Ruwa zai zama gwal ?

Hakkin mallakar hoto alamy

Abin da zai iya sa harkar samar da ruwa ta zama harka mafi daraja ta gaba a duniya, shi ne karancin ruwan wanda shi ne kashi kusan 97 cikin dari na doron duniya.

Bryan Borzykowski ya yi nazari a kai

Tambayi Eoin Fahy ya gaya maka daga cikin albarkatun duniya wannene ya fi daraja, ba tare da wani jinkiri ba zai ba ka amsa.

Fannonin zuba jari

Eoin ya ce, ''abu ne da yake bayyane karara. ''Ruwa shi ne abu mafi muhimmanci a duniya.''

Yawanci wannan amsa tana ba mutane mamaki, ya ce musamman ma yadda yawancin masu zuba jari suka sanya hankalinsu a kan farashin mai da ke faduwa.

Kari kuma a kan wannan, yadda yawancin mutane a kasashen da suka ci gaba na duniya ba su dauki samun ruwa mai tsafta wata matsala ba, ganin yadda da zarar sun kunna famfo a gidansu za su gan shi.

To sai dai ruwa fa abu ne mai iyaka, wanda kuma yake bacewa a hankali a hankali.

Fahy, masani kan dabarun zuba jari kuma babban mai tsare-tsaren tattalin arziki na kamfanin zuba jari na Kleinwort Benson Investors da ke Dublin, kwararre ne a fannin zuba jari a harkar samar da ruwa.

Ta wasu hanyoyin, harkar ruwa aba ce mai daraja wajen zuba jari, kuma ba kamar mai ba, ba za a iya jujjuya ruwa ba, sannan abu ne da kowa yake bukata ya rayu, in ji Fahy.

A daya fannin, samar da wutar lantarki ta hasken rana da kuma ta iska sun zama wasu hanyoyi na karin dogaro wajen samun makamashi.

Fahy, ya ce, ''ruwan da ake samarwa a kayyade yake kuma ba za ka iya kara yawan ba.''

''Sannan kuma za ka iya rayuwa ba tare da mai da sauran nau'ukan makamashi masu gurbata yanayi ba, amma ba za ka iya rayuwa ba tare da ruwa ba, kuma wannan na daga dalilan maganar zuba jarin, wato tsagwaron amfanin abun.''

Duk da cewa harkar yanzu take tasowa, amma tuni wasu hannayen jarin da ke da alaka da ruwa suka fara samar da riba ta kashi dari bisa dari, kuma da alamun harkar za ta kara bunkasa kamar yadda Fahy ya ce.

Rikicin ruwa

Matsalar ba wai cewa ruwan da yake a duniya kalilan ne ba, abin shi ne babu isasshen tsaftaceccen ruwan ne.

Kashi daya bisa dari ne kawai mutane za su iya sha. Kamar yadda hukumar kare muhalli ta Amurka ta bayyana.

Har yanzu akwai matukar tsadar kafa tashoshin gyara ruwan gishiri, wanda shi ne kashi 97 cikin dari na ruwan duniya, ya zama na sha.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Kashi daya bisa dari ne kadai na ruwan duniya mutane za su iya sha

Abubuwan da ke haddasa karancin ruwan mai kyau sun hada da ayyukan da ke kawo gurbatarsa da yawan jama'a da karin bukatar ruuwan a kusan komai, kama daga aikin gona da samar da makamashi ga ayyukan lafiya da masana'antu.

Yayin matsalar karancin ruwan sama ke kara zama babbar matsalar Amurka , lamarin ya ma fi kamari a China, kamar yadda Deane Dray babban jammi'i a kamfanin kasuwar hannun jari na RBC Capital Markets, kuma mai ba da shawara ga Majalisar Dinkin Duniya a kan harkokin ruwa.

Ya ce, ''ba tare da wata muhawara ba, yanayin can ya fi tsanani.'' Al'ummar biranen China na karuwa cikin sauri, inda Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutane miliyan 292 ne za su yi kaura daga zuwa birane a kasar tsakanin 2014 da 2050, wanda hakan zai sa bukatar ruwan ta karu a wadannan yankuna in ji Dray.

Kamar sauran kasashe, China tana samun ruwanta ne daga koguna da tafkuna, wanda kusan rabi a gurbace suke.

Kuma kusan yawancin ruwan da ake amfani da shi a kasar yana yankin kudu ne, yayin da yawancin al'ummarta suke zaune a arewa.

Kafin China ta shawo kan matsalar ruwanta sai ta kashe dimbin kudi (dubban biliyoyin dala) kamar yadda wani rahoto na shekara ta 2013 na kamfanin McKinsey & Company ya bayyana.

Wasu kasashen da suka hada da Indiya da Australiya da Isra'ila da Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu sassan Afrika su ma suna fama da matsalar karancin ruwan.

Kuma yadda yawan al'ummar duniya ke karuwa, hatta kasashen da ke da wadatar ruwa kamar su Brazil da Kanada da Rasha su ma za su fuskanci matsalar a nan gaba, in ji Dray.

Damar saka jari

Domin kauce wa matsala dole ne gwamnatoci su tashi tsaye domin maganin karancin ruwan, inda a nan ne damar zuba jari ta shigo.

Fahyi ya ce, hanya mafi sauki ta samun kudi ta wannan matsala, ita ce, mallakar hannayen jari a kamfanonin da ke aikin inganta ruwa.

Wannan zai iya hadawa da ayyukan cibiyoyin sarrafa ruwa mai gishiri ya zama na sha mai kyau da ayyukan gina madatsan ruwa da cibiyoyin samar da ruwan duka su dukufa wajen aikin tsaftace ruwan.

Wadanda suke son karin ilimi a harkar sai su karanta kasidar Global Water Intelligence, in ji Dray, wadda ta kunshi harkokin fannin samar da ruwan.

Duk da cewa wannan harka ce ta tsawon lokaci, duk da haka a yanzu matsalar take tasowa, kuma wanda ya zuba jari a ciki zai samu riba mai kyau a yanzu ma.

Ma'aunin ci gaban harkokin samar da ruwa na duniya na S&P Water Index, wanda ke bin diddigin ayyukan kamfanoni 50 a duniya wadanda suke harkokin kasuwanci da suka shafi ruwa yana da ribar kashi takwas da digo daya cikin dari a shekara da kuma ribar kashi bakwai cikin dari a duk shekara tsawon shekara uku.

Ma'ana wadannan kamafanoni suna samun wannan riba kenan a duk shekara.

Duk da cewa wannan kasa yake da ribar kashi 12 cikin dari ta ma'aunin kasuwar hannun jari na S&P 500 a duk shekara, amma dai abu ne da ya kamata masu sha'awar jarraba harkar samar da ruwan ta tsawon lokaci su gwada, in ji Dray.

Daga cikin manyan hannayen jarin kamfanonin da ke cikin tsarin Fahy, akwai na kamfanin gyaran ruwa na Amurka (American Water Works) da wani kamfanin kimiyya da fasaha mai suna Danaher Corporation, wadanda dukkaninsu sun kai darajar sama da kashi 121 cikin dari a cikin shekaru biyar da suka wuce.

Dukkaninsu kuma kamfanoni da ake gudanar da su da kyau, wanda hakan ne ya sa ake samun riba sosai a cikinsu, in ji shi.

Hakkin mallakar hoto alamy

Amma yana da kyau a sani cewa yayin da hannayen jarin wasu kamfanoni masu harkar ruwa suke samun riba sosai, wasu kuwa suna faduwa ne sosai.

Saboda kawai kamfanonin Fahy guda biyu suna samun cigaba sosai, hakan ba yana nufin za su yi ta cigaban ba kenan.

Wata fitacciyar matsala a wannan a fannin wannan zuba jarin, ita ce yawancin kamfanonin suna wasu harkokin a wasu fannonin.

A Danaher, kashi 12 ne cikin dari kawai na harkokin kamfanin ya shafi ruwa.

Haka shi ma kamfanin General Electric, wanda yana daga cikin kamfanonin da ke jerin masu hannayen jarin da ke bunkasa na Dray, kadan daga cikin harkokinsa ne a fannin ruwa.

Yayin da wannan ke nuna cewa manyan kamfanoni sun san amfanin da ke tattare da harkar ruwa, abu ne mai wuya mutane su dogara kacokan kan harkar kasuwancin ta ruwa.

Sayen ainahin ruwa

Wata hanay ta zuba jari a harkar ruwa ita ce ta hanyar mallakar ruwan kai tsaye.

A Australia, 'yan kasuwa sukan sayi hannun jarin kamfanonin da suka mallaki wuraren samar da ruwa, ko kuma wadanda suka de damar amfani da wasu bangarori na tafki ko kogi.

Kamfanin zai iya sayar damar amfani da ruwan ga wani ko ya bar wani kamfanin misali na harkokin aikin gona, ya rika amfani da ruwan yana biyansa.

Euan Friday, baban jami'in da ke kula da harkokin ruwa a kamfanin zuba hannun jari na Kilter Rural wanda ke Australia, ya ce wannan kasuwar ta ruwa ta fara ne a farkon shekarun 1990, lokacin da ake amfanin da ya wuce ka'ida da tafkin Murray-Darling na kudu maso gabashin Australia.

Hakkin mallakar hoto alamy

Kamfanin Friday ya mallaki kusan kashi daya bisa dari na ruwa a tafkin, kuma 'yan kasuwa za su iya biyan dala 14, 1555 domin hayar yin amfani da ruwan.

Wadannan 'yan kasuwa na shi suna samun ribar kashi hudu zuwa bakwai cikin dari a shekara kamar yadda ya ce.

Ribar da yake samu ta danganta ne ga yanayi da kuma yadda bukatar kasuwa take.

Idan aka yi ruwa sosai, to masu hayar amfani da ruwan ba sa bukatar ruwa da yawa, sanda haka sai farashi ya fadi.

Idan kuma shekara ta kasance mai zafi sai farashin ruwan ya tashi.

Friday ya ce babu wurare da yawa da mutum zai yi irin wannan harkar kasuwancin, saboda ta wani fannin kasashe masu tasowa kamar China da Kudancin Amurka suna da dokoki masu tsauri a kan amfani da ruwa.

Duk da haka yadda wannan harka ta yadda kamfanoni ke shiga harkar samar da ruwa ta fara kankama, haka alfanu da damar da ke cikin harkar za su bunkasa.

Fahy ya ce, ''Magana ce mai dadi.'' ya kara da cewa, ''tana daya daga cikin manyan matsalolin jama'a da za mu fuskanta a shekaru goma zuwa ashirin nan gaba.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Is this the real liquid gold?