Illar mugun shugaba ta kai ta taba

Hakkin mallakar hoto alamy

Za a iya kawatanta illar da mugun shugaban wurin aikinka ke yi wa lafiyarka da yadda hayakin tabar da mutane ke sha ke yi maka?

Illar da aiki a karkashin shugaban da ba shi da dadin sha'ani ke yi wa lafiyar ma'aikaci kenan a hankali a hankali kamar yadda wani rahoto da shafin intanet na Linkedn wanda Quartz ya wallafa ya nuna.

Yawan dadewarka kana aiki a karkashin shugaban da ba ya mutunta ma'aikatansa, iya yawan illar da hakan ke yi wa lafiyar jikinka da ta kwakwalwarka.

Kungiyar masana tunanin dan adam ta Amurka ta bayar da rahoton cewa kashi 75 cikin dari na ma'aikatan kasar na nuna cewa shugaban wurin aikinsu ne babbar matsalar da ke sanya musu damuwa a wurin aiki.

Amma kuma mafi yawan ma'aikatan da ba su da shugaba na gari,su kashi 59 cikin dari ba sa barin aikin, kamar yadda kafar yada labaran kasuwanci ta Quartz ta ruwaito.

Rahoton ya ce ga alama mutane suna jin dadin aikinsu, ko da kuwa ana muzguna musu, abin da ya sa da wuya su bar aikin, su nemi wani mafi kwanciyar hankali.

Hakkin mallakar hoto alamy

Masana daga makarantar nazarin harkokin kasuwanci ta Havard da kuma jami'ar Stanford a Amurka, sun tattara bayanai na sama da bincike 200, inda suka gano cewa galibin damuwar wurin aiki da ma'aikata ke fama da ita, tana da illa iri daya ga lafiya da hayakin da mutum ke shaka na tabar da wasu ke sha.

Babban abin da ke sanya wa ma'aikaci damuwa, shi ne rasa aikinsa, abin da ke jefa rayuwarka kashi 50 cikin dari a hadarin rashin lafiya, in ji rahoton na Quartz.

Idan kuma ya kasance an ba ka aikin da ke da bukata matuka sosai ne, wadda ta wuce ka'ida, to hakan zai sa ka kasance kashi 35 cikin dari a hadarin kamuwa da wani ciwo.

Hakuri har ka gudu

Duk da cewa a wani lokacin wani ma'aikacin ne mai dagawa ke sa shugaba ya zama mugu, amma akwai shugabannin marassa kirki.

A irin haka ta yaya za ka iya bambancewa tsakanin wanda daman mugu ne da kuma wanda ma'aikaci ya sa shi rashin kirkin?

Shugaban wurin aiki wanda daman mugu ne za ka ga, ya cika yawan fada, yana da son jikinsa, ko ka ga yana da son tashin hankali.

Idan ka kasa rarrabewa tsakaninsu, to ga mafita.

A yanayi na wahalar samun aiki sauya wani sabon wuri ba zabi ba ne da ya dace.

Abu ne mai sauki ka rasa kwarin gwiwar yin aiki mai kyau. Amma akwai dabaru masu sauki da za su iya taimaka maka ka ci gaba kuma su karfafa maka gwiwa.

Ka rubuta jerin abubuwan da kake so ka cimma buri a kullum, yadda za ka rika goge kowanne da zarar ka same shi.

Wannan biyan bukatar zai iya karfafa maka gwiwa ka ci gaba. Kashe wayarka ko kuma ka daina duba wasikarka ta email a karshen mako wannan zai iya kara zaburar da kai a kan aikinka ko da kuwa na dan gajeren lokaci ne.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan An awful boss could be as bad for your health as cigarettes