Akwai shawarar da ta fi ta mahaifiya?

Hakkin mallakar hoto alamy

Na san ka taba ji. Watakila daga bakin mahaifiyarka, amma dai yanzu ga sheda kila ko kana bukata, shawarar uwa ita ce ta fi kowacce shawara. Ko kun yarda da haka?

Mun garzaya sashenmu na tambaya da amsa, domin samun shawarwari na gari daga uwayen da ke da kwarewa wadanda kuma suka dade suna shan wahala.

'Ba kai kadai ba ne'

Antone Johnson wanda sabon lauya ne, ya bayyana irin shawarar da mahaifiyarsa ta ba shi game da rayuwa, inda ta ce masa, '' kada ka dauka kai kadai ne a duniyar nan, dauki abin da za ka iya ka shiga fafutuka.''

Mahaifiyar Johnson ta ba shi wannan shawara ne cewa, ya san da cewa rayuwar sauran mutane tana da muhimmanci a wurinsu kamar yadda shi ma yake ji da rayuwarsa.

Wannan shawara da ya gabatar tana da amfani musamman ga yara a lokacin da suke tasowa, domin sanin muhimmancin abokanansu da sauran jama'a, domin amfanin zaman tare.

Lauyan ya kara da cewa, ''ba wanda yake zaune kawai yake nazarin rayuwarka domin ya bayyana ta daki-daki,'' ya ce, ''kowa da ka gani sha'anin gabansa ya ishe shi, kan ya mayar da hankalinsa kan wani abin kunyarka.''

Ka gano wa kanka

Ita kuwa Shannon Holman ta rubuta cewa, saboda ta girma ne kafin zuwan intanet, maganar da iyayenta shawarar da ta san iyayenta sun fi ba ta a lokacin ita ce, ''je ki ki binciki ma'anarta.'

Ta ce, iyayenta sun yi sa'a suna da kudin sayen kundin littattafan bayanai (encyclopaedia). Kuma tana jin ta dace cewa,'' duniya tana da girma sosai ta yadda suke jin suna da wuri a cikinta, kuma girmanta ya kai girma ta yadda ba za mu ji mun san komai a game da ita ba.''

Me kirki ko maras kirki? Yadda za ka gane na bogi

Stephanie Vardavas ta ce, a lokacin da take 'yar karamar yarinya, mahaifiyarta ta ba ta shawara cewa, idan tana son ta gane ko mutum yana da kirki ko ba shi da shi, ta lura da yadda yake daukar kananan ma'aikatan kanti ko otal da makamantansu, wadanda ba su da wani karfin kare kansu.

Vardavas ta ce, ''(mahaifiyata) ta yi gaskiya dari bisa dari, kuma ban manta da wannan magana tata ba. Tana da amfani wajen sanin yadda mutane suke.''

Kafewa cewa kai a kan gaskiya kake

Ken Miyamoto ya ce duk da cewa akwai kauna da son juna a tsakanin iyalansu, to amma duk da haka akwai lokacin da suke samun bambancin ra'ayi wanda ke sa su musu mai zafi, abin da ke sa har mahaifiyarsu ta shiga tsakani.

Ya ce, '' a irin wannan musu ne a 'yan shekarun baya, tsakanin mahaifina da dan uwana da ni, mahaifiyata ta ce min, 'Da zama daidai (mai gaskiya) da dorewar dangantaka wanne ka fi so?' ''

Saboda haka a yanzu duk lokacin da tura ta kai bango, sai ya tuna wannan magana '' saboda ba ta yadda dangantaka za ta dore idan har kullum za ka kafe ka ce sai an yarda da ra'ayinka a rayuwa.''

Aure, a takaice

Michelle Roses ta ce gab da za a daura mata aure, sai uwar mijinta ta ce mata,'' Michelle, idan namiji ba zai iya dafa wa kansa abinci ba, to ya mutu da yunwa.''

Mun yarda sosai da haka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Here's proof that mum really did know best