Ko ka san dalilin da za ka tallata jahilcinka?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Daya daga cikin manyan kalubale da jami'ai ko shuwagabanni musamman na kasuwanci a yau suke fama da shi, shi ne cigaban fasaha. Kana son sanin yadda za ka yi maganin matsalar?

Riki kalmar ''ba komai na sani ba.'' In ji Jonathan Zittrain.

Mai rubuta wa BBC sharhi a kan harkokin kasuwanci kuma kwararriya a fannin tafiyar da harkokin kamfanoni, Lucy Marcus, ta hadu da Jonathan Zittrain, farfesa a kan harkokin shari'a da kuma ilimin kwamfuta a jami'ar Harvard ta Amurka a babban taron tattalin arziki na Davos na 2016, inda ta fara tambayarsa yadda kamfanoni za su iya maganin kalubalen zamani na fasaha da ke ci musu tuwo a kwarya. Shawara: Komai ya dogara ne kan tattaunawa.

Tambayar farko: Da yawa daga cikin manyan shugabannin kamfanonin da nake tattaunawa da su , suna cewa daya daga cikin manyan kalubalen da harkokin kasuwancinsu ke fuskanta a yau shi ne na gagarumin sauyin da ake samu na fasaha. Me wannan ke nufi? Me ya kamata harkokin kasuwanci su rika tunani?

Amsa: ''Ina ganin idan kana daga cikin manyan jami'ai ko kuma kai ne shugaban wani kamfani, ( na sayar da nama ko dankali) to fasaha na nan da abubuwa da yawa da za ka karu da su, fiye da wasu 'yan kalmomi da abubuwa na yau da kullum da aka saba haduwa da su (block chain, social media, mobile, cyber security).

Ba shakka muna ganin mutanen da suke son cewa, ''akwai wannan barazana a nan, za a bar ka a baya ko kuma za ka zama mai rauni a harkar kasuwancinka. Abin yi kawai shi ne a kudiri aniya shi ke nan, duk wata matsala za ta iya kaucewa.''

Abu ne mai matukar muhimmanci ga jami'ai da manyan shugabanni su kara shiga cikin harkokin fasaha, ta yadda za su iya sanin amsar da za su bayar idan wani ya fuskance su da wata tambaya, maikacinsu ne ko ba ma'aikacinsu ba ne, abin ya shafi kamfaninsu ko kuma bai shafi kamfaninsu ba, ''wa ya ce ba za mu iya yin wani abin da fasaha ba?''

Da yawa daga cikin muhimman tambayoyin da aka yi ba a amsa su ba gaba daya. Ba wanda za ka rubuta wa takardar banki ta karbar kudi kuma ka dauka cewa kagama da komai.

Tambaya: Me za ka iya koya wa wani na ilimin fasaha kan harkokin kasuwanci, ta yadda zai kware akalla ya gane idan wani abu ba daidai ba ne?

Amsa: Ina ganin mutum ya kasance zai iya amsa tambaya ba tare da wani shayi ba. Sannan kuma ya zama cewa ba ka shakkun za a yi maka kallon jahili a kan abu.

Za ka iya koya wa mutum ya karfafa tsarin tattaunawa tsakanin manyan jami'an kamfani da kuma masu wakiltar kamfanin. Inda za a samu yanayi da mai wakiltar kamfanin ba ya tunanin manufar abin ita ce ya tsira ba tare da wasu tambayoyi ba, tare kuma da kasance wa kowa yana ganin komai daidai yake.

Tambaya: Saboda ba wanda ya san komai?

Amsa: Ina ganin hakan daidai ne. Hatta neman wata dama a inda kamfani ya kasance ba mai daukar kansa, wanda kuma ba a kallonsa a matsayin na fasaha ba, za a iya tambaya, shin akwai wata hanya da wannan kamfani zai iya zama kan gaba wajen samar da fasaha, wanda wannan ba abu ne da kamfani zai ma yi tunanin yi ba (ma'ana mutum ya zama mai buri hatta a kan abin da ba a ma tsammanin zai iya yi).

Tambaya: To muhimmin abu shi ne, idan kana kokarin samun wani bayani, ya kasance ka lakanci yadda za ka yi tambaya yadda ya dace ka kuma fahimci amsar.

Wato kenan kada mutum ya dauka cewa akwai wata amsa guda daya tilo da za ta gamsar da dukkanin wadannan batutuwa?

Amsa: Kwarai kuwa. Wajibi ne ka zama mutumin da zai nuna rashin sani ko jahilcinsa da abu a fili. Kuma ka zama mai yarda da amsa, kuma ka karfafa amsoshin da ba su kammala ba, wato idan ka ji an kamo hanyar bayar da wata amsa aka toge sai ka taimaka wajen karasa ta.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. This is why you should 'advertise your ignorance'