Ka san hanyar tsimi da tanadin kudi?

Me ya sa wadansu mutanen a koyaushe suke da isasshen kudi, amma kai da zaran wata ya kare sai ka zama ba ko kwabo a hannunka?

Za ta iya kasancewa su suna bin wasu shawarwari ne na kashe kudi, wadanda kai ba ka tunaninsu, har ka rika almubazzaranci?

Wannan ba shawara ba ce da yawanci ka kan ji daga kwararru. Yawanci wata magana ce da kakanka ya taba gaya maka, ko kuma wani da ba ka yi tsammani ba ya fada maka.

Mun mika wannan tambaya shafin intanet na BBC (na Ingilishi) na tambaya da amsa, domin jin shawarar tsimi da tanadin kudi mafi kyau da aka taba ba mutane.

Ga abubuwan da wasu suka rubuto:

Michelle Gaugy ta ce shawarar kashe kudi mafi kyau da aka taba ba ta, ta same ta ne a wurin wasan cacar karta (poker) a Reno da ke Nevada a Amurka.

Ta ce, ''a lokacin da ake cacar kowa da kowa na nan, ina jin dadin yadda take kasancewa, sai kawai na ga, sauran wadanda muke kartar da su daya bayan daya kowa na sulalewa, suka barni ni kadai, ga lale ya yi min kyau amma ba kudi a gabana.''

Ta rubuta cewa bakin cikinta a bayyane yake, har ma ta kai ga furta wata kalma maras dadi a game da 'yan kudin da suka rage a gabanta.

Ta ce, ''tsohon mutumin da ke can daya bangaren tebur din da muke wasan cacar sai ya tura malafarsa keya, ya kalle ni, ya yi dariya, ya ce, 'yarinya kada ki taba manta cewa, ko ya nasara take ta fi rashin nasara'.''

Yi amfani da 'yar damar da kake da ita

A rubutun da ta aiko mana ne Gaugy ta ce tun daga wannan lokacin har yanzu ba ta manta da wannan magana ba.

Ta kara da cewa, ''Abu ne mai sauki ka dauka cewa nasarar da ba ta taka kara ta karya ba, ba ta da wani amfani.

To kada mu sake mu yi haka. Wannan nasara tana da muhimmanci sosai, domin duk yadda kankantarta take ta fi rashin nasara.''

Sanin darajar kudi

Steven Dillard ya rubuto cewa, tunanin adana duk dan kudin da zai iya, ya shiga rayuwarsa. ''Duk kwabon da ka adana kamar wanda ka samu ne,'' yadda ya rubuto.

''Wannan dabarar ta sa min tsoron Ubangiji kuma a kodayaushe ina kokarin adana duk abin da zan iya.''

Dillard wanda yanzu yake shirin yin ritaya daga aiki da wuri haka, ya ce ''domin jin dadin rayuwa kuma na zabi yin abin da nake son yi maimakon yin abin da wani zai gaya min na yi.''

Tarkon bashi

Marubuciyar littattafan yara kuma edita, Lily Aleksey, ta rubuta cewa abubuwa biyu kawai za ka yi; kada ka jefa kanka cikin wani babban bashi kuma ka sayi gida a lokacin da farashi ya yi kasa.

Wadannan abubuwa biyu su ne suka sa take zaune lami lafiya duk tsawon shekarun da suka gabata.

Alksey ta rubuta cewa ta koyi wannan darasi ne daga irin rayuwar da iyayenta suka yi, ta rashin kashe makudan kudade.

''Na fahimci cewa yawancin abubuwan da mutane ke kashe kudinsu a kai ba abubuwa ba ne da suka cancanta, kuma zan iya rayuwa cikin farin ciki ba tare da su ba.''

Aleksey ta ce idan ba ka fada tarkon kashe kudi da yawa ba, rayuwarka gaba daya za ta iya sauyawa'' saboda nan gaba, ba sai ka samu kudi masu yawa ba, abin da ke nufin ba sai ka dage aiki tukuru ba, ko kuma ka yi wani aiki da ake biyanka albashi mai yawa ba''.

Maimakon haka ta rubuta cewa, za ka iya zabar wani aiki da kake sha'awa wanda kuma ba wani na samun kudi ba ne sosai, ko kuma za ka iya aikin wucin-gadi ta yadda za ka iya samun isasshen lokacin da za ka zauna da iyalanka ko kuma ka samu lokacin yin wasu abubuwan da kake kauna.

Ka fara da wuri

Shi kuwa Jami Keller shawararsa ita ce ka dan kasance mai tunkarar matsala ko wani kalubale daidai yadda za ka iya, kuma a bisa yadda ya kamata, kada ka daukar wa kanka dala ba gammo.

Ya ce, ka fara tanadi ko zuba jari na ritayarka tun kana dan shekara 20 da wani abu, saboda duk dala daya a wadannan shekaru goma na farko ta kai dala 10 zuwa 15 a shekarunka na gaba idan ka zuba jari.''

Keller ya ce, ya farga da hakan ne bayan da ya ji a jikinsa, kasancewar ya yi kunnen kashi da kyakkyawar shawarar da aka ba shi tun da farko, kamar yadda aka ce ''jiki magayi''!

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Smart money advice, from poker playing cowboys?