka, inda har ta kai hukumar tabbatar da ingancin abinci ta Birtaniya a shekaru biyu da suka gabata ta yi gargadi a kan abubuwan karya da ake rubutawa a jikin robobin zumar cewa tana magani.

Babbar kungiyar hada-hadar samar da zuma ta New Zealand ta dauki matakan kare harkar inda ta samar da wani tsari na tabbatar da inagancin zumar domin fadakar da jama'a inganci da kyawun zumar kowace roba.

Kungiyar ta kafa dakunan binciken kimiyya a wurare da dama ciki har da birnin Nanjing na China domin tantance ingancin zumar da aka shigo da ita.

''A ganina wannan yana da muhimmanci sosai mun samar d mtaki na tabbatar da gaskiya,'' in ji John Rawcliffe, shugaban hukumar kula da samar da zumar UMF.

Kamar sanya dan sanda mai kula da ababan hawa ne a titi, za ka ga akwi lokacin da ba ya aikin komai. Kasancewar wuraren binciken kadai wani abu ne mi amfani.''

Bukatar ta China yanzu ta sa sai dole masu samar da zumar sun tashi tsaye domin wadatar da jama'a.

Kuma duk da matakin da kamfanin Comvita ya dauka na rubanya kongo-kongon da yake da su har zuwa 30,000 a shekaru biyu da suka gabata ba su iya cimma bukatar ba.

''A gaskiya ba mu iya cimma bukatar ba sosai,'' in ji Hewlett

Hakkin mallakar hoto comvita nz ltd
Image caption Kudan zuma a kan furen bishiyar manuka

Sauran masu samar da ita suna fadada noman zuwa kauyukan kasar inda sai dai a dauko zumar da jirgi mai saukar ungulu, in ji Molan.

''Abin ya zama kamar tururuwar samun zinare,'' kamar yadda Molan ya kara da cewa.

''Mutane a New Zealand suna sayen kongon zuma su kafa a tsakanin duk gidan da yake da furen manuka da zummar cewa zumar za ta ci furen su samu nau'in zumar ta manuka,''

Abu daya da New Zealand ba za ta yi a fargaba ba a kai shi ne gogayya, domin a Ausralia ce kawai take da dajin bishiyar ta manuka wannan ita ce kadai barazanarta.

Duk da cewa akwai rahotannin da ke nuna cewa China na kokarin samar da nau'in wani sanannen abinci mai kara lafiya na kasar waje (maca root) wanda ake samarwa a Peru, Rawcliffe ba ya ganin China za ta fara samar tata zumar ta manuka, ganin yadda kasarta take.

Rawcliffe ya ce, ''idan za ka iya daukar New Zealand kacokan ka dasa ta a China to sai na damu.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Sweet obsession: China's manuka madness