Ka san amfanin ƙaryar arziki?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Mawaƙi 50 Cent ya ce shi kam ya yi rayuwar ƙaryar arziki. To kai me zai hana ka gwadawa? Ko ba komai za ka samu cikakken ilimin yadda rayuwa da kayan aro take.

Ga nazarin Mark Johanson

Ka duba shafin Instagram na 50 Cent za ka ga tarin hotunansa na yadda nake nuna alamun facaka da dukiya ta fitar hankali.

Akwai inda mawakin wanda ainahin sunansa Curtis James Jackson III, ya ma kasa ganin kafafunsa saboda sun nutse a cikin takardun dala 100. Akwai kuma wani hoton wanda ke nuna firjinsa cike da takardun dala.

Wani hoton mafi rikitarwa kuwa shi ne, wanda ya jera abin da ya kira kudin cin abincinsa na rana, inda ya jejjera takardun dala 100, ya rubuta kalmar ya talauce da Ingilishi wato ''Broke''.

Wannan hoton na karshe shi ne ya fi ba da bayani kan facakar da ake ganin mawakin na yi da dukiya. A watan Yuli na 2015 ne mawakin ya gabatar wa kotu cewa ya talauce, inda ya bayyana cewa ana binsa bashin tsakanin dala miliyan 10 da miliyan 50, kamar yadda takardun kotu suka nuna.

To amma a lokacin da mai shari'a a Connecticut, ta aika wa mawakin mai shekara 40 takardar gayyata kan karar da masu binsa bashi suka shigar gabanta a watan Fabrairu, sai ta ce ita ta kasa fahimtar yadda za a ce mutumin da ya bayyana a gabanta shi ne a hotunan nan na Instagram

Hakkin mallakar hoto istragram 50 cent

Jaridar New York Times, ta ce masu binsa bashin ne suka nuna wa mai shari'ar shafinsa na Instagram. Da mai shari'ar ta nemi mawakin ya yi bayani kan hotunan sai ya bayar da amsar da ba a taba tsammani ba a takardar da ya rubuta wa kotun.

Tarin kudaden da kuke gani na daukar hankali ne ba wani abu ba. ''Don kawai an dauki hotona a kusa da wata mota ko a cikin motar, ko na sa wasu kaya, ko na rike wani abu, ko ina zaune a kusa da wani abu da ake gani kamar tarin kudi ne, ko kuma ina tallata wasu sarkoki da zobuna masu tsada, hakan ba yana nufin duk abin da yake hoton nan nawa ne ba.''

Kullum mutane suna rayuwa ta kayan aro ko haya wadda ta fi karfin samunsu ba domin komai ba sai kawai don su nuna su wasu ne.

Da wuya a ce mawakin shi kadai ne ya taba daga matsayinsa a wurin jama'a ba da dukiyar aro. Abu ne da aka sani a Hollywood cewa yawncin kayan da fitattun mutane ko 'yan fim suke sawa na haya ne ko kuma kamfani ne ya ba su aro, hatta su kansu motocin kece-ranin da suke hawa galibi haya ake ba su.

Ba fitattun mutane ne kadai suke wannan dabi'a ba, a yanzu mutane da yawa suna rayuwa da kayan aro ko na haya domin rayuwa ta karya, su nuna cewa su wasu mutane ne masu wani matsayi.

Kwararriya kan kwalliya da fitr mutum Marian Rothschild, marubuciyar littafin Look Good Now And Always, ta ce yin 'yan wasu sauye-sauye kanana domin ka nuna kai me hali ne ko wani me iko zai iya zama mai amfani a can gaba ga wanda yake kwarrare (ma'ikaci). Ka dauka kamar kana zuba jari ne domin tallata kayanka a nan gaba.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Rayuwar ƙaryar arziƙi

Ta ce, ''Yanzu mutane sun fahamci cewa suna bukatar su nuna kansu kan abin da suke gani za su iya zama, misali inda nake son zuwa, da yadda nake son rayuwata ta zama. Saboda haka bari in sayi wannan agogon Rolex din, ko in dauki hayar wannan motar mai tsada, ko in sayo wasu kayan sawa masu dan-karen tsada.''

Ta kara da cewa, ''Kamar dai irin abin nan ne da dawisu ke yi ya baza jelarsa, yana cewa, 'a kalle ni.' ''

Wani bincike da aka yi kwanan nan (Office Team) ya gano cewa kashi 80 cikin dari na manyan jami'ai suna daukar tufafi da muhimmancin gaske, idn suna duba yuwuwar kara wa ma'aikaci girma.

Haka kuma wani bincike irin wannan, wanda aka yi a jami'ar Yonsei ta Korea, ya gano cewa mutanen da ake ganawa da su domin daukarsu aiki, wadanda suka sanya fitattun tufafi masu tsada, an fi ba su fifiko a kan wadanda suka sanya kaya masu araha, sannan kuma sun ma fi samun albashi me yawa.

Binciken ya nuna cewa masu neman aikin da suka saya kaya masu tsada, kamar suna nunawa cewa za su iya sayen kaya masu tsada ne, saboda haka ana musu kallon manya a tsarin jari-hujja.

Carol Megehee, daya daga cikin wadanda suka rubuta rahoton, wadda farfesa ce a jami'ar Coastal Carolina a Amurka, talokaci da kuma yadda ka sanya fitattun kaya masu tsadana iya yin tasiri sosai a kan ra'ayin wadanda kake son su gani. Sai dai ba lalle ba ne a ko da yaushe ya zama mai amfani ba.

Malamar jami'ar ta ce, ''Idan ke mace ce za ki je wajen tantance daukar ma'aikata, inda mace ce, ke aikin ganawar, to ba zai dace ba ki yi kwalliya da kaya masu tsada sosai, domin hakan zai iya cutar da ke.'' Meghee ta nuna yadda kyashi tsakanin mata zai iya tasowa a wannan yanayi.

Julie Fisk ta yi shekara 25 a matsayin mai gabatar da shiri a rediyo lokacin da aka sallamet daga aiki a 2014, kuma ta yi tunanin zama mai aikin fashin baki a kan fina-finai.

To wannan sabon aikin da take son yi na bukatar ta bayyana a tashoshin talabijin biyu sannan kuma ta bayyana ga jama'a a garinta Dallas, da ke Texas. Wannan ya kunshi halartar taruka inda za ta tattauna ko yi wa fitattun 'yan fim da daraktoci tambayoyi.

Saboda bukatar samun tufafi masu tsada sai ta nufi wani kamfani mai suna Rent The Runway, wanda ya ke ba wa mutane hayar tufafi masu tsada a kan wani dan kudi maras yawa idan ka kwatanta d kudin sayensu.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana iya ba ka hayar kaya cikin kwabet gaba ɗaya

Wannan tsari dai ya biya mata bukata, har ana ta gayyatarta wurare daban-daban. A karshe dai har ta kai ta tsaya da kafarta , har ta yi hadin guiwa da kananan kamfanoni a yankin Dallas, wadanda za su ba ta aron tufafi da sauran kayan ado ta yi amfani da su, ita kuma ta tallanta kamfanonin.

Fisk ta ce, ''Ko da mai daukar aikin ko kuma mutumin da kake son ya san ka sa kaya masu tsada bai kula ba, yadda kai za ka ji a jikinka ma ka sa kayan wani abu ne na alfahari.

Yanzu akwai kamfanoni da yawa irin su Rent Way masu bayar da hayar kaya masu tsada, kamar su Girl Meets Dress a Biritaniya da Yeechoo a Hong Kong.

Saura kamar Eleven James da ke Amurka, wanda yake bayar da hayar agoguna masu tsada, idan ka yi rijista da shi ta shekara, su ke shirin fadada aikinsu har zuwa wasu kasashe.

LeTote da Gwynnie Bee su kuwa suna aika wa da mutum akwatin kaya ne gaba daya a matsayn haya domin ya rika amfani da su, idan ya yi rijista da su ta wata-wata.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Bayan hayar motoci yanzu har kananan jiragen sama na alfarma ma ana ba da hayarsu

Bayan kamfanoni masu bayar da hayar motoci masu tsada, akwai kuma jakunkunan da kayan kawa na mata da masu bayar da hayar jiragen sama na alfarma kamar su Jumpjet da NetJets.

Ba shakka idan mutum yana rayuwa irin ta karyar arziki, reshe zai iya juyewa da mujiya wta rana. Saboda haka Rothschild ke ganin, idan har kana son a dauke ka a matsayin wanda ya san ya kamata, mai gaskiya, wayayye kuma kwararre, to zai fi kyau ya tsaya iya matsayinsa da abubuwan da yake son a san shi da su.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The surprising benefits of living beyond your means