Ka san kyautar kudin da ke jawo fushi a China?

Hakkin mallakar hoto AFP

Bikin sabuwar shekarar miladiyya da ake yi a China ya hada da bayar da kyautar wani fakiti ja da kudi a ciki, to amma ka kiyaye kada ka yi wata katobara idan za ka bayar da kyautar. Katobarar? Kudi masu yawan lamba mara ko lamba hudu.

Ga bayanin Carol Peng

Kowace shekara, daruruwan miliyoyin jama'a a fadin duniya suna bikin sabuwar shekara, inda a wani lokacin suke tafiya zuwa wasu kasashe masu nisa domin shakatawa da iyalai da abokansu.

A kasar Sin (China) wannan gagarumin bulaguro na iya haddasa babbar matsala, domin misali mutane dubu 100 ne dusar kankara ta sa suka yi curko-curko, ba ta yi a wata tashar jirgin kasa.

Wannan biki na sabuwar shekara zai iya jawo wata matsalar ta daban ga masu kamfanoni da ma'aikatu, wadanda suke son su ma a dama da su a bikin.

Al'ada ce a kasar ta Sin a rika bayar da wata kyauta ta musamman wadda ake kira 'hongbao' da ke nufin jan fakiti, cike da kudi, ga iyalai da abokai da abokan aiki da ma'aikatanka a wannan lokaci na shekara, amma kafin ka yi wannan al'ada wajibi ne ka san yadda dokarta take, idan ba haka ba maimakon a yi murna da kai sai ka gamu da fishin wanda ka ba kyautar.

Hakkin mallakar hoto alamy

A lokacin wannan biki na sabuwar shekara kada ka sake kudin da za ka bayar na kyauta a cikin wannan fakiti mai launin ja, yawansu ya zama mara (misali dala dubu uku ko biyar ko bakwai ko tara da sauransu).

Domin a al'adar Sin, a wurin jana'iza ne kawai ake bayar da kudi haka, wanda kuma ana danganta hakan da rashin sa'a a lokacin biki.

Saboda haka ka bayar da kudin da yawansu yake da lamba wadda za a iya raba ta bibbiyu ba tare da ragowa ba (kishiyar mara), domin hakan kuma ana daukarsa a matsayin karin alheri.

Sannan ka guji amfani da lamba hudu, domin kalmar hudu da harshen mutanen Sin ana fadenta ne da 'si', wadda sautinta ya yi kama da na kalmar mutuwa, kuma ita ma ana daukarta a matsayin bacin rana ko rashin sa'a.

Shi wannan dan kunshin fakiti da ake kira 'hongbao wanda ke nufin jan fakiti, ana yinsa da launin ja din ne saboda an dauki launin ja a al'adar kasar China a matsayin sa'a.

Amma a baya-bayan nan an dauki launin ruwan hoda da hadin ja da shudi (magenta da Ingilishi) su ma da muhimmanci, suna samun farin jini.

Kuma ka lura kada ka yi amfani da launin fari ko baki, domin ana danganta su da mutuwa da makoki ne. Sannan ba a bayar da kyautar da tsoffin takardun kudi, saboda ana daukar hakan a matsayin rashin mutuntawa.

Abin da ake so shi ne, ka yi amfani da sabbin takardun kudin da suka fito daga banki, mutane ba su yi amfani da su ba.

Mutane suna son sabbin takardun kudi sosai, abin da ya sa har bankuna ba sa iya biyan bukatun jama'a, inda misali hukumar kudin Singapore tana buga karin takardar dala biyu har miliyan 100 a duk lokacin wani biki na shekara.

Tana yin hakan ne domin biya wa jama'a bukatarsu ta sabbin takardun kudi, kuma duk da haka gwamnati tana wani kamfe tun 2013, na wayar wa da mutane kai su dauki duk takardar kudin da ke da kyau kamar sabuwa domin rage mata matsin da take sha na buga sabbin kudin.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. An inside guide to how to give money at Lunar New Year