Ana nuna maka bambanci a albashi?

Me ya kamata ka yi idan ana nuna maka bambanci tsakaninka da sauran ma'aikata wajen yawan albashi ko kuma a wasu fannonin na aiki?

Karanta wannan bayani na Chana R Schoenberger.

A kwanan nan wani mutum ya shigo cikin ayarina wanda yawanci ya kunshi mata ne kwararru a fannonin ayyuka daban-daban.

Na yi mamaki ganin yadda ya ke daukar albashin da ya fi na matan da su ke matsayi daya da shi kuma wadanda suka ma riga shi fara aiki da kamfanin.

Sai na ji abin ya bani mamaki, na ce, ta yaya za a samu wurin aiki irin wannan a shekara ta 2015?

Me zan iya yi, kuma ta yaya zan hana sake faruwar irin haka nan gaba?

Ga matsalarka a nan

Amsa: Kana ganin wannan wani abu ne na daban? To ka sake tunani. Domin wani lokaci akwai kanshin gaskiya kan dalilin nuna wani bambanci ko wariya, kuma lalle wani lokacin a kan biya maza albashi fiye da mata a aiki iri daya.

Wannan shi ya sa a ke da dokokin hana nuna bambanci a kasashe da dama, domin hana wa da kuma gyara irin wadannan matsaloli.

Idan kana zaune ne a wurin da a ke da dokar da ta haramta nuna bambancin albashi bisa bambancin jinsi, to kamfaninka yana karya doka ta hanyar biyan namiji kudin da ya fi na mace wadda su ke mataki daya.

Amma wannan zai kasance gaskiya idan har namijin da matar dukkanninsu suna da takardar ilimi iri daya da kwarewar aiki da yin aiki iri daya da kuma kwazo daya.

Idan akwai bambanci mai yawa a tsakaninsu, a daya daga cikin dukkanin wadannan abubuwa da na ambata, to hakan zai iya zama dalili a biya ma'aikata albashi daban kuma hakan bai saba wa doka ba.

''Cikakken bayanin aiki da irin duk abin da ya kunsa da albashi dukkaninsu na bukatar a fayyace wa ma'aikaci dalla-dalla,'' in ji Denise Kleinrichert farfesa kan harkokin shugabanci da ka'idar aiki, a kwalejin nazarin kasuwanci ta jami'ar jiha ta San Francisco.

Akwai kwararan dalilai da ma'aikata biyu za su rika samun albashi daban-daban a aiki iri daya.

Watakila an dauke su aiki ne a lokaci daban-daban, daya an dauke shi a lokacin da a ke da saukin samun kwararrun ma'aikata, dayan kuwa an dauke shi ne lokacin da irin wadannan ma'aikatan kwararru suka yi karanci, ko a ke nemansu sosai, abin da zai sa kamfani ya biya shi albashi mai yawa domin ya jawo kwararren ma'aikaci.

Komawa wani kamfani daga wani kai tsaye na iya jawo karin albashi, ko da aiki iri daya ne, wannan zai iya sa albashin wani ma'aikaci ya fi na wani.

To sai dai idan kana zargin akwai bambanci tsakanin albashinka da na wani, inda za ka kai kara kai tsaye, shi ne ofishin kula da harkokin ma'aikata,

''Ma'aikaci daya, ba zai iya magance matsalar nuna bambanci a harkar dauka ko tafiyar da aiki ba, a karan kan shi, shi kadai, amma zai iya sanar da manyan shugabannin gudanarwa (wadanda su ke gaban masu daukar aikin da su ke nuna wariyar ko bambancin albashi), idan sashen kula da harkokin ma'aikata bai magance matsalar ba, ko kuma ta ci gaba, in ji malamar.

Idan sashen kula da harkokin ma'aikata (HR) bai dau mataki a kai ba, kuma kana jin ana nuna maka bambanci, za ka iya kai kara hukumar tabbatar da daidaito a aiki (Equal Employment Opportunity Commission) idan a Amurka ne, ko kuma wata hukuma irin wannan idan a wata kasa ne.

Kleinrichert ta ce ''wadannan hukumomi suna da ikon daukar mataki a kan kamfani ko ma'aikatar da ke nuna wannan bambanci domin gyara.''

Sai dai kuma ka yi hankali, domin duk da cewa abu ne da ya saba wa doka hukuma ko kamfani ya yi ramuwa a kan ma'aikacin da ya kai irin wannan kara, ba lalle ka sake jin dadin zama a wannan wurin aikin ba, idan har ka kai kamfanin kara.

Ko kayi nasara ko ba ka yi nasara ba a korafinka, a karshe kila ka nemi sauya wurin aiki.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Blowing the whistle on the pay gap