Abin da ya sa muke yarda da bayanai na bogi

Hakkin mallakar hoto walt disney co

Me ya sa mutanen da ake gani kamar wayayyu ne wadanda suka san abin da ya kamata suke amfani da bayanai na bogi kamar na gaskiya?

Sydney Finkelstein ta yi nazari.

Kafa wata harkar kasuwanci ko tafiyar da wani kamfani babba abu ne mai wuya ba tare da aikata wani kuskure ba.

To idan haka ne me ya sa a wani lokaci shugabanni suke yarda da duk wasu bayanai da ba na gaskiya ba, ko da kuwa cewa za su cutar da su?

Kuma ma bayanai da aka kitsa na bogi wani fanni ne na harkokin kasuwanci da siyasa a wurare da hukumomi da gwamnatoci da yawa.

Me ya sa mutanen da ake ganin suna da wayewa da kuma kwarewa suke yarda da bayanai na bogi kamar cewa na gaskiya ne?

Misali a wani taro na musamman da aka yi kwanan nan, na masu hannun jari, bukatar da babban jami'in bankin Amurka, Brian Moynihan ya gabatar ta kara masa matsayin shugaba bayan na babban jami'i, ta gamu da suka daga bangaren asusun kudaden fansho da sauran masu zuba jari wadanda suka nuna adawa da hakan.

To amma ga abin mamakin nan: kamfanonin da suke da babban jami'i wanda kuma yake rike da matsayin shugaban huukumar kamfanin babu wani abu da suke yi da suka wuce wadanda suka bambanta matsayin biyu.

Saboda haka me ya sa har ake tayar da jijiyar wuya akan tsarin da gwamnati ke son fitowa da shi wanda ba shi da wani tasiri?

Wannan daya kenan daga cikin hanyoyin da shugaba yake jawo cece-ku-ce ba tare da wani dalili ko bayanai da zai danganta da dalilinsa na yin abin da ya yi ba.

Hanyar kaiwa ga abubuwan bogi

Me ya sa mutanen da ake ganin suna da wayewa da kuma kwarewa suke abu bisa dogaro da bayanai na bogi kamar na gaskiya ne?

Bisa irin wannan dalilin ne 'yan neman takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republikan kusan gaba dayansu suka bayar da shawarar rage yawan haraji domin bunkasa tattalin arziki duk da irin shedun da ake da su a baya na lokacin shugabancin Ronald Reagan da Bill Clinton da George W Bush cewa hakan na kara gibin da ke tsakanin talakawa da attajirai ne kawai, amma ba bunkasa tattalin arziki ba.

Haka kuma a bisa wannan dalilin ne dai 'yan siyasa kamar su Francois Hollande a Faransa da Jeremy Corbyn a Burtaniya da Bernie Sanders a Amurka suka bayar da shawarar gwamnati ta rika taka rawar mai sa ido a harkokin jama'a kawai maimakon gudanar da komai da kanta, duk kuwa da shedar tabarbarewar ayyukan gwamnati a wadan nan kasashe, kamar makarantun gwamnati a Faransa da shirin kula da lafiya na tarayya a Burtaniya da kuma yadda aka tafiyar da yaki a Amurka.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Amsar ita ce akida. Akida ra'ayi ne mai karfi na mai tsattsauran ra'ayi na abin da yake daidai da wanda yake ba daidai ba, ba tare da la'akari da shedar abin da aka gani a zahiri ba, da kuma shedar tunanin akasin hakan.

A harkokin gwamnati kamar na kamfani akida na hana kawo sauyi. Saboda haka sai mu kawai mu rika amfani da bayanai na bogi da muka dauka kamar na gaskiya.

Wadan nan bayanai da ba na gaskiya ba za su iya shafar ayyukan da kamfani yake yi.

Yawancin manyan kamfanonin lauyoyi na duniya suna yi wa mutane aikin lauya ta hanyar dogaro ga sabbin daliban makarantun lauya masu ilimi sosai amma kuma wadanda ba su da kwarewa.

Inda suke karbar kudade masu yawa a hannun mutane su biya wadan nan sabbin lauyoyi 'yan kudade domin samun riba mai yawa.

Ganin cewa yanzu ana kalubalantar wadan nan kamfanonin aikin lauya a kan irin aikin da suke yi wa mutane kusan da za a ce na wadanda ba kwararrun lauyoyi ba, wasu daga cikinsu, suna ta fafutuka, amma duk da haka ba wani sauyi da suka yi kan abin da suke yi na amfani da sabbin lauyoyi.

Al'amura sun sauya, amma ganin cewa wadan nan kamfanonin aikin lauya sun zabi su ci gaba da bin tsohon tsarin da suke bi, hakan ya ci gaba da dorewa.

Abin da zai yi maganin wannan dabi'a ta amfani da bayanai na bogi shi ne yanayin da za a kai ga amfani da rumbun dimbin bayanai da sai kwamfuta ce za ta sarrafa s, ta samar da bayanai da suka danganci dabi'a ko halayyar mutum.

Dukkanmu mun yarda cewa wasu abubuwan da mukan yi sha'awarsu ko tunaninsu abubuwa ne da suke na gaskiya daga lokaci zuwa lokaci.

Sai dai abin takaicin shi ne a fagen gasar kasuwanci, akwai dama ko hanyoyi da yawa da 'yan kasuwa za su iya kalubalantar wannan bayanai na bogi da ka samar kuma kake tafiya a kansu.

Yawancin kamfanoni da suke bin tsari na da haka suke shekara 10 ko 20 da ta wuce, a lokacin da ake samun sauyi a kan fasahohi da dama (misali kamfanin kodak da ke kyamara da motorola a fannin wayar salula).

Haka kuma wannan shi ne dai abin da yake tattare da kamfanoni da dama da suka zuba jarin biliyoyin dala wajen samar da kayayyakin aiki, yayin da sabbin kamfanonin da ke amfani da intanet suke tafiyar da aiki cikin sauki.

Komawa kan gaskiya

Abubuwa ba su baci ba gaba daya. Za mu iya daukar abubuwa na bogi a matsayin yadda suke.

Hatta 'yan hukumar gudanarwar kamfani za su iya magana, wannan wani babban fanni ne na aikinsu.

Jagorori na bukatar mara baya ga mutanen da suke da kwarin gwiwar da za su fito fili su yi magana, amma ba su bata irin wadan nan mutanen masu karfin hali ba.

Hakkin mallakar hoto Getty

Ka tambayi kanka me ya sa kake yin abubuwa yadda kake yi. Watakila akwai dalilin da ya sa kake yin abin ta wannan hanya, to amma me yasa duk da cewa an samu sauyi a tare da kai, ka ci gaba da yin hakan?

Duk da cewa ina irin korafina a kan rumbun bayanai na fasaha na kawo sauyi, a fannin kirkira, amma ba za mu iya musunta karfi ko tasirin rumbun bayanan ba a sauyin da ya ke kawowa a harkar ma'aikata ba da kuma dukkanin fannoni na kasuwanci na zamani.

Wannan ci gaba na samun rumbum bayanai na fasaha na zamani shi ke da karfin kawar da wannan a'ada ta yin amfani da bayanai na bogi wadanda aka gina a kan tsari na gargajiya na amfani da akida.

Gabatar da wani ra'ayi na daban ba wai kawai bayyana matsayinka ba ne, kuma ka da ka rena hanyar bayar da labari (kamar yadda ake tatsuniya) wajen gabatar da sakonka.

Ba na kokonton cewa duk wani mafarki ko fata na shugabanni zai dakushe ya kau, ya zama babu shi, idan aka fiuskance shi da bayanai da gaskiya, ko da kuwa da karfi aka bayyana wa mutane shi. Wannan shi ne abin da muke da shi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why we trust made-up facts