Matsalar ci-da-zuci

Hakkin mallakar hoto alamy

Idan aka ce lokaci ne na gama makaranta, lokaci ne da matasa da dama za su bar rayuwa ta jami'a a shiga fafutukar neman aiki ko kuma ma a shiga rayuwar aikin mai cike da irin nata kalubalen.

Ban taba gabatar da wani jawabi ba a wurin bikin kammala karatu, amma idan da zan gabatar to da zan yi ne a kan rudani, wanda wani muhimmin abu ne wanda tasirinsa ya kan dauki lokaci kafin ya bayyana.

Wannan ya fi tabbata a zahiri a fannin shugabanci domin a wannan bangare ne idan ka yi watsi da wannan rudani za ka iya samun kanka cikin babbar matsala.

Ka dubi ci-da-zuci. Karfin duk wani shugaba shi ne ya iya nuna wa sauran jama'a cewa ya sana abin da yake faruwa kuma zai iya fuskantarsa.

Ya ce ku bi ni mu hada kai za mu samu nasara a kai.

A nan abin da za ka yi kawai shi ne ka duba sanannun fina-finai , ka ga yadda ci-da-zuci yake zaman wani muhimmin bangare na shugabanci.

James Bond da Indiana Jones da kuma Catwoman ba sa nuna wata alama ta tsoro ko jinkiri wurin aikata wani wani abu, a maimakon hakan ma sai ka gansu da karfin hali da kwarin gwiwa.

Saboda haka idan muka ga shugabanni suna yin irin wannan dabi'a sai mu ce, 'ga wani mai kwazo'.

Idan aka samu matsala ci-da-zuci kan haifar da matsaloli da kura-kurai da rashi zuwa bata lokaci mai yawa wurin kokarin kwarewa a wani tsohon abu maimakon ka mayar da hankalinka kan sabon abu.

Ba wai cewa karfin hali abu ne maras kyau ba. A'a, abu ne mai muhimmanci. To amma yana da kyau ya kasance a shriye kake ka karbi shawarar wanda ka ga tasa ta fi taka wato ka zama mai sassauci.

Kwarin gwiwa fiye da kima na nufin ka fara kasa ganin alamun gargadin cewa ba daidai kake ba.

Ba za ka ga wadannan alamu ba saboda kai ba ka ma san da su, domin ba sa ma gabanka ko ma a ce kai a wurinka babu su ma sam-sam. Maganar cewa za ka iya yin kuskure ma ba ta taso ba.

Kwarin gwiwa zai iya haifar da kyakkyawan sakamako idan aka yi amfani da shi inda kake da kwarewa sosai.

Na saba gani a aikin da nake yi da kamfanoni yadda ake daukar mutum kwararre ne a wani fanni sai a dauka wannan kwarewa tasa za ta yi aiki a wani fannin ma, wanda ba shi da alaka da wancan, mutane sai su dauka hakan zai yi.

A nan sai ka ga shugabar kamfani tana ganin kanta a matsayin kwararriya a fannin fasaha, ka ga farfesa yana ganin shi zai iya tafiyar da jami'a fiye da kwararre a fannin shugabanci zai yi ko kuma ka ga kwararren dan wasan guje-guje da tsalle-tsalle ya yi amfani da karfinsa ya tilasta wa mai horad da su ya kawo wasu 'yan wasan da yake ganin sun fi kwarewa.

Idan ba ka dauka ci-da-zuci (ji da kai) ne kadai abin da ke jawo hakan ba, ka jarraba kishiyarsa wato kankan da kai.

Kwararren shugaba mai kankan da kai ko tawali'u yana neman shawarar sauran mutane kuma ya yi amfani da ita idan ta dace.

Kuma hakan ba yana ba wa sauran mutane dama su nuna kwarewarsu ba kadai, yana sa a samu manufa da tsari mai kyau, domin kamar yadda aka ce 'hannu da yawa maganin kazamir miya'.

To sai dai kuma kamar yadda kwarin gwiwa idan ya yi yawa yake zama ci-da-zuci wanda kuma yake zama illa, haka tawali'u ko kankan da kai idan ya yi yawa shi ma yana haifar da illa.

Amfanin duk wata gasa shi ne nasara, kuma ji da kai ba wani abu ne maras kyau ba can-can.

A wata kasida da kocin kwararren dan wasan kwallon kwando na gasar Amurka ta NBA Stephen Curry ya rubuta a jaridar New York Times kwanan nan, kocin ya bayyana dan wasan a matsayin mai kankan da kai kuma mai jijji da kai.

Za ka iya kasancewa duka biyu kuma lalle wani zai ga cewa akwai bukatar ka zama duka biyun.

Dabarar ita ce komai da lokacinsa, ka duba lokacin da ya dace ka nuna kowacce daga cikin abubuwan da ka kware da su na shugabanci.

Taimaka wa 'yan kungiyarka su ci kwallo abu ne mai kyau, amma kuma idan ka nuna karfi da iyawa ka mamaye wasan ka rika ci da kanka shi ma abu ne mai kyau.

Kwarewa a fanni daya kawai ba dabara ce mai kyau ba a duk wata babbar gasa ta wasa ko ta kasuwanci.

Ko ina mafita kenan? Idan kai shugaba ne ko babban jami'i a wani wuri, ka tabbatar ba ka fada tarkon cewa, 'hannu daya ba ya daukar jinka' ba.

Saboda kawai karfin gwiwa abu ne mai kyau ko kan-kan da kai abu ne mai muhimmanci, hakan ba yana nufin ka rika neman mutanen da suke hakan ba kana kuma saka musu kan yin hakan.

Idan ba ka dade ba a aikinka kuma kana kokarin ka san inda ka sa gaba, ka yi hankali da inda kafi kwarewa.

Wannan shawara tana da muhimmanci ne zuwa wani mataki kawai, wannan mataki shi ne inda hukuma ta hadu da shugabanci.

Ka dage da aiki har ka san iya matsayin tsarin shugabancinka.

Ka yarda cewa kan-kan da kai zai iya jawo maka farin jini da abokan aikinka, amma idan ya kasance bangare daya kawai ka fi bayar da karfi ko kwarewa to zai yi wuya ka iya kaiwa matsayin shugabanci.

Fitattu kuma manyan shugabanni a duniya sun rungumi rudani ba su yarda sun yi watsi da shi ba. Hakan kuma shi ne mafi alfanu ga shugabanni masu tasowa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The trouble with being too confident