Yadda ma'aikata ke zaben abokan aure

Hakkin mallakar hoto istock

Ka yi watsi da furanni da alawar chakuleti, ka nemi sanin wadda za ka aura ta hanyar yanayin aikinta domin samun soyayyar da za ta dore.

Alina Dizik ta yi mana nazari kan wannan

A duk lokacin da za ka zabi matar da za ka aura, wadda kake son ku yi zama mai dorewa cikin soyayya, to ka koyi yadda ya kamata ka rika kashe kudi kuma ka tabbatar ka zabi wadda aikinta ya zo dace da naka (ba wai iri daya ba).

Masana tunanin dan adam suna bayar da shawara ga wadanda ke son bunkasa soyayyarsu, su lura su tabbatar da yadda aikinsu da yanayin kashe kudinsu za su yi tasiri a kan zamantakewarsu ta soyayya (aure).

Duk da cewa ma'aurata sun san kudi shi ne yawanci tushen musu ko sabani a tsakani, amma duk da haka wani lokaci matsalar kan shammace su idan aka yi maganar zaben aboki ko abokiyar aure ta fannin dabi'ar kashe kudi da kuma irin aikin da take yi.

Hakkin mallakar hoto alamy

Shawarar da ka yanke a kan abubuwa biyu manya na rayuwarka za su iya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka maka ka gina kyakkyawara rayuwar aure.

''A wani lokacin cin amanar abokin zama a fannin kudi ka iya kasancewa kamar cin amana ta fannin aure,'' in ji Fran Davis, masanin tunanin dan adam kuma mai ba da shawara kan aikin da mutum zai zaba, wanda ke aiki da jami'ar Havard.

Ga wasu sabbin dabaru guda biyar da za ka iya amfani da su ta yadda aikinka da kashe kudinka za su taimaka wajen bunkasa zamantakewarka ta soyayya:

Gu ji auren wadda kuke aiki iri daya

ZA ka ga neman wadda kuke aiki iri daya kamar abu ne da ya dace. Domin kila ka ce ai sai ku rika tattaunawa a kan harkar aikinku, ta yadda za ku kari juna ma

Hakkin mallakar hoto alamy

Wannan yana da kyau a farkon soyayyarku, to amma idan tafiya ta yi tafiya, can gaba abubuwa za su iya baci.

Ma'auratan da suke aiki iri daya, ko da ba sa gasa da juna kai tsaye a wurin aiki, za su iya samun sabani saboda ra'ayinsu zai iya bambanta a lokacin shakatawarsu.

Lauyoyi da ma'aikatan gona da kuma masu aikin a fannin ilimi (malamai da sauransu) ana ganin za su fi auren mata ko maza iri daya, ma'ana wadanda ke wadannan ayyuka, wadanda suke aure kusan iri daya ne (ba wai lauya ya auri lau ba, ko malami ya auri malama ba, ma'ana irin matar da lauya zai aura kusan irinta malami zai aura).

Su kuwa masu aiki a fannin kudi da ma'adanai da kamfanonin gine-gine ba lalle ba ne matansu su kasance kusan iri daya ba, kamar yadda wani bincike da 'priceonomonics' wani kamfani da ke tattara bayanai a Amurka ya bayyana ba.

Ma'auratan da suke aiki iri daya za su iya samun matsala wajen raba lokacin aikinsu, in ji Gail Kinman farfesa a fannin ilimin tunanin dan adam ta bangaren yadda aiki ke shafar lafiya, a jami'ar Bedfordshire, wanda ya gudanar da bincike kan ma'aurata masu aiki iri daya.

Ya ce, ''aikin zai iya zama kashin bayan auren nasu'' ta ydaa zaikankane duk wata tattaunawa da hira tasu,'' in ji Kinman.

Ka za bi wadda aikinku ya saba amma zai taimaka wa na juna;

A 'yan shekarun da suka gabata masu bincike sun fara duba ayyukan da suka fi dacewa da juna. Misali wadanda suke fannin aikin tallace-tallace yawanci sun fi auratayya da mawaka, yayin da 'yan sanda suke kulla alaka da ma'aikatan banki kamar yadda wani bincike da aka yi kan mutane 450,000 ya nuna (The Grade ne suka yi binciken).

Shafin intanet na hada masu neman aure ko soyayya, na eHarmony.com ya gano cewa mutanen da suke wasu ayyukan sun fi neman masu wasu ayyukan a wasu fannonin na musamman.

Misali daga irin abubuwan da shafin ya gano sun hada da yadda lauyoyi maza ke son mata masu aikin zayyana gine-gine (architects), mata lauyoyi kuwa suna son matukan jirgin sama maza, maza masu bincike su kuwa suna son mata masana ilimin harhada magunguna. Akwai kuma maza kadan shugabannin kamfanoni da ke son takwarorinsu mata masu irin wannan aiki.

Malaman addini da masu yin tabaran likita da injiniyoyi su ne suka fi zama da aurensu ko ma wane irin aiki matasu ko mijinsu yake yi, misali aikinsu daya ne ko ba daya ba ne, kamar yadda Michael Aamodt, tsohon farfesa a jami'ar Radford ya bayyana bayan da ya yi amfani da bayanai 2000 na Amurka.

Ka yi shiri kafin aiki

Dukkaninmu muna jin yadda ake samun korafi a kan maza ko matan da suke bauta wa aikinsu sosai. Za ki iya aiki akai akai na wasu lokuta da wani aiki kan taso, amma irin haka ka iya shafar rayuwarki idan wannan lokacin ko sa'o'in suka zo ne kawai ba da tsammani ba.

Rashin tabbas a lokacin aikinka ko aikinki zai iya shafar zamantakewar aurenki. Saboda haka kamata ya yi ki duba aikin da za ki iya dawowa gida a lokacin da ya dace, maimakon wanda zai rika sa kina barin gida ba shiri, ko kuma wanda zai sa ki rika dawowa gida da tsakar dare.

Aikin da zai sa ka ko ki rika sauya tsarte-tsaren ayyukan gidanki ba zato ba tsammani zai matukar bata ran matarka ko mijinki in ji Davis.

Wannan yanayin aiki zai iya sa mijinki ya dauka aikinki shi ne gaba da komai a wurinki. Ma'aikatan abnki ko kamfanoni na harkokin kwararru misali inshora da ko kudade da makamantansu za su iya jin suna gamu da matsala wajen yin wani tsari ga ba a kan aikinsu.

Ma'ana duk abin da suka yi na wani tsari game da aikinsu akwai abin da zai iya tasowa lokaci daya ya wargaza wannan tsari ko shiri.

Domin tabbatar da dorewar auren ba tare da wata babbar matsala ba sosai, Davis ta bayar da shawara ga ma'aurata da suka rika yi wa junansu bayani akai akai da zarar wani abu na aiki ya taso wanda zai iya haddasa sabani a zamantakewar, tare kuma da saurin daukar matakin sake tsarin abin da ma'auratan suka shirya yi.

A guji bikin kece raini

Idan ana son aure ya dore cikin yalwa da farin ciki to a guji bannatar da dukiya fiye da kima, in ji Andrew Francis-Tan farfesa a jami'ar Emory a Atlanta wanda ya gudanar da bincike a kan kudaden da ake kashewa a lokaci aure da kuma lokacin da auren ke mutuwa.

Masu binciken sun yi nazari a kan ma'aurata 3,000 suka gano cewa wadanda suka fi kashe kudi a lokacin bikinsu aurensu bai dade ba kamar na wadanda ba su kashe kudi sosai ba.

Babu tabbas ko cewa kashe makudan kudaden shi ne sanadin mutuwar auren, ko kuma dai hakan na da nasaba da mutuwar auren.

A Amurka wani binjike da aka yi kan mata 1,000 da aka yi wa baiko an ga cewa kashi 32 cikin dari sun shiga matsalar bashi bayan an yi auren, kamar yadda shafin intanet na TheKnot ya nuna.

A kasashen Malaysia da Indiya da ke nahiyar Asia misali, abu ne da aka saba gani iyalai su fada cikin bashi bayan sun yi wani gagarumin biki.

Domin kauce wa irin haka, ''kamata ya yi iyalan da za su yi aure su rage yawan kudin da za su kashe daidai da abin da ya kamata,'' in ji Francis- Tan.

Samu maras kashe kudi da yawa kamarka.

Samun matar da ba ta kashe kudi ko cin bashi kamarka yana da muhimmanci sosai fiye da yadda kake tsammani. Wani bincike da aka yi daga bayanan da aka tattara daga baitul-malin Amurka ya nuna cewa ma'auratan da yanayin kashe kudinsu ya zao daya sun fi jin dadin zaman aure.

A daya hannun kuma ma'auratan da aka samu sabani a yanayin kashe kudinsu, aurensu ya fi saurin mutuwa kamar yadda binciken ya nuna.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why police are drawn to bankers and teachers marry teachers