Masu wayo sun fi yin tabargaza

Hakkin mallakar hoto Thinstock

Kana da wayo. Kai shugaba ne. Kuma watakila kana yin kura-kurai da yawa wadanda ba ka san ma kana yinsu ba.

Mutanen da suka fi basira da kuma manyan shugabanni wani lokaci suna kura-kuran da wasu mutanen ba sa yi.

Wannan magana ce da masana a harkar shafin nan da sada zumunta muhawara tsakanin ma'aikata ta intanet Linkedln suka duba a 'yan kwanakinnan. Ga abin da biyu daga cikinsu suka ce.

Travis Bradberry, shugaban kamfanin TalentSmart

''Abu ne mai kyau ka zamanto mai basira, domin ko ba komai masu basira suna samun kudi da tara dukiya mai yawa kuma suna tsawon rai fiye da sauran mutane,'' kamar yadda Bradberry ya rubuta a wata kasida (why Smart People Act So Stupid).

To sai dai akwai wata daban, domin mutane masu basira sun yi fice wajen tafka kura-kurai da hatta mutane gama-gari ma ba sa yi, musamman a yanayi da ake bukatar amfani da hankali.''

A karshe dai watakila masana kimiyya za su bayyana dalilin da hakan ke kasancewa.

A bayaninsa Bladberry ya ce, su mutane masu basira sukan bayar da amsar abu ne kai tsaye da karfin hali da kuma kwarin gwiwa, ba sa wata tantama a kan abin da suka fada.

Binciken ya bayyana dalilin da ya sa ''tunani na basira da tsagwaron basira kawai ba sa jituwa ko tafiya tare''.

Wasu jami'oi biyu sun gano cewa, ''mutane masu basira za su bayar da amsar da ba daidai ba, saboda sun fi yin kuskure idan a fannin bayar da amsar wata matsala ce,'' kamar yadda Bradberry ya rubuta.

''Masu basira sun fi yin kura-kurai na katobara saboda yadda suke amfani da basirarsu kusan a makance.

Wannan makanta ta amfani da basira tana kasancewa tare da su ne, saboda yadda suke yin abu gaba-gadi da zummar cewa daidai suke yi.

Domin gadarar da suke da ita cewa su mutane ne masu basira, saboda haka ba sa bukatar ma su tsaya su auna ko su yi lissafi sosai a kan abu, saboda sun saba fadin amsar da take daidai kusan a ko da yaushe.

Sai kawai su bayyana matsayinsu, wanda a ganinsu shi ne daidai ba wata shakka, amma kuma sai ya zama katobara (babban kuskure).''

Akwai ''hanyoyi da dama da mutane masu basira suke kunyata kansu''. Ga wasu daga cikinsu:

''Mutane masu basira suna da ci-da-zuci. Yawan yabon da ake yi musu saboda nasarar da suke samu ko kwarewar da suke nunawa kan sa su ji cewa su masu basira ne da kwarewa a ko da yaushe,'' in ji Bradberry.

''Masu basira ba sa fahimtar lokacin da suke da bukatar taimako, kuma lokacin da suka fahimci cewa lalle suna bukatar taimakon, to sai su ga ba wanda ya isa ya yi musu wannan taimakon (ba wanda yake da sani kamarsu).''

''A ko da yaushe daidai suke. Abu ne mai wuyar gaske su yarda cewa ba daidai suke ba, wato suna dauka a kullum sun san komai. Su masu basira suna da girman kai, saboda sun saba da su yi abu daidai kowane lokaci, wannan sai ya sa su dauka ai ba za su taba yin kuskure ba, har hakan ta zama jiki a wurinsu,'' kamar yadda Bradberry ya rubuta.

''Su mutane masu basira dauka suke idan suka yi abu ba daidai ba kamar wani hari ne aka kai musu, kuma yin abubu daidai abu ne da ya zama wajibi a wurinsu.''

''Da wuya suke karbar gyara. Mutane masu basira sukan rena sani da basirar sauran mutane, wanda hakan ke nufin abu ne mai wuya su yarda da ra'ayin wani, domin suna dauka ba wanda ya isa ya yi musu gyara,'' in ji Bradberry.

''Wannan dabi'a ta girman kai ba kawai tana tauye cigabansu da kokarinsu ba ne kadai, ta kan iya haifar da mummunar alaka tsakaninsu da sauran mutane da kuma abokan aiki.''

''Suna son takurawa ko sanya wa mutane tsanani. Masu basira sukan sa buri mai yawa a ransu saboda suna samun abu da sauki, domin suna da fahimtar abubuwa cikin sauki, sai su bukaci kowa ya yi kamar yadda za su yi, alhalin kuma sauran mutane ba su da irin basirarsu,'' masanin ya rubuta.

''Idan mutane suka kasa cimma abin da su masu basira suke bukata a wurinsu ko ba su yi daidai ba, sai su dauka ai mutanen ba su mayar da hankali ba ne. Saboda haka sai su kara matsawa mutane.''

Sai bayanin, shugaban kamfanin jirgin sama na Japan Yoshiharu Ueki:

''Idan har umarni kawai dukkanin ma'aikatanka za su rika karba, ba za su yi tunanin kansu ba, ta yaya za ka dore da samun nasara?'' tambayar kenan da Ueki ya yi a kasidarsa a shafin na intanet (it's OK to Polish but Don't Lose Your Edges). Ya rubuta cewa, wannan kuskure ne da yawancin masu basira suke yi, saboda suna dauka cewa ai dole ne ma su a daidai suke.

''A kullum za ka iya goge dutse (ya yi kyalli),'' amma da zarar ka nike shi (farfasa shi) ba zai sake dawowa yadda yake ba, in ji Ueki.

''Idan a ko da yaushe kana yi takura wa kananan ma'aikatanka da lalle sai sun bi tsarinka, har ya kasance tun farko sun saba da karbar umarni daga gareka domin komai ya tafi kan tsari daya kawai, ba za su taba kokarin kwarewa ta yadda su ma za su iya jagoranci ba,'' ya rubuta.

''To idan haka ta kasance wanene kenan zai shugabanci al'umma ta gaba idan shugabanci na yanzu ya kau?'' (idan ba makoyi ba gwani).

Idan ka samu kanka a irin wannan tarko, akwai abubuwan da za ka yi ka sauya, in ji Ueki.

''Ka sanya sabbin ma'aikata a cikin masu yanke shawara kan harkokin kamfanin. Bayan ka bai wa ma'aikatanka wannan dama, to ka guji karawa mutanen da suke da sani da fahimta sosai amma kuma ba sa iya ba da shawara sosai girma,'' kamar yadda ya rubuta.

Ba lalle ba ne shugabanni na gaba su kasance kwararru a fannin da suke aiki kawai.

Dole ne mu tabbatar mun horar tare da bunkasa fannonin da ma'aikatanmu suke da sani daban-daban, ta yadda kamfaninka zai kasance yana da kwararru ta kowane fanni. Duk abin da ya bullo za a san yadda za a iya tunkararsa a magance shi.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why clever people make more stupid mistakes than most