Mecece illar soyayya tsakanin abokan aiki?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wasu abokanan aikinmu ne biyu suke soyayya a tsakaninsu. Kun san matsalar? Namijin yana da aure, har ma da 'ya'ya, wato yana cin amanar matarsa kenan. Ita kuwa matar da yake soyayyar da ita bazawara ce, amma ita ma tana da 'ya'ya.

Duk da cewa mu'amullar tasu ba ta saɓa wa wata ƙa'ida ko dokar wurin aikin namu ba, amma lamarin yana damunmu har ma muna ganin kamar ba su cancanta a ce ƙwararrun ma'aikata ne ba.

Shin akwai wani abu da kuke ganin za mu iya yi a kan lamarin?

Amsa: Akwai matsalar ƙa'idar aiki a nan, amma ba taku ba ce. Ba shakka abu ne da bai dace ba ka ci amanar matarka. Duk da haka ba alhakinka ba ne ka kai rahoton waɗannan abokan aiki naku wurin sashen kula da harkokin ma'aikata na kamfani ko hukumarku, sai dai idan alakar tasu tana shafarku kai tsaye.

Za ku ɗau mataki ne kawai idan har mu'amullar tasu ta shafi yanayin aikinku. ''Gaskiyar maganar ita ce, musamman a tsakanin ma'aikatan da ba masu yawa ba ne, kamata ya yi ka nemi hanyar da duk za ka kauce wa shiga sha'anin wasu abokan aikinka, waɗanda rayuwarsu abin ya shafa kawai.

Ka kawar da idonka a kan abin da suke yi, ka mayar da hankalinka kan abin da ya shafe ka, '' in ji Thorn Jenness, ƙwararre a kan harkokin ma'aikata a Huntington da ke New York.

Ko da yake za ka ga ɗabi'ar wasu abokan aikinka ba ta da kyau a wurinka, ko ba ta yi maka ba, to kada ka bari wannan ya shafi alakar aikinka da su. Matukar za ka yi aikinka, su ma za su yi aikinsu, to maganar wannan na neman waccan ko waccan tana soyayya da wane, ba abu ne da ya shafe ka ba.

Sai dai idan kana ganin abin da suke yi zai iya hana ka tafiyar da aikinka yadda ya kamata, to sai a cikin sauƙi ka nemi shugaban wurin aikin naku ya sauya maka wurin aiki.

Mutumin da ke da aiki a gabansa a nan shi ne shugabanku, wanda shi ke da iko da kowa a sashenku. Da farko sai ya duba ya ga ko abin da waɗannan mutane suke yi ya saɓa wa wata doka ta ma'aikatar.

Idan sun saɓa to maganar ta zo cikin sauƙi, domin ƙila ma'aikatar tana da hanyoyin ladabtar da waɗanda suka saɓa wa dokokinta. Idan kuma babu wata doka da suka saɓa, to a nan sai shugaban sashen da waɗanda suke soyayyar, su yi zama na sirri a kan lamarin.

Shugaban sai ya mayar da hankali kan yadda wannan mu'amulla take tasiri a kan sauran ma'aikata, amma kuma ya yi ƙoƙarin kauce wa maganar cewa ya amince da soyayyar nan da suke yi, ko bai amince da ita ba.

Shugaban ya kuma shawarce su kan su riƙa sirrinta mu'amullar tasu, sannan ya gargade su da kada su bari lamarin ya shafi aikin sauran ma'aikata, zai kuma iya kai maganar ga shuwagabanni na gaba ko ma ya raba wurin aikinsu.

Jenness ya ce ''a matsayinka na manaja wani lokaci abin da yake da wuya wanda kuma ya kamata ka yi shi ne, ka fito fili ka gaya wa ma'aikatan naka yadda abin da suke yi yake shafar aikin wasu ba tare da sun sani ba.''

Bisa al'ada mutane ba sa son a san wani abu na daban da suke yi wanda ya shafi rayuwarsu ne kawai a inda suke aiki, amma kuma wannan ita ce kasadar yin soyayyar a wurin aiki, domin an ce maganin kar a yi kar a fara.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Kissing colleagues