Ko boye jahilci na da kyau?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Me ya sa wadansu mutanen suke samun nasarar boye jahilci da rashin saninsu a tsawon rayuwar aikinsu,amma kuma wasu ba sa yin nasarar hakan?

Idan ba ka da kwarin gwiwa a aikinka, yawanci ana shawartar ka, da ka da ka fito fili ka nuna, ka boye, ka rika nuna kamar ka iya, ko kuma kawai ka rika ji cewa ka iya din.

To amma kowa ne yake iya tsira da hakan kuwa? Yaushe ne ya kamata mutum ya fito fili ya ce bai sani ba?

Ba zan bai wa 'yan sama-jannati da lauyoyi da likitocin zuciya da 'yan wasan kwallon zari ruga da injiniyoyin tashar nukiliya ko dakaru na musamman wannan shawara ba.

Mun mika wannan tambaya ga jama'a domin mu ga ko akwai lokacin da boye rashin sani a wurin aiki ba zai tserad da mutum ba.

''Ba zan shawarci 'yan sama-jannati da lauyoyi da likitocin zuciya da 'yan wasan kwallon zari ruga da injiniyoyin tashar nukiliya ko dakaru na musamman su dauki wannan dabi'a ba,'' Wannan shi ne abin da Franklin Veaux ya rubuto, amma kuma kin nunawar zai iya yi maka aiki idan burinka shi ne ka sauya wata dabi'a taka, kamar kana son ka samu karfin hali ko kwarin gwiwa.

''Ina nufin hakan ba zai yi amfani ba idan kana bukatar ilimi ne na kwararru ko wata kwarewa ko horo na musamman,'' amma Veaux yana ganin boye jahilcin naka ka iya kai ga ga nasara sosai idan kana son samar wa kanka kwarin gwiwa ko karfin hali ko boye halin da kake ciki ne.

Lauya, Jennifer Ellis, ta rubuto ne tana cewa, ya dogara ne ga irin aikin da kake yi. ''A aikina, boye rashin saninka har ka kai ga ka sani wata rana, mummunar shawara ce.''

Ellis ta bayyana cewa shekaru da dama da suka wuce, a lokacin da take aikin sakatariya, ''ban san yadda aikin yake ba.

Ba zan boye jahilcina ba, ban ji kunyar nuna cewa ni sabuwa ce a wannan aiki ba.

Kuma da haka na koya.'' Ta rubuta cewa ita ko alama ba ta taba yarda da wannan dabi'a ba, ta ka boye jahilcinka.

''Ina ganin ba wani abin kunya ba ne, ka fito fili ka nuna ba ka san wani abu ba, amma kuma ka sani cewa ya kamata kai ma kana da karfin halin da za ka nuna wa jama'a da kai kanka cewa za ka iya koyar abin da sauri.''

Sabanin lauya Ellis, Muralidhara Prabhu, wanda injiniya ne, shi yana ganin, wannan dabara ta boye rashin saninka, za ta iya kai mutum ga nasara idan malami ne ko mai bayar da horo.

Ya bayyana kansa a matsayin mutumin da yake da kunyar magana, wanda hatta a tsakanin mutane hudu ko biyar ba ya iya magana.

Amma kuma wata rana sai aka sa shi ya horad da wasu sabbin ma'aikata ( a kamfanin da yake aiki).

Sai ya shirya sosai, ya yi bita a gaban madubi, sanna kuma ya yi gwaji a gaban wasu abokan aikinsa 'yan kadan.

Ya ce, ''komai ya tafi daidai. Ammaa lokacin da na shiga dakin a ranar horon, har yanzu ban manta da abin da ya faru ba. Sabbin ma'aikatan su 60 ne sabanin 25 da aka gaya min da farko.''

Prabhu ya ce, ''karkarwa kawai nake ina zufa'' amma sai na rika yi musu murmushi sosai ina kokartawa ''in nuna karfin hali na bogi.'' Kuma da haka na yi nasara.

Ma'aikatan sun yaba sosai da yadda ya yi musu wannan horo, bayanan da suka bayar daga baya.

Ya ce, ''wannan abu da na yi sau daya kawai ya ba ni kwarin gwiwa sosai, kuma tun daga wannan lokacin na horar da ma'aikata 1,800, inda yawan mutanen da ake turo min ya kan kama daga 10 z0wa 120. To ni kam a ra'ayina zan iya cewa, mutum zai iya boye rashin saninsa har ya iya koya.''

To akwai kuma wani fage da wannan dabi'a take zaman ka'ida ce ma ta aiki, kamar yadda Forrest Murphy ya rubuto, wannan fage kuwa shi ne na ''zama uba ko uwa.''

Ya ce, ''lokacin da kake dan karamin yaro, abu ne mai sauki ka dauka cewa duk manya sun san komai. Amma mu kuwa (iyaye) a zahiri take cewa muna koyo ne kawai yayin da muke tafiya,''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Should you fake it till you make it?