An taɓa ma tambayar ɗaukar aiki ta ba-zata?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Yawancinmu an taba yi mana tambayar ba-zata, mai ban haushi ko ta ban mamaki a wani lokaci, to amma ya za ka yi idan a lokacin ganawar daukanka aiki ne aka yi maka tambayar?

Tambayoyin daukar aiki daman ana tsara su ne domin a fitar da wanda bai cancanta da aikin ba, kuma akwai tambayoyin da za a yi maka na ba-zata, daga masu ban mamaki da kuma masu ban dariya.

BBC ta nufi sashen tambaya da amsa na masu mu'amulla da shafinta na intanet domin jin irin tambayoyin aiki na daban da aka taba yi musu.

Ga wasu daga cikin irin wadannan tambayoyi da aka yi wa wani Adam Newman, wanda ke cike da mamaki, duka a lokacin daukarsa wani aiki, ya ce, ''an tambaye ni, 'Ta yaya za ka iya boye gawa?', 'Ta yaya za ka iya yi wa makaho wajen adana barkono a dakin girki?' da kuma 'mene ne wuri ne ya fi burge ka a fim din South Park?'

Wani jami'in kamfanin yin na'urorin wasannin kwamfuta, Keith Boesky ya rubuto cewa wani babban jami'i ya yi masa tambaya a lokacin da za a dauke shi aiki a wani babban kamfanin lauyoyi, da cewa, 'idan da za ka zama wani kayan lambu, me za ka so ka zama?'

Somya Tiwari ta ce an tambaye ta, 'mene ne ra'ayinki a kan tufafin ado?', wanda wannan tambaya ce mai kyau idan za a dauki mutum aikin masana'antar tufafi, amma, (ta ce) ''Ni a fannin aikin kirkiro manhajar kwamfuta na kware. Kuma na nemi aikin tsara shirye-shiryen kwamfuta ne a wurin.'

Ga wasu kuwa tantacewar ta fara ne tun daga dakin jira na baki( na inda suka je neman aikin). Bayan ya jira wanda zai yi masa tambayoyin kusan sa'a daya, bai zo ba, an tambayi Fernando Gutierrez, ' Za ka iya jira na wani minti 15?' sai ya ce a'a, akwai jirgin da zai hau.

Ya ce, ''Sakatariyar mutumin ce ta zo ta yi min wannan tambaya, kuma ta yi matukar mamaki da ta ga na yi tafiyata kawai,'' Gtierrez ya rubuta cewa. Shugaban nata daman ya yi kaurin suna wajen rashin raga wa ma'aikata, saboda mutane ba sa iya kalubalantar sa. Ina tsammanin yana son daukar wanda ba ya jin tsoronsa ne saboda daga baya ya kirawo ni ya ba ni aikin.''

Akwai kuma tambayoyin da za su girgiza ka.

Dianne Felder ta ce, ''Da dadewa, wanda ya fara yi min tambayar daukana aiki bayan na kammala babbar makaranta, ya tambaye ni wane irin maganin tsarin iyali nake amfani da shi.'' Ta ce ya yi min bayani cewa kamfanin ba ya son ya bata lokaci da kudi ya horar da wata 'idan za a wayi gari kawai a ga ta dauki ciki.' Felder ta ce: Sai kawai na rasa abin da zan ce. Kana jin wani zai yi maka wannan tambaya a yau?''

Lauyan kare wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka, Philip Rosmarin, ya rubuta cewa a lokacin da yake aiki a wani kamfanin tallace-tallace, yana yi wa kananan ma'aikata tambayoyi domin daukarsu aiki, ya rataye wani babban hoton Adolf Hitler a bayan teburinsa a sama da kansa, ta yadda duk wanda zai tantance sai ya ga hoton.

Roman ya rubuta cewa, ''Mun dauki wata mata (daga cikin mutanen) aikin,, domin tana da karfin halin da har ta tambaye mu dalilin da ya sa muka makala wannan hoto a nan..''

A wurin wasu ita tantancewar daukar aiki tana daukar wata siga ne daban ma da inda ake tsammani. Wata babbar jami'ar wani kamfani ta tambayi masanin kimiyya Nitin Gupta, lokacin da take yi masa tambaya domin daukarsa aiki a kamfanin, '' Idan ban dauke ka wannan aikin ba za ka yi mu'amulla ta kut da kut da ni?''

Gupta ya fahimci cewa ka'idar aikin kamfani ita ce ba zai yi mu'amulla ta kut da kut da ita ba idan an dauke shi aiki. Sai ya zabe ta a maimakon aikin.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa na. The most bizarre job interview questions