Dabi'un aiki da za su sa a tsane ka

Hakkin mallakar hoto Alamy

Ofishi ko wurin aikin kowa yana da wani mutum wanda kusan a ce yana da wuyar sha'ani wajen mu'amulla da sauran jama'a.

Yawancinmu muna damuwa da yin wani babban kuskure a wurin aiki, amma ba mu san cewa yawanci halaye ko dabi'u masu sauki ne ke bata mana suna ba.

Wasu mutanen suna gane kuskurensu ta hanya maras dadi, wasu kuma ba sa koyon darasi sam-sam.

Wannan dai batu ne da masana a kan mu'amulla tsakanin ma'aikata ta shafin nan na Linkedln suka yi wa karatun ta-natsu. Ga abin da biyu daga cikinsu suka bayyana.

Dakta David Bradberry, Shugaban TalentSmart

''Duk yadda kake da basira ko matsayin da ka kai a aiki, akwai wasu halaye da za su sauya yadda mutane suke daukarka kuma su bata maka suna har abada,'' kamar yadda Bradberry ya rubuta kenan a kasidarsa kan wasu munanan kura-kurai tara da za ka kauce wa a wurin aiki; 'The 9 Worst Mistakes You Can Ever Make at Work'.

Wadanne kura-kurai ne wadannan? Kuma menene maras kyau a game da su? Daga cikinsu:

''Sukar wanda kake nuna abokinka ne a bayansa. Sukar abokin aiki a bayansa, da sani ko bisa kuskure babban abu ne da ke haddasa rikici a wurin aiki,'' kamar yadda Bradberry ya rubuta.

Daya daga cikin hanyoyin sukar abokan aiki da aka fi yi ita ce ka kai sukar mutum wajen wani na gaba ba tare da ya sani ba, domin magance wata matsala.

Yawanci mutane suna yin hakan ne domin kauce wa rikici, amma kuma ba su san cewa ta hakan suke iya jawo babban rikici ba, da zarar mutumin da abin ya shafa ya ji labari ko ya gane.''

''Gulma. Mutane na bata kansu idan suka sakankance da gulma a kan sauran mutane,'' ya rubuta. ''Tsunduma a gulmar wasu mutane kan wani kuskure ko matsala da suka samu ka iya sa ransu ya baci matuka idan ta tashi. Ka dai kwana da sanin cewa ita gulma na bata maka suna kuma tana sa mutane su tsane ka a ko da yaushe.

''Bayyana cewa ka tsani aikinka. Abin da ba wanda zai so ya ji wani yana korafi a wurin aiki shi ne kuka game da aiki, wato mutum ya rika magana kan yadda ya tsani aikin da yake yi.

Yin hakan na sa a dauke maras son cigaba kuma yana karya wa sauran ma'aikatan gwiwa,'' yadda Bradberry ya rubuta. ''Shugabanni a wurin aiki na saurin kama irin wadannan mutane, masu karya wa abokan aiki gwiwa, kuma sun san cewa akwai wadanda suke neman wannan aikin da za su maye gurbinsu.''

''Cin abinci mai wari. Sai dai idan a jirgin ruwa kake aiki kawai, amma in har za ka ci abincin da zai tayar da hankalin abokan aikinka saboda warinsa, to wannan abu ne da bai dace ba. Ka'idar ita ce duk abincin da ka san warinsa zai wuce dakin cin abincinku na wurin aiki, kamata ya yi ka bar shi a gida kawai,'' Bradberry ya bayar da shawarar hakan.

''Yin karya. Karerayi da yawa suna farawa ne da niyya mai kyau, inda mutane ke son kare kansu ko wani, to amma karya tana iya girma ta bazu har a gano ta. Kuma da zarar kowa ya san ka yi karya ba ta yadda za ka wanke kanka,'' (Mutunci aka ce madara ne, idan ya zube ba a iya kwashe shi gaba daya). Kamar yadda Bradberry ya rubuta.

Ga shawarwarin da Clinton Buelter, mai masana'antu kuma wanda ya kafa HardToFill.com

Idan mun yi sa'a koyon darasi daga kura-kuranmu yakan iya zuwa mana da sauki. Sai dai a yawancin lokaci irin wannan darasi na da ciwo.Mai daukar ma'aikata kuma mai masana'antu Buelter ya rubuta cewa, ya ''yi kura-kurai masu yawa a matsayinsa na mai daukar ma'aikata'' abinda ya dauke shekaru kafin ganowa da kuma gyara.

A kan haka ne ya gabatar da muhimman darussan da ya koya guda 12 a aikin nasa, (12 Things I Leearned The Hard Way), wadanda suka hada da:

''Ka fara tattauna magana da mutane. Ka daina bata kashi 80 cikin dari na lokacinka kan damuwa cewa wani zai yaudare ka. Ka da ka zama mai shakku da dari-dari,'' ya rubuta.

Abu ne mai muhimmanci ka kasance mai sauraron wasu kowane irin aiki ka ke. ''Ka gane wanda kake son ka taimaka da za ka kulla alaka da shi. Ka kasance mutumin da zai iya samun damar gani a ko da yaushe.''

''Ka yi amfani da hanya mai sauki. Bayan kammala babbar makaranta, mukan so mu rika nuna kanmu ta hanyar rubutu na kakale. Wannan abin da ake tsammanin a gani a harkar aiki daga wurinmu, ko?,'' kamar yadda Buelter ya rubuta.

To ga shawararsa. '' Manta da wannan kakale. Ajiye wannan tsari kada ka yi amfani da shi a tattaunawarka da wasikunka na email da kuma rayuwarka ta yau da kullum.

Idan kana rubuta wa wani abokinka ko wani dan uwanka sakon kar-ta-kawana ta waya ba ka rubutu kamar yadda za ka yi na harkar aiki ko? A'a. Ka yi amfani da rubutun da ka saba na mu'amulla na sauran jama'a gama gari a sakonka, kuma da haka za su maido maka da amsa. Wannan ita ce hanyar da mutane suke amfani da ita.''

''Ka tashi daga teburinka. Abu ne mai sauki ka gaji tare da yin fushi a wurin aiki. Kana zaune ne kawai kana bata lokaci ba ka san ainahin abin da ke faruwa ba a duk minti,'' ya rubuta. K tsara lokacin da za ka tsaya da aiki. Sai ka tashi ka bar teburinka. Ka da ka je ka bata lokacinka a wani wuri. Maimakon haka ka mayar da hankalinka kan wannan lokaci ka yi amfani da shi sosai.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Work habits that make people hate you