Idan dukkaninmu maganar albashinmu kawai muke yi fa?

Sa ma'aikata zama cikin farin ciki ba wani abu ne mai wahala ba kamar yadda kake tunani, kuma ba wani kudi za ka kashe ba.

Samun gamsuwa kan aikin da mutum yake yi ba abu ne da lalle ya dogara ga albashi ba, abu ne da ya fi dogara ga gaskiya da amana da rashin boye-boye tsakanin ma'aikaci da me ma'aikatar kamar yadda wani rahoto na kamfanin Bloomberg mai harkokin bicike kan kasuwanci da tattalin arziki ya nuna.

Shugabannin wurin aiki da suke bai wa ma'aikatansu bayanai kan albashi, yawanci sukan kawar da jita-jita da mummunar fahimtar da wasu ma'aikata ke yi ta cewa ba a biyansu yadda ya kamata.

Wasu rahotanni biyu na wannan shekara ta 2015 da shafin intanet na PayScale, wanda ke tattara bayanai kan albashi ya hada ya gano cewa kashi 64 cikin dari na ma'aikatan da ake biyansu albashin da yake daidai da aikinsu, suna ganin ba a biyansu yadda ya kamata.

Daga cikin ma'aikatan da ake biya fiye da yadda kasuwa take kuwa, kashi 21 ne cikin dari kawai suka san ana biyansu fiye da kima, kamar yadda rahotannin suka nuna.

Tattaunawa a kan albashi ba abu ne mai dadin yi ba, domin abu ne da zai iya bayyana dalilin da ya sa mutane da yawa ba sa fahimtar yadda kasuwa ke tantance yawan albashin ma'aikaci da kuma sanin mecece ma'anar ''daidai'' ko ''dacewa'' idan ana maganar albashi ko alawus.

Shafin na PayScale ya gano cewa yawan ma'aikatan da suke nuna gamsuwa ya karu sosai daga kashi 40 cikin dari zuwa 82 cikin dari bayan da shugabannin aikinsu suka tattauna da su a fili kan yadda tsarin albashinsu yake.

Kawar da gibin da ake samu sakamakon rashin fahimta kan yadda albashi yake ba wani abu ba ne da zai ci wa kamfani awni kudi.

''Amma yana bukatar kamfani ya koya wa manajoji ko shugabannin kamfanin yadda ba za su kauce wa duk wata tattaunawa da ma'aikata ba game da albashi'', in ji Tim Low, mataimakin shugaban shafin na intanet na PayScale na bangaren talla kamar yadda ya yi wa Bloomberg bayani.

Domin saukaka wannan tattaunawa mai wuya, kamfanoni na bukatar samar da horo ga manajojinsu kan yadda ake yin wannan tattaunawa.

A tattaunawar za su bai wa ma'aikaci cikakken bayani a kan yadda tsarin albashi yake daki-daki da yadda ake lissafawa ko kuma kididdigar bayanan albashin nasu.

PayScale ya yi kiyasin cewa kasa da kashi 50 cikin dari na kamfanoni ne suke bai wa manajojinsu irin wannan horo na wannan tattaunawa da ma'aikata ko kuma bayar da bayanan albashi.

Yadda a yau ake iya samun bayanai kan albashi cikin sauki ta intanet zai fi dacewa ma'aikaci ya kiyasta albashin da ya kamat ya samu.

Domin kaucewa kyashi ko damuwa kan bambancin albashinka da na wani, ka yi kokari ka da ka bayar da fifiko ko mayar da hankali sosai kan kwatanta albashin naku.

Ka mayar da hankali kan irin aikin da kake yi, amma ba a kan abin da ba ka da shi ba.

Kuma duk da cewa ana biyan wasu ma'aikatan fiye da abin da suke ganin ya kamata su samu, PayScale ya ruwaito cewa kashi 83 cikin dari na wadanda suke ganin ba a biyansu yadda ya dace, lalle kam ana ba su albashin da akida kamar yadda kasuwa ta kama bai kai ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan What if we all just talked about our salary?