Batutuwan da ba a wasa da su a Asiya?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Da muguwar rawa gwamma kin tashi, haka dai Shakespeare ya rubuta tun kafin falken farko ya ci karo da al'adar Sin ta nade tabarmar kunya da hauka. A nahiyar Asiya maganar nan da a kan ce ''kurum ta raba ka da kowa'' ita ce hanyar zama lafiya.

John Krich na da bayani

Maganar da mutum zai yi ya kwana lafiya a kasasahen Turawa na yammacin duniya, ita ce za ta kai shi ta baro a kasashen gabashin duniya (Asia).

Fadin abin da ke zuciyarka ka iya karfafa hadin kai a New York ko Newcastle amma kuma hakan ne zai iya tayar da zaune tsaye a Nanjing ta China.

'Yancin fadin albarkacin baki kamar yadda aka fassara shi a dandalin Hyde Park na Landan ka iya zama furucin cin mutunci a wani dakin taro na Beijin.

A ko da yaushe akwai batutuwa masu muhimmanci da suka danganci siyasa da addini da al'ada wadanda bai kamata baki su taso da su ba, in dai suna son tsira da mutuncinsu.

Duk da haka abu ne mai wuya ka iya fayyace wadannan batutuwa takamaimai.

Yawancin kasashen Asiya ko alama ba su kai yadda a ke ganinsu kamar suna da mutane iri daban-daban (masu al'ada da addinai daban-daban ba).

Ku yi hakuri masu yawan subul da baka da masu katobara. Ga manyan dokoki guda goma na rufe bakin masu furuci da tattaunawar da ka iya bata kawance da yarjejeniya tsakanin kasashen Gabas da Yamma.

1) Ka da ka bari abubuwa su yi kamari.

Idan kana da wani korafi a kan wani sabon abokin aikinka dan Asia, ka yi kokari ka gaya masa ta hanya mai dadi.

Shugaban kungiyar manyan jami'an kamfanoni da hukumomi na Asia a Hong Kong (Asia CEO Forum), Mark Michelson ya ce, ''A Japan na ga inda dangantaka mai muhimmanci ta yi tsami tsakanin wani dan Amurka da jami'in gwamnati, saboda Ba'amurken ya soki jami'in Japan din a fili, inda a bainar jama'a ya ce masa, 'kai ba ka san abin da ka ke fada ba.'''

Ya kara da cewa, ''a ko ina, ba mutumin da zai zo ka kunyata shi; ya fi dacewa ka mutunta mutum. Saboda haka a Asiya idan ka daga muryarka ko ka nuna wa mutum yatsa za ka iya gamuwa da fushin mutum.

2) Ba za ka yi wasa da sunan Ubangiji ba (musamman ma idan ba abin bautarka ba ne).

Ma'ana kada ka sake ka soki abin bautar wani. Wata masaniya kan harkokin abinci Marryam Reshi ta ce, ''a Indiya akwai ra'ayi uku a game da addini; maikarfi wanda ya fi karfi da kuma mafi karfi gaba daya.''

A wasu yankunan Musulmi kamar wasu sassan Malaysia wasu shuwagabannin addini sun ce kare ba shi da tsarki saboda haka taba shi ma zai iya zama laifi.

A don haka, mutumin da ya kirkiro wata da'awa ta cewa 'yan Malaysia Musulmi su rika taba kare ya gamu da tarin barazanar kisa.

3) Ka guji furta kalaman da ke jawo fushi ko ce-ce-ku-ce.

Duk yadda tafinta ya ke da yarinta ko samartakar wani babban jami'i a China, ''furta kamalai a kan harafin ''t'' uku, wato Tibet da Taiwan da Tiananmen zai sa a dauki hakan katsalandan na kasashen waje,'' in ji Mike Chinoy babban jami'i a cibiyar nazarin dangantakar Amurka da China.

Haka kuma, ''kada ka sake ka yaba wa Japan a Korea, ko ka yabi China a Japan,'' kamar yadda Micha Peled darektan fim din China Blue ya rubuta a wata wasikar email. ''A Philippines, kada ka yi wasa da abinci ko Paparoma.'' A Koriya ta kudu, idan kana son zaman lafiya ambaton Koriya ta arewa ba abu ne da za ka yi ba shi ma.'' Yadda babban manajan kamfanin Seoul JW, Marriott Nicholas Tse, ya rubuta a wata wasikar email.

4) Ka kiyaye da manufofi

''Kila zai fi dacewa ka guji furta wata magana a game da nuna bambanci ko fifiko a Singapore,'' in ji Mitchell Farkas, shugaban wani kamfanin fim da ke China mai suna FarFilms.

Darektan cibiyar nazarin cigaba da al'adu da harsuna ta Nusantara ta Kuala Lumpur, A Najib Ariffin ya ce ya tuna, '' wata rana wani Ba'amurke ya yi kalamai na sukan tsarin nuna bambanci tsakanin ainahin 'yan kasar ta Malaysia da sauran 'yan kasar 'yan asalin China da Indiya, tsarin da a ke kira Bumiputra, wanda ya ke a cikin kundin tsarin mulkin kasar, ya manta da cewa ita ma kasarsa Amurka tana da irin wannan tsari na fifita 'yan asali.''

Ya ce, ''wannan ya fusata mutanen da ya ke mu'amulla da su a Malaysian, inda suka yanke duk harkar kasuwancin da su ke yi da shi.''

Wani misalin kuma da mai shirya fim Micha Peled ya bayar, ya ce, ''a Indiya kada ka gaya wa mutane cewa tsarinsu na mayar da wasu mutane ko kabilu 'yan bora (caste) ci baya ne da kuma jahiliyya, ko kuma ka tambaye su me ya sa ba su sasanta da Pakistan ba tun a baya.''

5) Kada ka ci mutunci ko nuna wulakaci

A Thailand, kada ka sake ka yi wasu kalamai da za a iya dauka na sukar sarkin kasar na yanzu, Bhumibol Adulyadej, ko tsohuwar sarautar.

Ka mutunta su a ko da yaushe. ''Idan an tunkare ka da maganarsa kawai ka ce mtum ne mai girma,'' in ji Peter Muening malami a makarantar nazarin harkokin lafiyar jama'a ta jami'ar Columbia ta New York.

Tun kafin juyin mulkin soji na sarauta ana matukar aiwatar da tsauraran dokokin hana cin mutuncin sarakin. Duk abin da aka dauka cin mutunci ne ga sarkin zai bata ran masu masaukinka, 'yar kasar kenan kuma zai iya kai ka ga gidan yari.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Mata sanye da hula mai hoton Sarkin Thailand Bhumibol Adulyadej

6) Ka kame bakinka kan yadda ka ga mutum

Yanayin yadda ado da shigar da mutane su ke yi na iya bambanta sosai.

''Kada ka taba magana kan yadda kaga dan kasuwar Japan ya yi da gashinsa.''

kamar yadda masanin tunanin dan adam Meyumi Ono, ya yi gargadi. Ba a wasa ko dariya a kan sankon mutum ko idan ka ga an turo dan gashin da ba shi da yawa a kai gaba.

Sannan kuma kar ka sake ka yi magana kan yadda ka ji mutum yana wari ko kanshi.''

7) Kada ka dauka wani ya fi wasu idan kana yabawa wani

Abin da ya fi bata ran Tse na Marriott, wanda dan asalin China ne da aka haifa a Biritaniya, shi ne, idan ya ji mutane sun ce, ''kai kana jin Tranci sosai!'.'' Bayan karshenta ma sauran 'yan kasashen Asiyan da ke wurin su ma kila a Amurka ko Biritaniya aka haife su ko kuma sun yi karatu sosai a kasashen.

''Nuna fifiko ga wata al'ada ko wani abu babbar matsala ce,'' in ji Michelson na kungiyar manyan jami'an kamfanoni na Asiya (asia CEO Forum). ''Idan mutane suna magana da 'yan Asiya to kada su rika ayyana abu a kan gaba dayan jama'a.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ka da ka dauki malmalar abinci ta karshe

8) Ka kiyaye da dabi'unka ko al'ada.

Za ka iya gamuwa da fushi kan yin kalmomi na yabo idan ba ka yi su ta yadda suka dace ba.

''Ka tabbata idan kuna hada kwaf din gilashi (na shan lemo ko wani kayan ruwa) naka ya yi kasa da na shugaba ko wanda ya fi ka mukami,'' in ji masanin tunanin dan adam Ono. Wannan haka ya ke, musamman a China.

Haka kuma, ''kada ka ki karbar abinci idan an yi maka tayi,'' in ji Ono

Amma duk da haka ka yi kokari ka nuna juriya a kan wasu nau'ukan abincin, in ji Chinoy wanda ya halarci bukukuwa da yawa.

''Kada ka zama mutum na karshe da zai dauki ragowar (abin ci) kayan abincin da suka rage a tangaran, saboda idan ka kwashe wannan sauran, masu masaukinka ('yan Asiya) z\a su yi Allah-wadai da kai domin ka sa kenan sai sun sa an karo abincin.''

A Koriya da wasu kasashen hakan zai zama kamar turaren wuta na tsinke wanda a ke kunna wa gawa. Amma kuma sidar miya da kara (har ana ji) ana daukar hakan kamar wata yabawa.'' In ji Michelson.

9) Kada ka dauki ''e'' (yes) a matsayin amsa.

Iadan ta kai ta kawo babbar matsala za ta iya kasancewa abin da ka ce maimakon abin da abokan kasuwancinka na Asiya suka bari a dukunkune, ba su fayyace ba.

''Na ji labarin wani babban jami'in kamfani da ya rasa aikinsa saboda ya dauka wani kamfanin Koriya ya amsa ''e'' wato amincewa da a sayar da hannun jari kashi 51 cikin dari, wanda kuma su a wurinsu wannan ''e'' tana nufin sun fahimci maganar,'' in ji Chinoy.

Ya kara da cewa, ''a China idan ka ji an ce ''a'a'' da sauri to yawanci hakan na nufin suna son ka kara (misali ka kara kudi idan ciniki ku ke yi), a hukumance ko kuma ba a hukumance ba.

Amma a Japan da Thailnad da sauran kasashen Asiya da yawa ''a'a'' ba kalma ce da a ke furtata a kasashen ba.

Maimakon fadinta, sai dai a yi jinkiri ko kuma kauce-kauce, an fi daukar hakan a matsayin mutunci amma ba ka ce a'a ba.

Wani lokacin matsalar ka iya kasancewa samun amsa kawai.

''A Thailand , sakatarori da mataimakan shugabannin kamfanoni da makamantansu suna ganin aikinsu su kare shugabanninsu'' in ji dan Biritaniya Ian Semp, wanda darekta ne a wani kamfanin lemo da barasa na Bangkok (Pacific Beer & Beverage Co).

Ya ce, ''duk da cewa ga su ina ganinsu a teburansu, an ce min ba sa ofis.''

10) Banda daga mura a waya.

A Hong Kong inda aka saba magana da karfi a waya, abin da zai iya zama babbar matsa shi ne maganarka ta waya ta damu ta wani ( ka daga murya fiye da muryar sauran na kusa da kai).

Amma kuma a Japan, ''duk wata hira ta waya ana daukarta a matsayin takurawa jama'a da surutu,'' in ji Ono.

Kamar dai magana ta kasuwanci, an fi son yin shiru. ''Turawan kasashen yammacin duniya ko da yaushe suna ganin ba za su iya jure hakan ba,'' in ji Michelson.

Ya kara da cewa, ''amma dai duk yadda ta kasance, abubuwan da aka bari ba a fada ba sun fi abin da aka fada daraja.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Touchy topics to avoid in Asia