Me zai hana gudu ya zama tsira?

Hakkin mallakar hoto getty

Kana jin kamar tafiyar da harkokin rayuwarka na yau da kullum yana kara zama mai wuya da gajiyarwa, duk da dimbin fasahar yau?

Wani abu daya da mutanen da suke aiki da wadanda ba su da aiki suke da shi, shi ne, kusan a ko da yaushe suna cikin aiki, ko da yaushe suna kokarin su kammala tarin ayyukan da ba su da iyaka, kuma a yayin hakan suna wahalar da kansu.

Ko da mutane sun san ainahin abin da suke bukatar yi, yadda abubuwan suke ta kara taruwa kadai, jera su ta yadda za ka yi su daya bayan daya shi kansa ba karamin aiki ba ne, hasali ma kara aiki ne a kan aiki.

Fasaha an samar da ita ne domin ta saukaka rayuwa komai ya tafi daidai cikin sauki, to amma hatta ita kanta, idan ka duba tana kirkirar wasu tarin ayyukan ne na ba gaira ba dalili.

Ka duba tarin lambobin sirrin ko mabudi (password) da za ka haddace na shiga wasu shafuka da sauran abubuwa na fasahar, da wasikun email kusan 500 da kake samu a kullum.

Me ya sa za a ce sai na bude shafin masarrafa ko wani shafin intanet mai amfani da Facebook ko Twitter?

Hatta su kansu abubuwan fasahar da aka yi domin su saukaka maka abubuwa suna ta karuwa.

Mabudin sirri (password) nawa kake bukata ka haddace, kafin ka iya tafiyar da harkokinka na kullum?

Mafitar za ta iya kasancewa kirkirar wani wuri ne da ba ya kunshe da tarin abubuwa, wanda zai iya taimaka mana mu samu natsuwa da saukin al'amura.

Ba abu ne mai wuya ba kamar yadda za a iya dauka. Yawancinmu muna yin abubuwa ne na yau da kullum wadanda ladan shi ne saukin da muke ji na gudanar da su, ko da kuwa jin hakan na dan wani guntun lokaci ne.

Idan kana motsa jiki ko zama ka natsu ba ka komai na dan lokaci za ka san abin da nake nufi.

Masana tunanin dan adam na bayyana hakan da karfi ko ikon natsuwa, wanda a takaice yake nufin, rayuwa da abin da ke gabanka a lokaci ba tare da takura wa kwakwalwarka da abubuwa da yawa ba.

Daukar komai da sauki a rayuwar yau da kullum ba abu ne mai sauki ba, amma dai ba kuma abu ne da ba zai yuwu ba.

Sannan akwai abubuwan da za mu iya yi domin mu saukaka wa kanmu rayuwa.

Ka fara duba hanyoyi masu sauki da za ka gudanar da ayyukanka, a matsayin matakin farko.

Wannan abu ne da zai iya kasancewa mai sauki matuka. Wana abu ne na farko da za ka yi idan kwamfutarka ko wata na'urarka ta kwamfuta ta cije (ta tsaya)? Ka zare wayarta kawai. Kafin na koyi wannan dan karamin darasi wane irin lokaci ne ban bata ba, wajen duba wannan takarda da waccan da tuntumar kwararru masu bayar da dauki, duk domin fitar da ni daga wannan matsala?

Kirkirar wani yanayi ko lokaci na saukaka wa kanka aiki, abu ne mai wuya, da ya dogara ga abin da kake yi, amma dai akwai hanyoyin da za ka iya samun hakan.

Kada ka rika duba wasikunka na email ko da yaushe. Hanya daya ta yin haka ita ce ka rufe shafin samun wasikun naka (outlook). Idan ba haka ba lalle ba ne ka iya jurewa kasa duba wasikun.

Ka kirkiri wani lokaci, da za ka fara da minti 20 har ka kara a gaba zuwa sa'a daya ko sama da haka, wanda zai zama ba ka wani aiki da intanet ko kwamfuta kwata-kwata, ka kaurace mata.

Ba kowa ne zai iya yin wannan ba, amma dai minti 20 abu ne da mafi yawan mutane za su iya fara gwadawa da shi.

Idan ba za ka iya yin wannan ba, matsalarka kadan ce, wato kenan kana da abubuwa da masu yawa a gabanka, kila masu nasaba da yawan son duba wasikun email.

Kuma ma ko da ka rabu da intanet din, ai za a ce wayarka na nan , saboda haka ba ka rabu da intanet din ba baki daya kenan.

To hakan ya nuna ba wai kamar ka kulle kanka a wani wuri ba ne da ba ruwanka da wasu harkoki ba gaba daya , da sunan neman hutu na dan lokaci ba.

Ka rage fuskantar abubuwa da kanka. Manyan jami'ai ko shugabannin wurin aiki, suna takurawa kansu ne, ta yadda za ka ga a ko da yaushe su fuskanci wannan abu ko ko su tafi shawo kan wata matsala nan da can, maimakon gudanar da abubuwa.

Za ka iya saukaka wa kanka wannan ta hanyar kirkirar lokacin hutun natsuwa da waiwaye na minti 15, na kwanakinka.

Wannan lokaci ne da za ka natsu ka yi tunani, na san abu ne da kusan ba a taba ji ba a wannan zamani da duniya ke tafiya ba hutu, sa'o'i 24 a kwana bakwai, muna harkokin ayyukanmu.

Ka tsaya ka yi tunanin abin da za ka iya sauya yadda kake yinsa, yadda za ka inganta shi, ko ma wanda ba lalle sai ka yi shi ba.

Ka rika amfani da lokacin wajen tunkarar abu kafin ya faru, maimakon ka ce sai ya faru ka tunkare shi.

Amfani da moriyar da za ka ci daga wannan dabara ta tsara rayuwarka za ka ji su ne daga tarin saukin da za ka ji ka samu.

Ka yi amfani da kayan aikinka. Ka kaddara cewa za ka iya hada tarin ma'aikatan da za su ba da gudammawarsu, maimakon ka rika yin komai da kanka.

Idan kai shugaba ne a wurin aikin, kila kana da mutanen da suke aiki a karkashinka daman.

Shugabannin da suka fi iya aiki su ne wadanda suka fi iya nada wakilci. Kana daga cikinsu?

Zama shugaba ba abu ne mai sauki ba, amma tsarin nada wakilci abu ne mai sauki. Ka tsara abubuwanka yadda ya kamata kawai. Ka koyar da mutane yadda za su iya tafiyar da ayyuka. Ka dora musu alhakin duk abin da ya faru. Ka horar da su kan aikin.

Za ka san cewa abubuwanka na tafiya daidai, idan ka ji cewa lalle yanzu za ka iya yin wannan dan hutu naka na natsuwa da tunani na minti 15 a kullum ba tare da wata fargaba ba.

Dukkanin wadannan shawarwari suna kunshe da wani abu daya, mai matukar daraja, wadda ta kai duk wata daraja da za ka iya tunani, darajar ita ce, samar da lokaci.

Idan kana da isasshen lokaci za ka iya tafiyar da komai kuma ba tare da wani matsi ko damuwa ba.

Sauki daya ne daga cikin abubuwa na daban, inda karin maganar nan da ake cewa, ''dan hakin da ka rena shi ke tsone ma ido'', yake kunshe da shi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why is simplicity so complicated?