Hatsabiban attajirai

Hakkin mallakar hoto airwolfhound flickr cc by sa 2.0

Yayin da matukin karamin jirgin saman dan kasar Rasha ya silalo jirgin, hanci ya doshi kasa, sannan ya yi juyin waina da shi, 'yar tazara tsakaninsa da kasa, Yanik Silver yana zaune ne a cikin jirgin kawai ba abin da yake yi sai murmushi.

''Na ji na'urar jirgin da ke tantance nisansa da kasa, mai aiki da kanta tana gargadin cewa 'hadari hadari jirgin ya yi kasa sosai' kuma hakan ba karamin abin ban sha'awa ba ne.'' in ji Silver, mai sheakara 42, wanda attajiri ne da ya yi kaura daga Rasha zuwa Amurka tun yana yaro.

Tunanin yin irin wannan hatsabibanci kadai ya isa ya sa yawancin mutane su tsorata, shi kuwa Silver ba karamin dadi yake ji ba.

Hakkin mallakar hoto Yanik Silver

Idan ba yana kan sayar da kayayyaki ta intanet ba da kuma tafiyar da shafin mu'amulla tsakanin 'yan kasuwa na intanet mai suna Maverick 1000, ba abin da za ka samu Silver yana yi sai wani hatsabibanci na kasada da rai.

Ko na alkafura mai juyi uku daga wani dogon wuri ko wasan durowa daga wani wuri mai tsawo sanye da irin kayan nan na masu saukar lema.

Yana ma da tikitin tafiya zuwa duniyar samaniya ta farko da kamfanin jirgin Virgin Galactic ya shirya wadda aka biya dala dubu 250, wadda kuma sai nan da shekaru za a yi ta.

A wurin hamshakan attajirai irin su Silver, wadanda suke zuba jari a harkokin nishadi bayan harkokin kasuwancinsu na yau da kullum, kasada wata hanyar rayuwa ce.

Wannan sha'awa ta hatsabibanci tana jininsu ne, kamar yadda masana tunanin dan adam suka bayyana, kuma ba wai wani buri ba ne na yin hakan ko debe kewa suke sa su hakan ba, ko da yake su ma suna taka rawa.

Hatsabibanci a zuci:

Masanin kimiyyar tunanin dan adam Ken Carter ya ce mutane irin su Silver suna da wannan dabi'a ta sha'awar kasada da hatsabibanci ne a jikinsu, saboda suna jin dadin hakan a jikinsu.

Masani kan sha'awar neman jin dadi a jiki, Dakta Carter, wanda farfesa ne kan tunanin dan adam a jami'ar Emory da ke Atalanta a Georgia ya duba yadda jiki yake martani ga gajiya.

Da yake amfani da wani tsari da ya samo asali daga shekarun 1960 domin bayyana dalilin da wasu mutane suke amfani da wasu hanyoyi daban-daban wasu wasu masu sarkakiya da kuma masu tsanani yayin da wasu kuma ba sa yin hakan, Dakta Carter ya ce mutanen da suke da sha'awar hatsabibanci sosai jikinsu ba ya samar da kwayoyin halitta da ke sa damuwa (cortisol) a maimakon shi, sai dai ya samar da kwayoyin halitta masu sa mutum jin dadi da nishadi (dopamine) a lokacin da suka yi tsayuwar kasada a gefen misali wani tsauni ko dutse mai tsawo (wanda idan mutum ya fado da wuya ya rayu).

Mu kuwa da muke daukar tsalle a fito daga jirgin sama a lokacin da yake shawagi kamar wata kasada ce mai hadarin gaske jikinmu yana samar da kwayoyin halitta ne masu sa mutum jin tsoro maimakon masu sa jin dadi, ya bayyana.

''Ka ji ana cewa 'ka yi aiki sosai, kuma ka yi wasa sosai'. Haka abin yake a wurin wasu mutanen,'' ya ce.''kamar abin nan ne da ake cewa mutum ba ya taba wadata, to haka su ma suke, a ko da yaushe suna son cimma wani babban abu a rayuwa.''

Hakkin mallakar hoto Max Cisotti

Yawan samun rashin nishadi wani dalili ne. Yawanci wadanda suke da son irin wannan nishadi sosai suna rayuwa ne cikin matukar sha'awar nishadi da jin dadi.

Wannan watakila shi zai bayyana dalilin da ya sa 'yar kasar New Zealand, Natalie Sisson mai shekara 38 ta ke gararamba daga wannan kasa zuwa waccan kasa.

Yayin da ita kuma ba ta sha'awar sulu cikin iska ko durowa daga sama kamar yadda Silver ya ke matukar so, ita dai tana son tattaki ne zuwa wurare masu nisa da kuma bulaguro sosai.

Ya zuwa yanzu ta yi nasarar kawar da bajintar duniya da aka yi ta tsere a jirgin ruwa a mashigar ruwan Ingila, kuma ta yi tafiya a keke tsawon kilomita 19,000 daga Nairobi zuwa Cape Town.

Ta ce wadannan kalubale su suke karfafa mata gwiwa ka kara kwazo a matsayinta na shugabar wani kamfani na bayar da horo kan harkokin kasuwanci da kuma harkokin ilimi ta intanet, mai suna Suitcase Entrepreneur.

''Za ka iya tunkarar rayuwa rabi da rabi ko kuma ka tunkare ta gaba daya,'' in ji Sisson. ''A duk lokacin da na tura kaina, sai na kara kwarewa a fagen,''

Abubuwa masu tsada:

Wannan hatsabibanci ba na maras tsoro ba ne kawai, abu ne na masu kudi. Misali Sisson ta ce tattakin da ta yi a keke a Afrika ta kashe dala dubu bakwai da 700, kuma wasu kamfanonin su kan karbar kusan dala dubu 18 da 400 a kan shawagin minti 45 a jirgin sama mai gudun tsiya.

Hakkin mallakar hoto Jordan SiemensGetty Images

Dakta Carter ya ce yadda suke wannan kasada kusan daya ne da yadda suke harkokin kasuwancinsu, inda za ka ga suna da sha'awar kasadar zuba makudan kudade a harkokin da za su samu riba sosai.

''Idan kana da kudi sai komai naka ya karu, kuma idan hatsabibanci dabi'arka ce, to za ka zuba kudi sosai a harkar saboda hakan zai nuna wanene kai,'' in ji Dakta Carter. ''Haka kuma magana ce ta samun dama. Watkila dukkanmu kowa yana da burin idan ya samu kudi kazazai ce yana son ya je wuri kaza da kaza, to kuma su wadannan mutanen suna da wannan dama (kudi) saboda haka sai su dukufa.''

Dakta Carter ya ce, burin cimma wani kalubale ko yadda jikinsu ke angiza su su yi abin da suke so na kasadar nan yana taimakawa su irin wadannan mutane masu son hatsabibanci su yi amfani da damuwa ko zakuwar aikin da ke tare da su a wani abin da mafi tasiri.

''Idan ka yi tunanin gajiya za ka ga ba abu ba ne da za ka yaka ko ka kai wa hari, amma idan kana hawan wani dogon tsauni, za ka karkatar da karfinka da zuciyarka da yanayinka kan wannan abu, idan ka yi galaba a kansa, to ka cimma burinka,'' kamar yadda Dakta Carter ya ce.

A wani bangaren kuma su irin wadannan mutane sukan iya jefa kansu cikin hadari ba tare da sun sani ba.

Kuma abin da yake sa su hakan shi ne rashin damuwa ko tsoron da ba sa ji idan suna yin abu kamar wasa ko iyo a ruwa a kusa da katon kifin nan shark.

Bayan wannan ma kuma masu sha'awar kasada ba sa damuwa su lura da wata barzana kafin su yi abu, wannan ke sa su yi abu mai hadari ba tare da sun natsu sun duba ko akwai wani hadari da ke tattare da yin hakan a lokacin.

Hakkin mallakar hoto Daniel Audunsson

Daniel Audunsson mai shekara 25, wanda ainahinsa daga Bodmodsstadir da ke Ice land yake, ya yi hatsabibancin wasa da karamin jirgin sama da wasan tsere da motoci (lamborghinis), amma ya fi son tattakin dakake zuwa wani wuri da bai taba sani ba..

Akwai wani lokaci da ya taba tashi a lema daga shalkwatar kamfaninsa a Manila kasar Philippines, inda ya sauka a wani surkukin kauye, daga nan kuma ya sami wani mutum wanda bai sani ba ya dauko shi a babur ana ruwan sama, ya fito da shi zuwa wani wuri da ke da nisan tafiyar sa'a biyu.

Shi dai da zarar ya yi niyyar abin da zai yi to ba ya jin kira sai ya yi, ba zai fasa ba.

''Masana tunanin dan adam sun gaya min cewa ya kamata in rika yin taka tsan-tsan, saboda zan iya jefa kaina cikin hadari,'' in ji Audunsson. ''Duk abu daya ne a wurina, a duk wani fanni na rayuwa, kana jarraba wani abu za ka ga abin da za ka iya yi , za ka ga iyakarka da damar da kake da ita.

A matsayina na dan kasuwa, a ko da yaushe ina tura kaina zuwa iyaka, kuma yayin da na kai wannan iyaka, sai na yi kokarin kara turawa.''

Audunsson ya ce a wani lokacin yakan dogara ne dga shawar abokin kasuwancinsa, wanda yana da taka tsan-tsan.

Yayin da yake bayyana kansa a matsayin wanda ke hangen nesa a harkokin kasuwancinsu ta intanet, abokin nasa shi ke rike da ragamar harkar inda yake tsara abubuwa a sannu ya yi nazari kafin su yanke shawara.

Ina iyakar take ?

Idan kai mutum ne da ke da sha'awar shiga kasada za ka yi mamakin yadda ba za ka taba gajiya ba, musamman idan kana da kudin yin kusan komai.

Hakkin mallakar hoto Hilda Lunderstedt

Yayin da shekaru ke kama ta 'yar kasuwar Afrika ta Kudu mai zuba jari, Hilda Lunderstedt, mai shekara 49 ta ce yanzu sha'awarta ta za ma ta abubuwa masu sauki kamar shawagi ta ratsa kogin Nilu ta sama da kumbon balan-balan.

Ta ce ta yi wannan sauyi ne saboda yanzu tana da 'ya'ya da kuma yadda take ganin abokanta suna jin rauni a hatsabibancin da suke yi.

''Sai ka auna ka gani, shin abin da za ka yi yana da amfani, ganin yanzu ke uwa ce?''

Lunderstedt ta ce. ''Zan iya duba baya in yi tunani, in ce to ai na yi hakan a da, magana ce ta lokaci da dama, idan ban yi abin ba a da, sai in duba baya in ce da ma a ce na yi abin,''

Shi kuwa Silver wanda yake da 'ya'ya boiyu, cewa ya yi duk da cewa yana lissafin hadarin da yake shiga, duk da haka yana son cigaba da kara matsawa.

''Ba za ka iya tsara yadda za ka mutu ba, amma za ka iya tsa ra yadda za ka rayu,'' in ji Silver. ''Ina da abokan aiki da suke ce min 'kana da 'ya'ya bai kamata ka yi abu kaza ba'ni kuwa sai in ce musu ai abin da ya sa ma nake yi kenan, ina son su gan ni yi rayuwata yadda nake so.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The millionaire daredevils