Almubazzari ya auri matsoluwa- Ya kenan?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Ina ganin ka sha jin cewa kudi shi ne ke jawo musu da sabani tsakanin ma'aurata ko masoya da dama. To ko almubazzari zai iya auren matsoluwa kuma su zauna lami lafiya?

Kate Ashford ta duba lamarin

Tun daga ranar da suka hadu abu ne da yake a zahiri cewa Taylor Murray da matarsa kishiyoyin juna ne idan ana maganar kudi.

''Ni ne mai kashe kudi matata kuma mai tsimi,'' in ji Murray mai shekara 33 wanda ke zaune a California.

''Ta san nawa ne a cikin asusunmu na ajiya na banki da ka, ba tare da ta duba littafinmu na banki ba. Kuma tana da kafiya kan kin sayen wani abu wanda haka kawai yazo maka a rai ko kayi sha'awarsa.''

''Wani lokacin tana ganin ni almubazzari ne, ni kuma ina mata kallon matsoluwa ce.''

Wannan ya zama kamar hanyar magance matsalar aure, domin musu a kan kudi shi ne abin da ya fi haddasa mutuwar aure, kamar yadda binciken da aka yi a jami'ar jihar Kansas da ke Amurka ya nuna.

To amma sabanin haka, lamarin ya sha bamban a wurin Murray da matarsa.

Yana ganin su a nasu bangaren sun amfana ne daga dabi'a da ra'ayin junansu.

''Mun yi tafiye-tafiye masu dadi saboda sha'awata kuma za mu dade ba mu manta da su ba,'' in ji Murray, wanda kwararre ne wajen yin manhajar kwamfuta a kamfanin CallTools.com.

''Muna da gida mai kyau da tarin kudin da ya kai albashin wata shida a asusunmu, a matsayin na ko-ta-kwana, kuma duka wadannan sun samu ne sakamakon tattalinta.''

Ko da yake Murray da matarsa su dai sun yi nasara a zamantakewarsu ta aure duk da sabanin da suke da shi wurin kashe kudi, to amma abu ne mai wuyar gaske ka iya zaman aure da wadda ra'ayinka ya bambanta da nata ko nashi kan kashe kudi.

A wani bincike da aka yi, kusan rabin matsolo-matsolon da ke auren almubazzarai ne suke ganin su suna jin dadin aurensu, idan aka kwatanta da auren wadanda suke ganin tasu ta zo daya da abokan aurensu a fannin kashe kudi da tanadi.

Kamar yadda binciken na makarantar nazarin harkokion kasuwanci ta jami'ar Michigan a Amurka ya nuna.

Hakkin mallakar hoto Alamy

''Sabani a fannin tattalin kudi ka iya haifar da gagarumar matsala a tsakanin ma'aurata da kuma tsawon soyayya,'' in ji April Masini masaniya mai bai wa ma'aurata da masoya shawara kuma mai rubutu a shafin intanet na AskApril.com a Amurka.

''Bambance-bambancen na da wuya a iya magancewa,'' ta ce.

Amma kuma masu bambancin dabi'a a fannin kashe kudi suna sha'awar juna, in ji masana.

Duk da cewa za ka ji namiji ko matar da take ita kadai na cewa, ta fi ko ya fi son ya auri wadda halayyarsu ta kashe kudi ta zo daya, masu matsolanci sosai da kuma masu almubazzaranci sosai sun fi karkata ga junansu a aure, kamar yadda wani bincike da aka yi a jami'ar Northwestern da kuma makarantar harkokin kasuwanci ta Wharton a jami'ar Pennsylvania dukkaninsu a Amurka suka yi.

''Lalle kam , abu ne da yake faruwa ba shakka,'' in ji Farfesa Ewan Gillon masani kan tunanin dan adam a Scotland.

Ya ce, ''mun san cewa daya daga cikin abubuwan da ke jawo rikici tsakanin ma'aurata shi ne kudi.

Kuma ba abu ba ne na daban, ka ga cewa daya daga cikin ma'aurata ya kasance mai taka tsan-tsan da tsumi wajen kashe kudi sabanin dayan (matar ko mijin), wanda zai kashe kudi ba tare da damuwa ba, kan abin da zai iya faruwa nan gaba ba.''

Dadin abin shi ne akwai dabaru na yadda ma'aurata masu sabani kan tsimi da tanadi na kudi za su iya bi, kuma su zauna lafiya ba tare da wata matsala ba ta zamantakewa ko ta kudi.

Kowa yana son samun 'yanci da kuma yadda zai kula da harkokin kudinsa da kansa.

Domin samun hakan, sai a yi asusu guda uku; daya naka, daya na matarka sannan kuma dayan na harkokin gidan naku.

Duk abubuwan da suka shafi gidan ko kuma ku biyun sai a yi amfani da kudin asusun gidan.

Kuma kowannenku yana da asusunsa da zai yi amfani don harkokin kashin kansa kamar yadda yake so.

''Idan almubazzari daga cikinku na son sayen barasa ko wani abu na dala 600, shi kuwa mai tattali ko matsolo na son kashe kudi don zuwa yawon bude ido, sai kowa ya yi yadda yake so,'' in ji Julia Chung masaniya kan harkokin kudi da tsara gine-gine, wadda ke aiki da kamfanin JYC Financial a Langley, ta Columbian Biritaniya da ke Canada.

''Hakan na aiki da kyau kuma yana rage damuwa sannan kowa yana samun 'yanci da ikon da yake so.''

Ka duba wasu alamu:

''Ka nemi takardar bayanin kashe kudinka na banki na watanni uku da suka wuce, sannan ka yi alamomi daban-daban guda uku da za su bambanta bukatun dole da wadanda lalle kake so da kuma wadanda ba su zama dole ba kuma ka kashe kudi a kansu,'' in ji Jeff Motske masani kan harkokin kashe kudi kuma mawallafin littafin shawara ga ma'aurata kan kashe kudi, (The Couple's Guide to Financial Compatibility).

''Wannan zai taimaka wa mai kashe kudi da mai tattali su ga inda kudinsu yake tafiya.''

Hakkin mallakar hoto Alamy

Nemi shawarar kwararre:

Mai bayar da shawara kan harkokin kudi zai iya taimaka muku a matsayin ma'aurata ku tsara yadda za ku rika kashe kudinku na 'yan wasu shekaru.

''Na ga cewa yin tsarin kashe kudi abu ne mai muhimmanci sosai,'' Chung ta ce.

''Musamman ma ga wanda yake da dabi'ar kashe kudi barkatai, wannan zai fayyace masa dalilin da zai sa bai kamata ya kashe kudi kan wani abin ba.

Magana ce kan yin tsari, domin ya fahimci muhimmancin kudi a wurinsa da kuma dalilin da ya sa yake kashe kudin ta yadda yake kashewa.''

Ga Murray da matarsa kuwa, wata dabara da suke amfani da ita daga cikin dabarunsu, ita ce, ware kudin bushasha.

''Idan muka ga wani abu da muke so kuma muna da isasshen kudi a wannan asusu (na bushasha), sai mu sayi abin,'' in ji Murray.

''Amma dazarar wannan kudin ya kare, sai mu dakata da irin wannan siyayya.

Muna tara karin kudi sannan kuma muna musu da junanmu kadan. Sannan hakan yana koya min yadda zan kiyaye da saye-sayena na sha'awa wadanda nake yi barkatai.

Tattaunawar kudi a duk sati:

Idan har sai an samu wata matsala ne kawai za ku tattauna kan kudade, to matsaloli za su yi saurin taruwa.

'Idan kuna tattaunawa akai-akai kan harkokin kudinku, za ku fi samun kwanciyar hankali, dukkanninku biyun.

Sannan za ku fi saurin magance duk wani bambanci da zai iya tasowa tsakaninku,'' kamar yadda Monica Salazar, masaniya kan harkokin kudi a kasar Ecuador ta ce.

Ku sa iyaka kan kashe-kashen kudinku:

''Ku ware wani kaso na kudin da dukkaninku kuka amince za ku rika kashewa, wanda kuma sai kun yarda za ku kashe idan bukatar kashewar ta taso,'' in ji Masini.

''Ma'ana idan dala 300 ne ko 3,000 ku yanke shawara cewa dukkaninku ba za ku sayi komai ba da ya wuce wannan kudi, ba tare da kun tattauna kuma kun amince ba.''

Murray da matarsa suna bin wannan tsarin. ''Mun amince mu tattauna kan duk wata sayayyar da za mu yi,wadda ta wuce dala 200,'' ya ce.

''Wannan shi ya ba ni 'yanci da dama yadda nake da dabi'ar kashe kudi, in kashe yadda nake so, amma fa iya wannan kasafi na kudin bushasha.

Kayayyakin gida kuma wannan abu ne da muke tattaunawa tsakaninmu kafin mu yanke shawarar saye.''

Idan daya daga cikin ma'aurata ya rika haura wannan iyaka ta kudin da za a kashe, to kuna bukatar gudanar da bincike kan sauran hanyoyin kashe kudin ( ka ga ko can ma ya kashe), kamar katin sayayya na banki (credit card), tare da sanya masa ka'ida mai tsauri, ko kuma ku rika taro kan tattauna kudadenku akai-akai.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Ka dauka kai ne a halin da matarka ke ciki (ko ki dauka ke ce a halin da mijinki ke ciki):

Me ya sa matarka ko mijinki yake da wannan dabi'a a kan kudi (almubazzaranci ko matsolanci)?

Bai taso da kudi ba ne a rayuwarsa, shi ya sa yake tsantsan wajen kashe su? Ko kuma fama da ta yi na fafutukar ganin ta samu kudi tana yarinya, ita ta sa yanzu take almubazzaranci da su saboda ta same su?

''Fahimtar dalilan mijin naki ko matar taka na wannan dabi'a, ka iya sa ku hada kanku, ku yanke shawara kan yadda za ku rinka kashe kudinku, in ji Nikki Martinez, masani kan tunanin dan adam, mai bayar da shawara kan harkokin lafiya ta shafin intanet na BetterHelp.com.

Ka zama mai shirin sassauci kan ra'ayinka:

Zama da mutumin da yake da tunani daban da naka ko naki, abu ne da ke bukatar sassauci daga kowane bangare.

Idan daya daga cikinku ba zai taba yarda ko ya sassauto ya amince da bukatar dayan ba, wannan ba alama ce mai kyau ba,'' in ji Gillon.

''Shi sassauci domin samun daidaito yana amfanar dukkanku biyun, saboda haka ka tambayi kanka idan kana da taurin kai kamar abokiyar zamanka (matarka) ko kina da kafiya kamar mijinki.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan A spender marries a saver - now what?