Al'adar cin abinci tare ta fara yaduwa a duniya

Hakkin mallakar hoto Getty

Fika wata al'ada ce ta mutanen kasar Sweden, inda jama'a sukan hadu wuri daya su ci, su sha, su tattauna da juna a wurin aiki. A yanzu wannan al'ada ta fara bazuwa a duniya, kamar yadda Elizabeth Hotson ta gano.

A kasar Sweden dole ne yin wannan al'ada wadda ma'aikata za su zauna tare su ci kayan kwalan da makulashe da shan gahawa a wasu lokuta da suke bakin aiki.

Ita Fika ta zama kamar wani bangare na aikin mutum wanda dole ya yi shi, kamar yadda ba zai iya raba kansa da rubuta wasikar email ba da sauran abubuwa na ofis.

Matts Johansson, wanda ya kafa shagon shan gahawa na Da Matteo a Gothenburg, ya ce., ''abu ne da ya samu gindin zama sosai a al'adarmu''

Ya ce, '' yawancin 'yan Sweden suna yin wannan zama na ciyayya sau da dama a rana daya, walau a ranakun aiki ne ko kuma a ranakun karshen mako ne.

Abu ne kawai na zama da mutane ku ci kayan kwalan da makulashe da aka yi a gida da kuma shan gahawa mai dadi. Kamar zuwa kulob ne a wasu kasashen.''

Kamfanonin Sweden da yawa suna da wannan tsari da ma'aikaci dole ya je ya yi wannan zama da sauran ma'aikata, inda ake ba su gahawa kyauta. To duka wannan hutun da suke yi a fakaice yana kara nagartar aiki?

Hakkin mallakar hoto FlickrAndreas IvarssonCC BY 2.0
Image caption Kayan kwalan da makulashe na Fika

Nazarin da aka yi na nagartar aiki a kasashe 38, a sheakara ta 2014, ya nuna cewa Sweden ce ta 11 yayin da makwabciyarta Norway take ta biyu, a bayan Luxembourg wadda ita ce kasar duniya ta daya da aka fi samun nagartar aiki.

Ma'aikatan Amurka su ne na hudu a duniya, yayin da Faransa, kasar da ake dadewa ana hutun cin abincin rana take matsayi na bakwai, nesa da Japan ta 20 da kuma Korea ta 30, kasashe biyu da ma'aikata ke dadewa suna aiki a duk ranar aiki.

Al'adar zaman ciyayyar ta Sweden, Fika, tana da matukar muhimmanci a kasar, domin ba wai ta tsaya ba ne ga shan kofi da cin abinci, tare, lokaci ne da a kan tattauna da abokan aiki, a kuma lalubo hanyar samun wata mafita da ta fi dacewa a kan wata matsala. A irin wannan zama ne ake samun wasu dabaru ko shawarar da ta fi dacewa ta yin wani abu.

Andreas Astrom na majalisar kasuwanci ta Stockholm shi ma ya yarda da hakan, yana mai cewa, '' tsarin gudanarwa na Sweden ya bambanta da na yawancin kasashe. Tsari ne na ba wanda ya fi wani a tsakanin ma'aikata.''

Ya ce, ''idan kana da tsarin da ba wanda ya fi wani, za ka iya sauraren kowa, kuma ta hanyar wannan zama na ciyayya, Fika, ana samun damar tattaunawa tsakanin ma'aikata da da hukumar ma'aikatar. Wannan hanya ce mai kyau ta sanin ra'ayin kowa a kan yadda ya kamata a tafiyar da kamfani.''

A kwanan nan wannan al'ada ta fara bazuwa a duniya, inda jama'ar New York da birnin Landan da Sydney da sauran birane za ka ga ma'aikata sun fice daga ofis sun nufi shagon sayar da gahawa, inda sukan kwashe minti 15 akalla domin yin Fika.

Lars Akerlund ya kafa shagunan da ake yin wannan al'ada ta Fika. Ya koma birnin New York ne daga Sweden a 2001, inda ya bude shagonsa na farko, wanda ya sanya wa suna FIKA a kusa da babbar tashar birnin a 2006. A yanzu dai yana da shaguna 17 na Fika, zai kuma bude wasu biyu a nan gaba.

Ba kai wa mutanen New York gahawa ba ne kawai burinsa, fatansa shi ne ya kai musu wani sabon tsarin rayuwa.

Ya ce, ''manufar samar da Fika, ita ce, domin mutane su zauna su more gahawarsu da dan abin ci, su tattauna ko da na minti goma ne.''

Akerlund ya kara da cewa, ''a New York mutane sun saba da su shiga shago su sayi gahawa ko wani abin ci, su fito suna tafiya suna ci a kan hanyarsu ta zuwa aiki ko wani wuri, a kan haka ne na da cewa zan iya kawo musu wani abu mai kyau da zai sauya yadda mutane suke abubuwansu, su tsaya su dan shakata.''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu kenan suna ciyayya a Landan, a lokacin yawan shakatawa, kamar yadda ake yin Fika

Tsarin na Fika, ya samu karbuwa a Manhattan ma, kamar yadda a Australia ma aka rungume shi, yayin da a yankin Walthamstow da ke Landan wani shagon abinci na 'yan Sweden, Baygga Bo shi ma ya kwaikwayi tsarin.

Al'adar Fika

A tsarin ciyayyar ta Fika ana hada 'yan kayan ciye-ciye ne (cincin) yin gida, iri daban-daban har guda bakwai da kuma gahawa, inda za ku zauna ana ci ana tattaunawa kan wani abu da ya shafi aiki ko rayuwa.

Idan kaan son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Is this the sweet secret to Swedish success?