Idan so samu ne za ka so yau a haife ka a Iran?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Dalilin da ya sa Iran ta fi dacewa da wurin haihuwar mutum a yau. Abu ne da ya shafi magana kan ainahin abin da ke sa kasa ta amsa sunanta kasa ko kuma kamfani ya kasance mai bunkasa da kuma buri da fata.

Idan har kana da zabin inda za ka so a haife ka yau, ina za ka zaba? Me ke sa kasa ko kamfani ya kasance cike da dama ga kowane mutum?

Wadannan na daga abubuwan da masana harkokin kasuwanci da aiki a shafin sada zumunta na ma'aikata ta intanet na Linkedln suka auna a cikin watan Disambar nan da ya wuce.

Ga kuma abin da biyu daga cikinsu suka ce.

Ian Bremmer shugaban kamfanin Eurasia Group

''Sanin abin da ka sani da kuma amann da abin da ka yi amanna da shi, idan kana da damar zabin inda za a sake haihuwarka a duk fadin duniyar nan a yau, ina za ka zaba?,''

Wannan ita ce tambayar da Bremmer ya yi a kasidarsa mai suna Ina Za Ka So a Haife Ka Yau? Ya bayyana amsoshi uku.

Ya rubuta cewa, ''abu ne mai wuya na ki zabar Amurka, ba wai kawai domin kasata ce ba.''

Shi dai Bremmer ba ya fito ne daga gidan iyalai masu hali ba, wato iyayensa ba masu kudi ko wani matsayi ba ne, ya taso ne a unguwa ta talakawa a kudancin Boston, kuma mahaifinsa ya mutu lokacin yana dan shekara hudu. A lokacin dan kudin da iyalan suke da shi ba shi da yawa.

Ya ce, ''duk da haka mahaifiyata ta dage sosai ta tabbaatr na samu ilimi mai kyau. A kan wannan harsashin ne na kirkiri rayuwata, ma'ana na samar da tushen abin da na zama yau,'' kamar yadda ya rubuta.

Ya kara da cewa, ''hatta wanda ya fi kishin kasa a cikinmu ya san cewa Amurka na cigaba da samun matsaloli kuma inagncin damar da mutum zai samu a rayuwa na cigaba da zama fata kawai.

Kuma idan mace aka haife ki, idan an haife ka ko ke a cikin 'yan tsirarun kabilu, ko idan kai dan luwadi ne ko 'yar madigo ce ko idan an haife ka da wata nakasa, za ka iya fuskantar wasu matsaloli.''

Zabi na biyu na Bremmer zai iya ba ka mamaki sosai. Domin kasar da ya zaba ita ce Iran.

Ya rubuta cewa, ''Watakila za ka so ka kasance dan kasar da ke kokarin gina kanta.

Dage jerin takukumin da aka yi wa kasar ya sa dimbin matasa Iraniyawa sun tashi tsaye cike da buri da fata.

A karon farko a rayuwarsu, basirarsu da burinsu sun zama masu muhimmanci.''Yadda ya rubuta.

Ya kara da cewa, ''Wannan kasa ce mai abubuwa da dama da kuma tattalin arziki mai fannoni da dama.... tattare da abubuwa da za su bunkasa.

Saboda haka kasancewa cikin wannan tafiya abu ne mai matukar ban sha'awa.''

Hakkin mallakar hoto Alamy

Zabinsa na karshe kuwa shi ne: Kasar Bhutan da ke yankin tsaunukan Himalaya a kudancin Asiya, wanda wuri ne da ya ke gani na cike da neman basira da farin ciki.

Bremmer ya rubuta cewa, ''lokacin da na ziyarci kasar a 'yan shekarun da suka gabata, na ga mutane wadanda su ke da lokaci da kuma sararin yin tunani, da numfashi da kuma mu'amulla da juna.''

Shi kuwa Josh Bersin babban jami'i kuma wanda ya kafa kamfanin Bersin by Deloitte, ga bayani da zabin da ya yi.

Idan kana neman wurin aikin da za ka samu karbuwa, to wannan sabuwar shekara ta 2016 da aka shiga shi ne lokacin da ya fi dacewa ka nemi wurin.

Shekara ta 2016 za ta kasance mai cike da dama iri-iri ta harkokin kasuwanci?

Tambayar kenan da Bersin ya jefa a kasidar da ya rubuta mai suna abin da ya sa tattalin arziki mai fannoni da dama da kuma shigar da 'yan kasuwa cikin harkokin tattalin arziki za su zama abin da za a fi ba wa fifiko a 2016 (Why Diversity and Inclusion Will Be a Top Priority for 2016). Amsarsa ita ce e!

Abin da ya rubuta shi ne, ''a duniyar aiki ta yau, kokarinka na jawowa da shigar da kowa da kowa manya da matasa, daga kowace al'umma da matsayi da jinsi abu ne da ya zama dole ga nasarar kasuwancinka.

Ya kara da cewa, ''bincike ya tabbatar cewa kamfanonin da su ke da ma'aikata daga bangarori daban-daban sun fi takwarorinsu cigaba sosai.''

Kamfanonin da su ke da danbarun da aka hada da tsarin hadakar gwamnati da 'yan kasuwa da kuma fannonin harkoki daban-daban, misali suna samun karin shigowar kudade 2.3 a kan duk ma'aikaci daya, kuma za su fi zama gaba wajen kirkira sau 1.7 a harkokin kasuwancinsu.'' In ji Bersin.

Ba shakka wasu dabarun sun fi wasu tasiri. ''Amma fannoni biyu da suka fi amfani, su ne wadanda su ke da alaka da babban tasirin da ake samu wajen wanzuwa da cigaban kasuwanci, kuma su ne na rarraba kafa da kuma hadaka ta gwamnati da 'yan kasuwa.

Shigar da 'yan kasuwa shi ne burin kuma fadada harkokin kasuwancin shi ne ma'aunin nasarar.'' Yadda Bersin ya rubuta.

Ya kara da cewa, ''Wannan yana bukatar cakuda tsarin hadaka tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa da kuma fadada harkokin kasuwanci wajen daukar ma'aikata da lura da kokarinsu da tabbatar da dorewar bunkasar harkar da samar da shugabanci da koyo da kuma musamman auna yawan bambance-bambancen da a ke da shi a wurin da dorawa shugabanni alhakin duk sakamakon da aka samu.''

Hakkin mallakar hoto alamy

Me ya sa haka? Watakila abu ne da ya ke a zahiri, amma ''mutane sun fi kokari da jajircewa a kan abu idan sun san an dauke su da daraja, da ba su kwarin gwiwa da kuma ganin cewa takwarorinsu na mutunta su.'' In ji Bersin.

Idan wannan ta kasance, ''a harkar kasuwanci a yau, kamfanonin da suka gina tsari na gaskiya na hada gwamnati da 'yan kasuwa za su fi takwarorinsu bunkasa.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan This is why Iran could be the best place to be born today