Ainahin yadda ake zama shugaba

Hakkin mallakar hoto istock

Ba shakka abu ne mai dadin ji a ce kai ne shugaba. To amma kana da kwarewa da iyawa da duk abin da ake bukata na shugabanci da kula da jama'a da kuma samun hadin kansu?

Yawancinmu muna da burin samun babban mukami a wurin aikinmu, muna son zama shugaba. To amma shakka babu ba a ko da yaushe ba ne mu ke samun abin da mu kai tsammani, ko samun sauki na mukamin.

Ma'ana dadi da kuma saukin da muke tsammani na tattare da shugabanci ba lalle ba ne mu samu hakan. Wannan ya fi kasancewa a kan masu harkokin kasuwanci ko kamfani.

Sirrin nasara a shugabanci dabaru ne, kuma masu muhimmanci. Wannan batu ne da yawancin masana a shafin sada zumunta da muhawara na intanet, wanda ya kunshi harkokin aiki, Linkedln suka tattauna a kai a 'yan kwanakin nan.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Ga abin da biyu daga cikinsu su ka ce, kan abin da suke gani mutum ya ke bukata ya zama dan kasuwa da kuma shugaba a wurin aiki.

Richard Branson wanda ya kafa kamfanin Virgin Group;

''Yawancin lokaci a kan tambaye ni, ''wai ta yaya a ke zama shugaba?' tambaya ce mai wuyar amsawa.''

Abin da Branson ya rubuta ke nan a kasidarsa a shafin na Linkedln mai suna, Ta yaya ake zama shugaba? Shugaba da Jagora ( 'What Does it Take to Be the Boss?' Managers Versus Leaders).

Aikin jagora, kamar yadda ya rubuta, shi ne aiki da mutane, ''sauya rayuwar mutane ta zama mafi inganci''. Shi kuwa shugabanci ko sanya ido, ''abu ne da ya kunshi tabbatar da dorewar tsari da da'a da kuma ayyuka.

Inda masu sanya ido da kula da aiki suka kiyaye da doka, jagorori sai su zama masu son karya su, ko kuma akalla su gano wasu hanyoyi na dabaru a kansu.'' In ji Branson.

Dukkanin wadannan na da muhimmanci a harkar kasuwanci da kuma zama shugaba, amma dole ne ya kasance kana da abubuwan da jagoranci ke bukata'' musamman idan kana son kafa kasuwanci na kanka, kamar yadda ya rubuta.

Sirrin abin shi ne ya kasance kana da dukkanin wadannan mutane biyu a kamfani domin dacewa da nasara.

''Harkokin kasuwanci a duniya na bukatar shugabanni (masu lura) da kuma jagorori da za su yi aikin babban shugaba (boss),'' In ji Branson.

Hakkin mallakar hoto PA

Branson ya rubuta cewa, ''Idan ka yi imani da abu, karfin imaninka zai jawo hankalin wasu, hakan zai taimaka maka ka dauki mutanen da su ke da irin wannan fata naka, kuma za su samu kwarin gwiwar taimaka maka ka ci nasara.''

''Kuma sha'awa ba kawai hanya ce mai sauki ta iya daukar ma'aikata ba, bayan haka za ta taimaka maka ka samo mutane da za ku kulla kyakkyawar alaka da hadaka da sauran 'yan kasuwa da masu kamfanoni.

Da yawa daga cikin wadannan za su iya kasancewa shugabanni na gari wadanda za su iya taimakawa kasuwancinka ya bunkasa.''

Ga abin da Ron Shaich, shugaba, sannan babban jami'i kuma wanda ya kafa gidan burodi na Panera ya rubuta.

''A wurina kasancewa shugaba na nufin samun lokaci kai kadai kana tunanin kalubale, '' Kamar yadda ya rubuta.

Ya kara da cewa, ''yana nufin rashin barci da daddare, kana ta auna abubuwa da zabin abin da ya kamata ka yi, kafin ka yanke hukunci mai matukar muhimmanci, wanda ba wanda yake son a ce shi ne ya dauki wannan mataki, sanin cewa nasara ko akasinta alhaki ne da ya rataya a wuyana. Shugabanci na nufin zufa (wuya) da bayanai.''

Shaich ya gabatar da abin da ya kira ''wuyar shugabanci''. Daga cikinsu akwai;

Ya ce,'' galibi kasuwancin ne ya mallake ka, ba kai ne ka mallake shi ba.'' ya kara da cewa, ''gina kasuwanci abu ne mai cin lokaci, domin abu ne da zai cinye maka dukkanin lokacinka na harkoki da kuma yawancin sa'o'inka na barci.

Yana tare da kai a mota da bandaki da kuma lokacin hutu. Yawancin mutanen da suka gina harkokin kasuwanci ba za su iya dakatawa ko kuma rage kwazo da himmarsu na cigaba ba.

Za ka kasance da abubuwa da dama da za ka yanke hukunci a kansu, saboda kalubalen shugaba ba ya taba karewa.

Muddin wannan kasuwanci alhakinka ne, to kana bukatar tunanin yadda zai dore har can gaba. Kana bukatar kirkira da maimaici (har ka dace) da kuma cigaba.

''Abin mamakin shi ne idan har ka sance ka yi nasara, to ba zai zama cewa harkoki kadan ka ke tafiyarwa ba, zai kasance ka fadada zuwa fannoni da dama.''

Idan kana jin hakan jan aiki ne, Shaich ya ce, to shi kam har yanzu wannan ba abu ne da zai yi sake ya bayar da shi cikin sauki ba.

Ya ce, ''duk da cewa kasancewa shugaba wani lokaci zai iya zama kamar wata doguwar tafiya ta kai kadai, yana da riba.

Kuma wannan riba ba iko ba ne, ba kuma kudi ba.'' Ya ce, ''a wurina wannan riba ita ce dadin da na ke ji na magance matsalar da ba wanda ya iya magance ta.

Ladan shi ne ganin tarin damar da wasu ba su gani ba, ko kuma ta kufce musu, da kuma kirkiro dabarun da wasu ba su iya kirkirowa ba ko ma tunaninsu ba su yi ba. Harwayau ribar dai ita ce gina kasuwanci tun daga tushe.

Ya kammala da cewa ''Kasancewa shugaba abu ne da ribarsa ba ta da iyaka, idan har ka fahimci burin da ka sa a gaba.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan What it really takes to be the boss